COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

ji yake kafarsa da gangar jikinsa su na neman gaza ɗaukarsa, murje idonsa yayi ya bude sannan ya wanka wa kansa mari har sau uku amma har yanzu abu ɗaya yake gani a gabansa, durƙusawa yayi, da rarrafe yazo gaban Ummu yasa Hannu yana so ya karbi Naila.
Sai a lokacin Anty Ummu ta ɗago jajayen idanunta ta kallesa ta kuma fashewa da kuka, a hankali Ubaidullah ya jawo Naila jikinsa yana girgiza ta yaga dilim, ya sa hannu ya bude idonsa ya ga duk sun kafe, dubansa ya kai kasar farin siket din less din dake jikin, wanda yasha yaga ta gefe da gefe ga jini kamar an yanka zakara,wani razanarniya kara Ubaidullahi ya saki tare da furta.
“INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN!!!!!! Noooooo! Innalillahi wainna Ilayhirrajiun!!! Ya Allah karka ɗoramin abun da bazan iya ɗauka ba” ya fashe da kukan rashin hankalin da ba asa masa rana.
“Su wayeeeeeeee!!!!! Su wayeeee!!!! Suka aikata min wannan. Ɗanyen aiki?”
Ya sake ɗago Naila yana jijjigata.
“Kanwata! Kanwata !kanwata! Ki..kki..ki tashi kinji gani nazo!.. Tashi ki faɗamin su waye suka aikata maki hakan kinji Nailata ki tashi..!”
Anty Ummu ta rungumesa tana kuka, jama’a da yawa a wajan kuka suke yi, da rarrafe Ubaidullah ya rarrafa da Naila a ƙirjinsa yaje gaban Mama wanda ke zaune kamar babu Ita.
“Mama dan Allah ki ce ta tashi Mama wai me ke faruwa ne!? Su waye suka aikata?” MAMA kallon Naila tayi babu abun da ya faɗo mata rai sai dazu da zata fita, ta juya ta fashe da dariya ta ce.
“Mama ina sonki ki yafe min” sai kuma lokacin da take mata fada ta ke cewa.
“In sha Allahu ni zan rigaki Mutuwa Mama”
Kuka bai ban tausayi da tsuma zuciya gami da tashar da hankali Mama ta sa ta rungume gawar Naila.
➰➰➰➰➰➰➰➰➰➰
????To????️
STOP
A YAU NA DAKATAR DA RUBUTA LITTAFIN COLONEL UBAIDULLAH SABODA WASU DALILAI NA MASU KARFI.
NA FARKO.
KAFIN NA FARA RUBUTA BUK DIN NAN SAI DA NA FUSKANCI KALU BALE MAI TARIN YAWA, WANDA NAYI HAKURI NA SHANYE NA CI GABA DA RUBUTAWA, A INA RUBUTUN MA ZUCIYATA BA ADAINA BATA MIN ITA BA
BAN CIKA SON INA BABATU AKAN MAGANA DAYA BA , GASKIA DAN NIMA INA DA ABUNYI
NA BIYU.
YANDA NASHA KALUBALE WAJAN RUBUTA LITTAFIN NAN KAMATA YAYI ACE KU FANS DINA KU KARAMIN KARFIN GUIWA HAR MUJE KARSHR KAMAR YANDA KUKA FARA A FARKO AMMA SAI KUKA SA JIKINA YAYI SANYI, A HAKAN BAWAI NA GAMA DA KALUBALEN DANA FUSKANTA BANE
KARFIN GUIWAR KUWA TA HANYAR YIMIN DOGON SHARHI NE A LITTAFIN, SANNAN KU DINGA TATTAUNA ABUN DA KUKA FAHIMTA A LITTAFIN DA ABUNDA KUKA KARO DA WANDA YA BAKU HAUSHI DA WANDA YA BAKU DARIYA, DOMIN NA GANE SAKON DA NAKE SON ISARWA YANA ISA YADDA YA KAMATA, AMMA BUN TAKAICI WAI NA TURO LITTAFI WASU MA KAM SAI DAI SU KARANTA SUYI SHURU ABUN HAUSHI KUMA BANYI TYPING BA A ISHENI DA WAI CI GABA, TO YAYA ZAN CI GABA KUWA? BAYAN BAKU BANI GOYON BAYA 100%BA, ZAN ZAUNA NA KASHE AIKIN GIDANA DA KULA DA YARANA, NA ZAUNA NA ZUBA MUKU TYPING KUSAN 4TO5 READMORE AMMA KU 1READMORE JUST FOR DOGON SHARHIN DA ZAI FARANTA MIN YA GAGAREKU.
