COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai bayan sun fita ne KB ke sanar da Ubaidullah ai da Zeey suka taho nan KB ya basu labarin yanda sukayi da General Of The Army, girgiza kai Ubaidullah yayi gami da cewa.
“Dan Adam kenan, ba komai rayuwa ce, ta ishe kowa ishara, Hanan kuma Allah ya saka mata da alkhairi.

Tun da suka dawo daga maƙabarta basu koma cikin gidan ba,dan haka Ubaidullah bai san halin da Mama take ciki ba, sai da aka yi sallar la’asar tukunna suka shiga cikin gidan dan su gaisa da Zeey, nan Ubaidullah ya ga Mama tamƙar ba ita ba harta canza kamanni, nan hankalinsa ya sake tashi fiye da na da.

Hafiza ma haka ta koma bata um bata um um sai illa rungume pic dinsu da tayi a ƙirjinta duk wanda ya ganta sai ya zubar da hawayen tausayinta, harta Anty Ummu ta koma tausayin Hafiza.

Da dare kuwa ta shiga Kitchen dan ta dauko ruwa ma wata mata nan ta ci karo da tashin hankali.

ba komai bane illa girkin da suka fara shiryawa Yayansu babu wanda ya taba abinci yadda suka ajiye haka yake, da gudu da kuka ta fice tayi hanyar part dinsa.

Suna zaune jingum-jingum shi dasu Zaidu, sai ga Hafiza da Kuka kamar an wullota, tana zuwa ta faɗa jikinsa, ta ƙanƙame shi tana kuka mai mutukar tashin hankali.

Ɗauriya iya ɗauriya Ubaidullah ya ɗaure kafin ya ɗaga Hafiza daga jikinsa yana share mata hawaye yana girgiza mata kai alamun tayi shuru, tama kasa magana illa hannu da take masa nuni dashi akan zo, tashi kuwa yayi ta kamo hannunsa suka fice, sukayi cikin gida har izuwa kitchen, suna shiga suka samu Abi’atu a kitchen din tana kuka.

Nan Hafiza ta hau nunnunawa Yayansu abun da suka harhaɗa masa, dan kamar kurma haka Hafiza ta koma, Abi’atu ce tayi karfin halin fara magana.

“Haƙika da nasan alaƙata da kanwarka ba zata jima ba dana roƙi Allah bai haɗani da su ba, kwana ɗaya ne kawai yasa muka yi sabon da ko shekara biyu albarka, bansan me Ubangiji ya tanadar ba na haduwar mu dasu,amma ka gani duk wannan girkin sun shirya shi ne domin kai, ashe abincin da ba za aci ba kenan”

“Ƙannanka su na sonka tamƙar yadda kake son su, mun sha hira dasu shekaran jiya, jiya su na haɗa maka abinci har nazo na tayasu ashe duk aikin ban kwana muke yi da Na’ilah ” ta karasa maganar da sabon kuka.

Duk da Ubaidullah baya jin dadi amma haka ya zauna ya dauki abincin da suka dafa masa ya hau ci yana kuka, nan itama Abi’atu da Hafiza suka hau tayasa ci su na kuka har suka ci wanda zasu iya ci, kafin Ubaidullah ya koma part dinsa.

Wannan family yadda suka ga rana haka suka ga dare, babu wanda ya rintsa Ubaidullah da Zaidu kwana sukayi su na sallah, Ubaidullah ma fita ya dinga roƙon Allah a cikin lamarinsa.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

A daddafe har aka samu akayi sadakar ukun Na’ila.

Babu laifi jikin Mama da sauki amma har yau bata magana, amma idan aka zo mata gaisuwa tana amsawa da kai.

Bayan jama’a an watse saura yan uwa na jiki wanda su na nan sai anyi adduar bakwai kafin su tafi su ma.

Bayan mutane an ragu Ubaidullah Zaidu KB Zeey nan suka shiga bincike da iyakacin basirar da Allah ya basu akan gano wa inda suka yiwa Na’ila fyaɗe, barin ma Zeey da take jami’ar bincike (CBI)

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

DAN ALLAH MY PPL’S SU KARA HAKURI WLH INA BUSY NE SHIYASA BAKU SAMUN POSTING AKAN LOKACI NGD DA KULAWARKU A GARENI.

GA MASU KORAFI AKAN MUTUWAR NA’ILAH KUYI HAKURI HAKA LABARIN YAZO KU DAINA GANIN LAIFINA FATAN ZAKU FAHIMCENI KU FAHIMCI INDA LABARIN YA DOSA NGD.

