COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Kamar a wasa yake tambayarsu aikin da suke sha’awa domin aikin karfi bazai kaisu ko ina ba.
Ubaidullah ya ce ,” Aikin Soja.“
Alhaji Adamu ya ce.
“Da gaske aikin soja ku ke so?”
Suka jinjina kai gami da cewa “eh”
Alhaji Adamu da yake babban mutum ne ya ce, “ai kuwa major Hamza aboki na ne yana garin Abuja, sannan da ma naji wani sanarwa akan cewa yara matasa masu jarumtaza’ayi zabe wanda suke sha’awar aikin soja, za’a turasu ƙasar libya domin su samu ingantacciyar training, ina da aboki ma a ƙasar libyan wanda shine mataimakin mai bada horo, idan kuna so sai na tsaya muku na nema muku takarda ku tafi, shekara uku kacal za kuyi ku dawo da cikakkun tambarin ku na sojoji.”
Abun nema ya samu, nan Ubaidullah da Zaidu sukayi na’am
Ko da Ubaidullah yake fadawa Mama fatan Alkhairi tayi masa, sannan ta saka masa albarka.
Abu kamar wasa, bayan su Ubaidullah sunyi wannan maganar da Alhaji Adamu da sati biyu ya kira su yake shaida musu akan cewa sun samu shiga, murna kamar miye, suka dinga zuba godiya tare da yima Alhaji Adamu adduar gamawa da duniya lafiya.
Alhaji Adamu ya ce,”kun zama tamkar yarana saboda ni ban da ƴaƴa maza, mata ne su biyu kuma duka duka shekararsu goma sha biyu ne, babbar sha uku, ai kun san su ko?” suka ce “eh” ,Alhaji Adamu ya ce “ina jinku tamƙar yarana, dan haka ku daina min godiya, nan da wata daya zaku tafi kuje ku fara shiri.”
Ai kuwa nan da wata daya su Ubaidullah sukayi sallama da gida, Mama,Anty Ummu,su Hafiza ,sunyi kuka dan gani suke idan ya tafi bazai dawo ba, shekara uku ba wata uku bane ba sati uku bane, ba kuma kwana uku bane.
Sai da suka fara zuwa Abuja tukunna aka ajiye su a Abacha barracks, nan suka karbi wani horo na sati daya, kuma jirginsu ya ɗaga izuwa libya.
Sosai Ubaidullah yake nuna jarumtarsa da baiwarsa a fagen training, a cikin wata shidda Ubaidullah ya iya riƙe bindiga tare da kwarewa a wajan saiti, shi a karan kansa mai koyar dasu sai da ya sallamawa Ubaidullah.
Su na waya dasu Mama lokaci zuwa lokaci su na jin lafiyarsa shi ma yana jin nasu.
A cikin shekara biyu Ubaidullah ya zama kwararre, idan ka kalleshi sai ka rantse ya kai shekara ashirin amma bai kai ba, shekarunsa sha bakwai ne, kawai jikin ne ya horu da horo ya saka shi zama babba, fuskarsa dama tun asalinsa ba mai ƙaunar dariya bane, sai dai idan yana tare da yan uwansa ko abokansa.
Lokacin da su Ubaidullah suka yi shekara uku a kasar libya sai da aka tura su yaƙi a maƙotar ƙasar ,inda suka yi nasaran lashe yaƙin.
Kafin Ubaidullah su dawo Nigeria sai da ya karbi matsayin master sergeant.“
Ranar da suka dawo kuma aka shirya musu liyafa agarin Abuja na taya su murna.
Alhaji Adamu yaji dadi sosai ganin su Ubaidullah basu watsa masa ƙasa a ido ba, su ma sosai suke basa girma tamƙar mahaifinsu, dan sun mai dashi Babansu.
Ranar da Ubaidullah ya sauka agarin Bauchi wayyo zo kuga murna awajan yan uwansa, inda suka rungumesa sannan suka saka kukan farinciki sakamakon ganinsa da sukayi da kakin sojoji, tare da nasarori tun da ga takardansa wanda zai fara aiki a MURTALA BARRACKS ABUJA.
Tun daga wannan lokacin Rayuwa ta canza ga ahalin margayi tsohon Soja Abdullahi galadima.