KWANAKI DA NAYI MAGANA, WATA MARAR KUNYA TA BINI PC TANA GAYA MIN CANZAN BANZA, NAN MA KYALETA KAWAI NAYI WLH DAN BANA SON DOGON TURANCI
DAN HAKA BAZAN CI GABA DA RUBUTA LITTAFIN NAN BA KO DA KUWA, ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH NE
INA GODIYA GA DUK MASOYANA WA INDA NA SANI DA WAINDA BAN SANI BA,INA MIKO MUKU GAISUWA TARE DA FATAN ALKAIRI
ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MUKU A DUK INDA KUKE A DUK GARIN DA KUKE INA ALFAHARI DAKU.
SANNAN INA NEMAN AFUWAR WA INDA NA BATA MUSU TARE DA NEMAN GAFARA KU YAFEMIN NIMA NA YAFEWA KOWA,ALLAH KUMA YA YAFE MANA GABAKI ƊAYAN MU.
DAGA KARSHE INA ROKON MANA GAFARAR UBANGIJI,ALLAH YA YAFE MANA ZUNUBANMU YA GAFARTA MANA, YA YAYE MANA WANNAN ANNO BA TA CUTAR CORONAVIRUS(COVID19)ALLAH YASA MU GAMA DA DUNIYA LAFIYA AMEEN.
SADUWAR ALƘAIRI DAGA.
ZAHRA ABDUL MOMYN AHLAN.
BISSALAM.
[8/19, 10:57 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶••~~•~•~•~
my wattpab@Fateemah0
QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
page°°°°°37&40
Ta rungume gawar Na’ila a jikinta, tama kasa magana banda kukan da take yi tana girgiza kai tare da jijjiga Na’ila, da kyar Mama ta iya fizgar magana a bakinta muryarta harta canza kala tsananin tashin hankali.
“Ƴata! Yarinyata Na’ila! Dan Allah ki tashi!”
Cike da ɗimauta Mama take magana, Ubaidullah ji yake duniyar tayi masa zafi har wani duhu-duhu yake gani, ga kansa dake juya masa, komai ya cakuɗe masa, yanzu sam yaji baya gane komai.
Jama’ar dake tsaye a wajan banda kukan tausayi babu abinda sukeyi dan tausayi iya tausayi sunji ma wa innan familyn yarinya da aka zo har kofar gate din gidan su, aka cilla gawarta.
Ana nan a tsaye cirko-cirko kowa ya rasa abun yi, an rasa mai lallashin wa innan bayin Allah, har kuma yanzu Hafiza bata farka daga sumar da tayi ba, itama tana nan a kwance a kasa.
Mahaifin su Abi’atu ne ya dawo yaga mutane rututu akan layin nasu, gabansa ne ya fadi ya ce.
“To meke faruwa ne haka a arean tamu ko dai mutuwa akayi ne?” yana tambayar kansa yayinda ya samu waje yayi parking din motarsa ya fito.
Cikin ikon Allah kuwa ya hango babban ɗansa Safwan a cikin mutanen yana tsaye a gefe yana share hawaye.
Karasowa Baban su Safwan yayi ya dafa kafaɗar dan nasa yake tambayarsa kan meya faru, nan Safwan ya kwashe komai ya fadawa Mahaifin nasu.
Baban su Safwan shine wanda yaje ya dafa Ubaidullah wanda da kayi masa kallo ɗaya zaka gane babu hankalin da natsuwa a tare dashi duk ya fice daga hayyacinsa.
Kallonsa da kyau Baban su Safwan yayi kafin yayi karfin hali irin nasu na manya ya ce.
“Haba ɗana kana namiji da kai, kuma daga ganinka kai din jarumin maza ne taya zaka saka mata a gaba kana kuka? Bai dace da kai ba plss, kayi hakuri, ku tashi mu kai yarinyar Asibiti a dubata, a tabbatar da abun da ya sameta watakila ma ba mutuwa tayi ba”
Ya juya ya ce.
“Am Safwan ɗauko mota, ku kuma dan Allah ku ɗan matsa a wuce”
Kamar mahaukaci haka Ubaidullah ya suri Na’ila, yayinda Safwan ya juya da gudu domin yaja mota, jama’ar dake wajan suka matsa.
Safwan yana kawo mota Ubaidullah ya shige gidan baya rungume da Na’ila a ƙirjinsa, Inna ta cire mayafinta ta miƙawa Ubaidullah ta ce ya rufewa Na’ilan jiki dashi.
Karba kawai yayi ba tare da yayi magana ba, Umma (mahaifiyar su Zaidu) da Inna da Mama su ne suka ɗauki Hafiza wacce tayi shame-shame a kasa tamƙar itama babu rai a tattare da ita, suka sakata a motar.
Baban su Safwan ya shige gidan gaba, Ubaidullah a baya shi da Na’ila ga Hafiza a gefensa itama.
Ta window Baban Safwan ya leƙo ya kira Ummin su Abi’atun akan ta shigo gidan baya su zauna tare da Ubaidullah da Na’ilan idan yaso saita rungume Hafiza, tun da Abi’atu ta iya mota sai su taho dasu Mama da Umma da Inna, da kuma Anty Ummu.