Nasan za a samu kuskure ayi hkr banyi editing ba.

COMMENTS

AND

  SHARE

MOMYN AHLAN TA KU CE????????
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

WALLAHI NA CI WUYA SAU BIYU INA TYPING YANA GOGEWA ????????

page°°°°°51&55

Babu kalar binciken dasu Ubaidullah ba su yi ba dan ganin sun gano wa inda suka aikata wannan danyen aikin,amma babu wani information da suka samu.

Da haka har aka yi sadakan bakwai din Na’ila sauran jama’a aka watse, amma babu wani hasken da suka samu, sosai Ubaidullah da Zaidu suka shiga damuwa akan hakan.

Zeey bincikenta ne ya kasu kashi biyu, ga wanda ta ke yi a barracks ta barosa ga kuma wannan, ita ma ta shiga damuwa, babban burinta ta taimaki Ubaidullah ya koma bakin aikinsa idan yaso bayan ya koma sai su dage da neman wa inda suka yi raped din kanwarsa ya hukuntasu da kakinsa.

Kwanar su Zaidu goma cif a bauchi su na gudanar da bincike kullum basu zama a gida, tun safe zasu fice ba zasu dawo ba sai dare, har wani rama Ubaidullah da Zaidu suka yi, saboda tsananin damuwa da tashin hankali.

A kwana goman nan kuwa da dare General Of The Army ya kirawo su Zaidu akan su dawo gobe idan kuma basu dawo ba, to a bakin aikin su.

Nan take Zaidu ya ce ba zai koma ba yabar aikin, sai da Ubaidullah ya yi da gaske kafin Zaidu ya amince zai koma a goben, a daren ranar ba su yi wani bacci ba.

Da washe gari Ubaidullah ya nemo driver ya ba shi mota ya mai dasu Zaidu Abuja, idan ya so sai ya dawo masa da motarsa.

Sosai Ubaidullah ya din ga yiwa Zeey godiya yana mata fatan alkhairi, murmushi kawai tayi ta ce.
“See u soon”

Da rashin fahimta ya kalleta, ta sake murmushi ta ce.
“A barracks nake nufi”

Girgiza kai kawai Ubaidulllah yayi sannan ya kalli Zaidu wanda ke tsaye har yanzu babu walwala a tattare dashi, kafaɗarsa Ubaidullah ya nausa cikin wasa, sai ga hawaye a idon Zaidu, da sauri Ubaidullah ya rungumesa shima ya fara hawaye, cikin dauriya Ubaidullah ya ce.

“Sai Hakuri sirkina, Allah ya kara mana hakuri, Na’ila ba zata dawo ba ,da ace zata dawo tun kafin mu kaita maƙabarta ta tashi ko dan saboda kukan da muka din ga mata , ta ri ga da ta tafi ta barmu da kewa, kana gani dai har yanzu Hafiza bata dawo dai-dai ba tun da har gobe bata magana, Mama ita ma gata-gata nan ne, yanzu idan ka bar aikinka abun zai yiwa iyayenmu yawa, ni na ajiye kai ma ka ajiye me aka yi kenan? Kayi hakuri duk inda ka ke na tabbata kai din masoyin kanwata ne na hakika, abu daya na sani shine bazan taba barin wannan abun ya tafi a banza ba, wa inda suka aikata min wannan abun ba su san waye ake kira da Ubaidullahi bane, amma zasu sani ranar da suka shiga hannuna.”

“Za su yi nadama marar amfani a rayuwar su, dan duk randa nayi tozali dasu sunan su GAWAWWAKI.”

Yana gama fadi ya saki Zaidu sannan suka rungumi juna da KB, Sosai Ubaidullah yake zuba musu godiya tare da adduar Allah ya barsu tare har abada.

Har cikin dakin Mama su Zaidu suka shiga mata Sallama.

Mama kasa hada ido tayi da Zaidu ,dan gani take kamar zata ga Na’ila a gefensa shima Zaidun hawayena tab a cikin idonsa, cikin rawar murya ya ce.

“Mama zamu koma bakin aiki, ki sa mana Albarka” duk dauriyar Mama sai da tayi hawaye ta ce.
“Allah ya muku albarka Zaidu Allah ya kai ku lafiya, Allah ya kara mana hakuri ka ji?” Zaidu ya jinjina kai, KB da Zeey ma Sallama suka mata, Mama ta musu godiya tana sa musu albarka, dan ba laifi yanzu Mama ta dan sake tana magana, duk kuma saboda Hafiza ne, duk ta zama wata iri da ita, wani lokacin ma idan tayi abu kamar mai matsalar kwakwalwa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button