COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai bayan la’asar suka baro gidan Anty Ummu daga nan suka wuce gidan su Umma( gidan su Zaidu) sosai Umma taji dadin ganin su Mama, nan aka gaisa aka sake yiwa juna ta’aziyya.

Abi’atu Hafiza Afnan Manal suka koma gefe su na dan taba hira wanda hiran Afnan da Manal sai Abi’atu dake jefa baki sama-sama amma ban da Hafiza.

Inna ta ce.
“Yauwa yarinyar nan, shekaran jiya dana kunna radio naji labarin mutuwar Na’ila a DUNIYAR MAMAKI RADIO, kuma naji muryar mai gabatarwar kamar ke?” Inna ta faɗa tana kallon Abi’atu.

Abi’atu ta buɗe baki zata yi magana bata kai ga yi ba, kamar daga sama taji muryan Ubaidullah yana faɗin.

“What! Labarin mutuwar kanwata a duniyar mamaki radio? Taya hakan zata kasance tun da ni dai ban yi hira da yan gidan radio ba?”

Abi’atu ta ce.
“Ni ce na kai kuma nayi magana akai, sannan nayi dogon rubutu akan fyaɗe, wanda ranar alhamis jaridar zata fito idan Allah ya kaimu, yan jarida zasu zo domin su tattauna da Mama da kuma kai, sannan….” maganar da Abi’atu bata karasa ba kenan Ubaidullah ya katseta da kakkausar murya.

Ya kalli Mama ya ce.
“Mama tashi mu tafi gida, Umma Inna sai an jiman ku, Hafiza ta so mu tafi” ya fada yana kama hannun Hafiza, itama Abi’atu tashi tayi jikinta duk ba kwari.

Su na fita Inna tayi tsaki gami da cewa.
“Iskancin banza kawai, ba ga irinta ba halin nasu, wai soja, soja ko mala’ikun duniya, dan Allah ki gani fa yarinya tana jawabi cike da natsuwa da ladabi amma ya katseta da kakkausar murya, ya figi hannun Hafizatu kamar wanda yake shirin zuwa sama jannati wai su tafi, yaro kullum fuska sai kace hadiri haba” nan Inna ta dasa mita tana yi tana karawa, ita dai Umma bata ce komai ba.

@@@@@@

Ubaidullah bai tsaya a ko ina ba sai a gate din gidan’su ,su na isowa ana kiran sallar magriba, dan haka ya yi masallaci su kuma suka shiga gida.

Mama tana dakinta Abi’atu da Hafiza su na zaune a daki sai ga Ubaidullah ya shigo ransa a b’ace ya damƙi hannun Abi’atu yayi hanyar fita da ita.

Tana so tayi magana amma bata so Mama taji kuma ta fito ta ga Ubaidullah ya riƙo hannunta, dan haka tayi shuru sai da suka fito daga parlour ta fara magana.

“Malam! Lafiya kuwa? Ina zaka kaini? Me nayi maka zaka min irin wannan rikon? Karka karyani mana ka sake min hannu” ko sauraronta bai yi ba ya yi hanyar part dinsa da ita.

Bai tsaya ba sai da suka shiga parlourn’sa ya cillata kan kujera yana kallonta yana huci.

“Akan me zaki kai labarin mutuwar kanwata gidan radio?” a masifance yake maganar.

Miƙewa tsaye Abi’atu tayi ta ce.
“To miye aibu? Dan na kai labarin mutuwar Na’ila radion mamaki? Naga kai soja ne, a sojan ma Captain na tabbata ba zaka taba barin wa inda suka kashe Na’ila ba, ni na kai labarin ne saboda idan ka kama su kayi musu hukunci ya zama izna ga yan baya masu sha’awar aikata hakan da su hankaltu, dan hausawa sun ce ana tauna tsakuwa ne dan aya taji tsoro, to miye laifina dan na kai labarin gidan radio? Eh tabbas nayi dogon rubutu akai wanda ranar alhamis zai fito kuma ma ai…”

“Pls malama! Ya isheki haka! Ni na faɗa miki cewa ni soja ne yanzu? Duk ba bukatar kiyi haka sai ki nemi izinina, wai shin ma miye sunanki wacece ke?”

Ran Abi’atu ba karamin sosuwa yayi ba da maganganun Ubaidullah.

“Sunana Abi’atu Abdul’Maleek shehu journalist, ni yar jarida ce kuma ni writer ce a gidan radio ina rubuta abubuwan da suka shafi mata.”

