COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Mama dan Allah ki yafe min duk abun da na miki Anty Ummu kema ki yafe min, Yayana kaima ka yafe min, Yaya su bakwai ne suka kamani suk…..”maganar da Na’ila bata karasa ba kenan ta koma fizgan kalman shahada a bakinta.
Gabaki ɗayan su sun ruɗe da gudu Anty Ummu da Abi’atu suka fita neman likita, zuwa wani lokaci kuma tayi ɗiff ta daina murkususu da fizge-fizgen kamar cutar ya lafa mata.
A kiɗime likita dasu Anty Ummu suka shigo, nan doctor ya hau dubata ya gama tattabata sannan ya jawo farin yadin ya rufe mata fuska ya ce.
“Sai dai fa kuyi hakuri amma yanzu kam ta cika, ta amsa kiran mahaliccinta”
Mama ta kalli hannunta wanda suke sarƙame dana Na’ila ta riƙe gam, doctor yasa hannu ya raba hannun Mama da na Na’ila, tangal-tangal Mama tayi baya ta zube sharab a kasa Umma tayi kanta da sauri, yayinda Abi’atu ta kwalla karan da yayi dai-dai da isowarsu Abba da Safwan.
Ubaidullah tamkar almara yake ganin Abun,ihu ya saka gami da cewa.
“Haba Na’ila!! Haba Na’ila! Ya zaki min haka? Baki fa fadamin suwaye ba? Dan Allah ki tashi Kanwata!?Kanwata!?Kanwata!? Ki tashi kince su bakwai ne suwaye bakwai din!?” Da karfi yake magana yana jijjigata, su Abba da Safwan da kyar suka b’anb’are Ubaidullah daga jikin gawar Na’ila nan ya hau buge-buge, wannan shi ake kira tashin hankali wanda ba a sa masa rana, mutuwa kuwa bata sallama da lokaci yayi sai tafiya.
????????????????????????????????????????
ALHAMDULILLAH AM BACK MY FANS PLS KARKU BANI KUNYA, YADDA KUKAYI ALKAWARI TO KARKU KARYATA.
LATE COMER INA TAYAMU MURNAR ZAGAYOWAR SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEEN AMMA BA IRINTA 2020 BA.
ALLAH KUMA YASA IDAN KUKA KARANTA KUNA MIN SHARING DINSA.
ALLAH YABAR SO DA KAUNA MY PPLS
ZAHRA ABDUL
MOMYN AHLAN
TAKU CE????
[8/19, 10:57 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶••~~•~•~•~
my wattpab@Fateemah0
QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
page°°°°°41&45
Da kyar Abba ya jawo Ubaidullah suka fita haraban wajen asibitin, Abba ya ɗaga waya ya kira Malam Liman, na unguwar tasu yake sanar dashi akan cewa yarinyar ta cika,Allah ya mata rasuwa, Abba yana gama faɗawa Malam Liman ya kira wasu Aminansa ya ce dan Allah su zo da mota babbar asibitin Specialist za a dauki gawa ne.
Ubaidullah na tsaye lokaci guda ya nemi hawayen dake zuba a idonsa ya rasa, idonsa ya ƙafe babu ruwan hawaye, ajiyar zuciya ya koma saukewa ba ƙaƙƙautawa.
A can ciki kuwa Inna da Ummi sune suka kamo Mama sukayi waje da ita, yayinda Umma ta kama Anty Ummu da Abi’atu tayi waje dasu su ma.
Abokan Abba sun zo su uku da manyan motaci guda Uku da mutane biyar, nan aka tsaya maganar sa hannu a bada gawar Na’ila dan aje gida a mata sutura a kaita gidanta na gaskiya.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da misalin karfe bakwai da rabi na safe.
Tsaye suke sanye da kakin sojoji a jikin su, Zaidu sai jeka ka dawo yake yi ya kasa zama sai trying din numbern Ubaidullah yake amma yanzu kwata-kwata wayar bata shiga switch up ake ce masa, cike da damuwa gami da faduwar gaba ya ɗago suka hada ido da KB ya ce.
“KB har yanzu fa Ubaidullah shuru anya lafiya kuwa? Gaskiya ni jikina baya bani lafiya, rabon da muyi magana dashi tun da ya ce min ya kusan shiga bauchi I told he will call me so that ya sanar dani cewa ya isa lafiya, but shuru fa” ya karasa maganar kamar zaiyi kuka, KB ya ce.
