COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Sir, nazo neman permission ne zamu tafi bauchi yanzu saboda mu samu jana’izar”
“Taya zaku ce zaku tafi bayan kunsan yau akwai meeting ? Wanda ya mutu ai ya mutu Allah ya jikanta, but babu inda zaku je, ina shi Zaidun yake?”
Wani kallon rashin imani KB ya bi General dashi kafin ya ce.
“Zaidu yana can a ɗaki baya cikin hayyacinsa”
General zai sake magana yaji muryar matarsa Hajiya Jameela tana cewa.
“Allah ya jikanta amma dole sai kun bisa ne, wai ma ba jiya shi yabar aikin ba?”
Kafin General yayi magana sai suka ji muryar ƴarsu Hanan.
“Haba Daddy!? Haba Daddy!? Anya Daddy akwai imani kuwa a ranka?” ta fashe da kuka lokaci ɗaya, ta ci gaba da magana.
“Daddy ka sha yabon Captain Ubaidullah a lokacin da yake saɗaukar da rayuwarsa domin ya ɗaga darajarka, dan kaddarar sharri ta gitta masa? Wanda duk idanuwan ku suka rufe ku ka kasa fahimtarsa? Na ɗauka kowa a barracks din nan ya fahimci halin Ubaidullah ashe duk ba haka bane, shi da ko maza baya kulawa taya zai kula wannan kuchakar kauyen Rumaisa? Yarinyar da ko class bata dashi,gudun wulakanci ya saka shi ajiye aikinsa duk da so da kaunar da yake yiwa aikinsa, yanzu kuma ance kanwarsa ta rasu zasu je Daddy kace ba zasu je ba, to wlh sai sunje idan kuma kana neman daƙushewar wannan barracks din nan Daddy bismillah ga hanya nan, amma tafiya dole sai sunje ni ma kuma zan bisu!”
Tana gama faɗi ta haura sama aka bar General da matarsa baki sake su na kallon yarinyar tasu, juyowa General yayi ya kalli KB, KB ya sara masa ya juya ya fice ,komai ta fanjama fanjam, dan yaji zuciyarsa ta ƙiƙashe shima.
Part dinsu ya koma ya samu Zaidu zube a kasa yanda ya barshi.
Basu wani tsaya daukar kaya ba, KB ne dai ya sauya kayansa daga kaki zuwa kayan gida riga da wando, amma Zaidu ya kasa wannan, sun fito kenan sai ga wani sergeant da sako daga wajan ɗiyar General Of The Army.
Karban Sakon KB yayi ya duba yaga ashe latter ne tayi rubutu kamar haka.
” KB Daddy ya hanani fita karshe ma yasa sojoji tare ni, amma kuje filin jirgi yanzu na siya mana sit mu uku jirgin zata tashi nan da 1hr, tsakanin Abuja da Bauchi indai a jirgi ne 2hrs ne kawai dan haka ku tafi yanzu na bawa Zeey tawa kujerar In sha Allah zaku samu jana’izar na kira Zeey na faɗa mata, yanzu Sergeant Montie zai kai Ku airport ku hanzarta pls“
KB yana gama karanta sakon yayi murmushi gami da cewa.
“Allah ya biya ki Hanan, harka da ƴaƴan manya akwai dadi, komai nasu a saukake”
KB ya juya zai yiwa Zaidu magana sai ga Zeey kamar an wullota, cikin tashin hankali ta ce.
“Yanzu Hanan take faɗa min mummunar labari”
KB ya ce.
” muje dai yanzu tukunna kar mu makara”
Mota suka shiga Sergeant Montie ya dauki hanyar airport.
Zaidu tun da Umma ta ce masa NA’ILA TA RASU ya kasa banbance yana duniya ne ko akasin haka, burinsa kawai yaje yaga karya ne Lovely dinsa tana nan.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Sai wajan karfe tara kafin aka samu Doctor ya zo yasa hannu aka bada gawar Na’ila.
Ubaidullah na tsaye aka fito ana tura gawarta, ganin abun yake kamar shirin film, har aka sakata a daya daga cikin motar Abokan Abba wasu mutum biyu daga cikin mutanen da suka zo, sune zasu ja motar Ubaidullah da wanda Abba da Safwan suka taho dashi.
Bayan an gama komai Inna ta ce ita zata zauna da Hafiza, su wuce kawai, haka kuwa akayi har sun fita sun fara jan Mota Hafiza ta farka a haukace drip din da aka daura mata ta fizge shi ta diro daga kan gadon.
Da mugun gudu ta dauki hanyar wajan asibiti tana ihu tana cewa.
“Wayyo Allah na Na’ilata!! Wayyoo Allah yar Uwata! Ina Yar Uwata!? Wayyo zan mutu!”