Da mamaki Ubaidullah ke binta da ido, a ransa yake cewa.
“Wannan yarinyar ce yar jarida kuma har da rubuta abun da ya shafi mata wannan yar abun?” yake tambayar kansa amma a fili ya ce.

“Duk wannan ba damuwata bane, kuma karki kuskura wasu su zo mana gida da sunan wai yan jarida sun zo yi mana tambayoyi bamu da bukatar haka” nan ya gaggaya mata maganganu.

Kwalla ne ya cika a idonta ta kallesa bakinta na bari ta ce.
“Nakan yi shige-shige dan ganin na binciko wasu abubuwa dan na yi rubutu akai a samu mafita, bansan cewa nayi shishshigi bane, kayi hakuri idan ka sake ganina a gidan ku na yarda kayi min duk abun da ka gadama” tana gama fadi ta fice da gudu.

Duk wannan draman da suke yi Hafiza tana tsaye a bakin kofa tana jin su, har san da Abi’atu ta fice da kuka.

Rimtse ido Ubaidullah yayi wani bangare na zuciyarsa bai ji dadin kuma yanda ya mata ba.

Yana tsaye hannunsa ɗaya a kugunsa daya kuma a fuskarsa ya ji sautin muryan da yau kusan kwana nawa bai jita ba, a hankali ta furta.

“Yayana”

Da sauri Ubaidullah ya juyo yana kallonta da sauri yazo ya rungumeta yana hawaye ya dago fuskarta ya ce.

“Kanwata ke ce? Ke ce kikayi magana? Faɗa min?”

Jinjina kai Hafiza tayi ta ce.
“Yaya baka kyauta ba abun da kayiwa Anty Abi’atu, shin kasan kalar kokarin da take yi kuwa, wajan taya ka gano wa inda suka kashe min sismieta? Ita da Yaya Safwan kullum su na fadi tashi ,su na iyakar kokarin’su, Yaya, Anty Abi’atu tana da matukar kirki fiye da tunaninka bata da matsala ko kadan, ya kamata ka bata hakuri akan abun da ka mata.”

Ubaidullah ya ce.
“Kina so na bata hakuri?” Hafiza ta gyaɗa kai alamun eh, ya ce.
“To shikenan idan tazo gobe zan bata hakuri kin ji?” Hafiza ta sake gyaɗa masa kai sannan suka fito a tare suka shiga dakin Mama.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Da sallama ta shiga parlourn gidan su Abba da Ummi su na zaune duk da fuskarta babu walwala amma sai da ta danyi fara’a tazo kusa da Ummi ta zauna, kafin ta gaishe da iyayenta, suka amsa Abba ya kara da cewa.

“Ah ai na dauka zamu bi ki da kayanki ne ai yau kusan kwana uku ina tambaya kina ina wai kina gidan’su Mama” dan murmushi tayi ta ce.

“Haba dai Abbana gani na dawo ai” Ummi ta ce.
“Ya jikin Mama da Hafizan?”

“Alhamdulillah Mama da sauki, itama Hafizan Alhamdulillah amma har yanzu bata magana”

“Allah sarki! Zata ware a hankali Allah ya basu lafiya” cewar Ummi suka amsa da ameen, Yaya Safwan ya yi sallama ya shigo ya ce.
“Ah journalist yau an dawo kenan” hararan wasa ta masa sannan ta miƙe ta shige ɗakinta bata kula Yayan nata ba, kwanciya tayi tana tunanin maganganun Ubaidullah, sake rimtse ido tayi ,ta dauko wayarta ta shiga wajan video nan ta ci karo da videon Na’ila, kukanta tasha kafin ta tashi tayi sallar isha’i ta kwanta.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Da washe gari Ubaidullah ya yi shirin faɗawa mahaifiyarsa cewa yabar aiki.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

DA BABU GWARA BA DADI, KU LALLABA DA WANNAN KARKU ZAUNA SHURU PLS WLH YANZU BANI DA LOKACIN TYPING BUK BIYU, BAZAN IYA CE MUKU GA LOKACIN DA ZAKU DINGA SAMUN UPDATE BA, SABODA SABON BUK DIN DA NAKE TYPING, FATAN ZAKU FAHIMCENI, NGD

GA MASU BUKATAR SABON NOVEL DINA NA KUDI MAI TAKEN SUNA ITA CE ZUCIYATA SAI KU NEME NI TA NUMB TA KAMAR HAKA, 08165550116 KIRA KO WHATSAPP NGD.

COMMENTS AN SHARE.

MOMYN AHLAN TAKU CE????????,
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button