“Gaskiya nima jikina yana bani ba lafiya ba, jiya na dauka gajiyar hanya ce ta sashi mantawa damu shiyasa bai kira mu ba, amma kuma Ubaidullah baya makara wajan sallarh asuba,kuma baya rabuwa da wayarsa a kusa dashi, kuma da asuba din nida kai duk mun kirasa bai ɗaga ba, gaskiya ya kamata ka kira Umma ka tambayeta tunda itama Mama ka kira bata ɗaga ba, gaskiya bana tunanin akwai lafiya”
Zaidu ya ce.
“To taya Umma zata sani? Ko da yake bari na kiranta idan yaso saita aiki Afnan da Manal su je su gani ko lafiya” Zaidu ya hau dealing din Numbern Mamansa, cikin sa’a kuwa a lokacin ita wayar yana hannnunta su na tsaye a waja ana jira Doctor yazo yasa hannu a bada gawar Na’ila, ta ji wayarta na neman agaji, tana dubawa ta ga Zaidu ne ke kiranta, ita tama manta da kiransa shakaf ta fada masa abun da ke faruwa, inama aka ga natsuwar kiraye-kirayen.
A lokacin Anty Ummu tana rungume a jikin Umma ita da Abi’atu su na Kuka mai ban tausayi, Umma ta dan ɗaga kansu ta tashi ta koma gefe tana sharbe hawaye da hijabinta kafin tayi karfin halin ɗaga wayar Zaidu.
Sallama ya mata ta amsa, a yanda yaji muryarta nan take ƙirjinsa ya bada dam!dam!dam, cikin damuwa ya ce.
“Umma lafiya kuwa? Ya naji muryarki kamar kina kuka meya faru? Dan Allah Umma ki fada min meke faruwa,haka kawai naji jikina yana bani gida ba lafiya ba, jiya Ubaidullah ya taho bauchi inata kiran wayarsa bai ɗaga ba yanzu kuma bata shiga, harta Mama na kirata bata ɗaga ba, yanzu kuma na kira ki naji muryarki kamar kina kuka dan Allah Umma meke faruwa?” ya karasa maganar kamar zaiyi kuka.
Duk yadda Umma taso ta daure karta yi abun da zaisa Zaidu ya gane amma ta kasa, bata san lokacin da wani sabon kuka ya b’arke mata ba, cikin kuka ta ce.
“Zaidu, duk abun da kakeyi ka ajiyeta ka taho bauchi yau din nan kuma a yanzu, Zaidu babu lafiya,Zaidu ba kalau ba, Zaidu Mama ba zata iya daga waya ba, na tabbata bata san ma inda wayar take ba, Zaidu Abokinka yana cikin babbar damuwa da tashin hankali,Zaidu NA’ILA TA RASU!! NA’ILA TA RASU!! Zaidu” Umma ta sake fashewa da kuka.
Zaidu bai san lokacin da wayar dake kunnnansa ta fado kasa ba, ya zube a kasa ji yake kamar mafarki yake yi, gabaki ɗaya wani duhu ne ya ziyarci kwakwalwarsa da idanunsa, ganin haka yasa KB saurin ɗaukar wayar yasa a kunnansa, banda shashshekar kuka babu abin da yake ji na tashi, cikin tashin hankali KB ya ce.
“Umma lafiya kuwa me yake faruwa ne?”
Cikin kuka Umma ta ce.
“Rasuwa aka yi ƙanwar abokin ku ce ta rasu, yau da safen nan ta cika a asibiti yanzu haka ma muna asibitin muna jira Likita yazo yasa hannu abamu gawarta muje gida, idan da hali dan Allah ɗana ku taho yanzun nan ku samu jana’izarta , ka taimakawa Zaidu dan nasan yanzu ba zai iya wani ƙwakƙwarar motsi ba” tana gama fadi ta ajiye wayar dan tasan da maganar Zaidu na cewa yana son Na’ila zai jirata ya aureta.
Kallon tausayi KB ya hau bin Zaidu dashi ganin yadda ya zube a kasa kamar ba shi ba, tunani KB ya hauyi yanzu ace zasu tafi a mota ai ba zasu samu jana’izar ba, “yanzu miye abun yi?” ya tambayi kansa, nan take ya fice da sauri har yana tuntube.
KB bai zarce ko ina ba sai gidan General of the army, dan ma shine yasa aka barsa ya shiga.
Nan ya samu ganin General Of The Army yake faɗa masa abun da ya faru, duk da yana jin haushin abun da Ubaidullah yayi na barin aiki amma bashi ya hana General jajantawa ba, KB ya ce.