Da gudu Inna ta bi bayanta a lokacin motar su Ubaidullah ne bai kai ga barin asibitin ba, amma har sun bata wuta, yana cikin motar yaji ihun kanwarsa da sauri ya fito.
Can ya hangota kuwa tana gudu tana ihu bata ma san inda zata je ba.
Inna tana cewa.
“Dan Allah yan uwa ku taimaka min ku riƙe min ita” wasu kuma sun ƙi riƙeta ne dan sun dauka mahaukaciya ce.
Da mugu Ubaidullah ya taro kanwarsa tana ganinsa ta sake rushewa da Kuka, jawota jikinsa yayi yana bubbuga bayanta sannan suka jira Inna ta karaso wajan suka shiga mota sai gida.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Unguwar su Ubaidullah kamar an buga tambari haka jama’a suka cika har ba matsaka tsinke, saboda lokacin da Abba ya kira Malam Liman ya faɗa masa yarinyar ta rasu, shi kuma ya fadawa Jama’ar unguwa shiyasa kafin su iso unguwar ta cika da mutane, barin ma Na’ila da take da jama’a saboda gagararta ta shiga nan ta fita can, ga hidima da jama’a shiyasa nan da nan jama’a suka cika layin unguwar tasu.
Da kyar aka samu aka wuce bayan an wangale gate din gidan gabaki ɗaya.
Direct aka wuce da gawar Na’ila ɗakin Mama domin ayi mata wanka.
Lokaci ɗaya Mama ta nemi kukan da ke idonta ta rasasu ,ji take idon ya bushe ƙamas, tana zaune a gefen gawar , su Umma da Ummi(mahaifiyar su Abi’atu) suka shigo da ruwan zafi wanda za’ayiwa Na’ila wanka dashi suka ajiye, suka dubi Mama wacce ta kafe Na’ila da ido ko giftawa bata yi, Umma tazo ta zauna kusa da Mama ta dafata ta ce.
“Mama dan Allah kiyi hakuri, ki tashi ki fita, zamu wanketa nida Maman Safwan”
Girgiza kai Mama ta shiga yi gami da cewa.
” A’a Umma zan tsaya na yiwa ƴata wanka dan muyi sallamar karshe, ku zo muyi mata kawai, zan wanke ƴata, kin gani ko Umma jiya iwarhaka ina tare da ƴata wasa da dariya amma wai yau gata nan kwance a gabana ina so nace mata ina sonki ƴata ko da sau ɗaya ne ta bani amsa amma ina hakan ba zai yu ba, jiya har faɗa sai da nayi mata ashe duniyar ma gabaki ɗaya zata tafi ta bar min, Umma kin ganta kalli fa ki gani kamar bata mutu ba ko zamu koma asibitin ne a sake duba min ita?”
Mama ta karasa maganar tana duban Umma.
Duk yadda Umma ta so daurewa amma ina ta kasa, sai da Mama ta bata tausayi ta fashe da kuka, itama Ummi hawayen take yi kafin tayi karfin halin cewa.
“Dan Allah kuzo mu suturta yarinyar nan a kaita makwancinta,Dan Allah Mama kisawa zuciyarki salama, kiyi dangana, kiyi tawakkali, ki dauki wannan kaddarar,ki ta nanata kalmar INNALILLAHI WA INNA ILAYHIRRAJIUN! a cikin zuciyarki Dan Allah!” ita ma ta karasa maganar tana sake share hawayen da suka kasa tsayuwa a idonta, Mama ta ce.
“To” a sanyaye.
Nan suka yiwa Na’ila wanka amma Mama ta kasa tsayawa a shirya Na’ila, dan haka Ummi tayi waje da ita, wani bedroom wanda yake kusa da nasu Na’ilan nan aka saka Mama a ciki ,Mutane sai dannarta suke suna bata hakuri, amma sai dai ta ce.
“Uhummm”
Dan ji take Numfashinta ya fara Of and down.
Hafiza kuwa bayan sun iso gida Inna tana tare da Ita a dakin su, dasu Anty Ummu, Abi’atu, Afnan Manal, sai kuka suke yi, Anty Ummu na zaune bata um bata um um,Hafiza kuwa ta raku’be a jikin Inna jikinta sai rawa yake yi.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Karfe goma da rabi jirgin su ya sauka a airport din Bauchi State, ba tare da bata lokaci ba, suka nemi tazi sai a lokacin Zaidu yayi magana.
Maganar kuwa unguwar da za akai su ne.
Tun da Zaidu ya sauka a Bauchi faduwar gabansa ya tsananta, idonsa kuwa ya zubata kachokar a hanya.
Zuciyarsa bai sake tsinkewa ba sai da suka doso unguwar su Ubaidullah tun daga farkon layi yaga jama’a, nan yaji ya fara yaƙi da numfashinsa, drivern ne ya ce sai dai su sauka in ba haka ba, idan ya shiga ba zai iya fitowa da wuri ba.