“Hakan ne ya sa Ubaidullah ya fiye zama a garin Abuja, sai dai ya zo weekend 2days ya koma Abuja bakin aikinsa, dan basu son Ubaidullah yana nesa dasu.
Duk yaƙi ,ko kuma kama yan’ ta’adda su Ubaidullah ake turawa.
Shekararsu daya da dawowa daga libya suka sake komawa wani yaƙin, inda aka dinga ɗauki ba’daɗi, da kyar su ka sha kamar ba zasuyi rai ba, amma da ikon Allah suka ci yaƙin, yayin da Ubaidullah shi da Zaidu suka ƙarasa wannan yaƙi a ƙasar. Bayan sun dawo aka gayyatoAlhaji Adamu, inda ya tsaya amatsayin Uba,
aka musu ƙarin girma, inda suka lashe muƙaman first lieutenant sannan suka samu kudi.
Ubaidullah ya kawo shawara suka haɗa kudi suka canzawa Alhaji Adamu mota.
Ya ce “a’a yarana kun fini bukatar kudi ,dan haka wallahi na yafe.”
Su ka ce “ai ba dan yana da bukata bane kawai dan su faranta masa ne amatsayinsu na ‘ya’yansa, dan haka ya karba ya saka musu albarka.”
A lokacin ne kuma aka mai dasu 9JA BARRACKS bayan sun dawo nigeria kenan.
Nan suka hadu da KB kuma suka zama abokai.
Tun da Ubaidullah ya tako kafarsa izuwa 9ja barracks to’fa nan ladies suka sakosa a gaba, amma ko kadan baya ɗaga ido ya kallesu balle yasan dasu.
Gida Ubaidullah ya gina wa mahaifiyarsa mai kyan gaske, inda yanzu a nan suke rayuwa, dan yanzu kudi yana shigo masa, dan first lieutenant ba wasa ba, da ma ance bayan wuya sai dad i,babu wanda yake fata ya mutu a wuya ko a talauci.
Wannan kenan shi ne taƙaicaccan tarihin First Lieutenant Ubaidullah wanda a yanzu akayi
masa ƙarin girma ya koma CAPTAIN UBAIDULLAHsaboda yaƙin da sukaje agarin maiguduri, yayin da da yawan Sojoji sun gudu wasu kuma an kashe su, hatta su Ubaidullah sai da suka sha harbi kafin suka tsira.
Dawowar su da wata biyu shine aka musu ƙarin girma, sannan za’a sake tura su border nan da wata daya, wannan kenan.”
_ Wasa farin girki
Gaskiya ba kullum zaku dinga samun littafin nan ba,
Ina barar adduar ku
Ngd ngd ina ƙaunar ku masoya a duk inda ku ke.????
COMMENTS
&
SHARE
BY MOMYN AHLAN✍????????
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
my wattpab@Fateemah0
QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????
Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako????????
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????
dedicated to my Fans
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________
page°°°°5&6
Da washe gari suka fara fita ƙarin training a wajan commander Victor.
A cikin 2weeks Ubaidullah ya sauke nashi, dan shi baya wasa barin ma a wajan aikinsa na soja.
Ya fito zaije office dinsa suka hadu da Zeey.
sanye take da 3quarter na sojoji da black t-shart tana ganinsa ta taho da gudu tayi tsalle ta ɗaga kafarta,ta kai masa naushi amma ko gizau Ubaidullah bai yiba, yadan gota kadan ,a madadin ta fadi, sai tayi wani juyi ta ɗirko akan kafafunta tana kallonsa tana smiling, tahau bubbuge hannayenta tana cewa wow nyc, that’s very good my hero,
that’s why I love u always bcox u ar the best, ta karasa maganar tana kashe masa ido daya tana shirin hugging nasa.
Hannu ya ɗaga mata ciƙe da bacin rai ya ce.
Enough Zeey i said enough!
Don’t even touch me! ya fada a tsawance rai bace idonsa har sun kaɗa sun kara zama ƙanana.
Ko a jikinta ta ce.
Oh my boo common kai meyasa har yau kaƙi ka waye ne kam?
Mtswwww Zeey u are very stupid oya get out of my way b4 nayi football dake.
Maƙe kafaɗa tayi alamun ko a jikina sannan ta ce.