COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

@@@@

Kusan awa ɗaya, Abi’atu tana zaune Ubaidullah bai ce da ita ƙala ba, tun gaisawar da suka yi.

Guntun tsaki taja ba tare da ya ji ba, a ranta ta ce.
“Ni Abi’atu yau na ga salon wulakanci har gidan Ubana, mutum ka zo, ka sa a kirani amma ka mai da ni tamkar wata poster? To wallahi baka isa ba, idan baka da abun yi ni ina dashi” tana gama faɗin haka a zuciyarta ta miƙe zata fita har ta kai kofar fita ya ɗago shi bai ma san ta tashi ba, da sauri ya ce.

“Amm keee! ABI’AH.”

Cak Abi’atu ta tsaya saboda yanda ya kira sunan nata wai Abi’ah take tsiƙar jikinta ya tashi ga wani kasala da ya sauke mata.

“Subhanallahi! Wannan bawan Allah akwaisa da fi’ili” duk maganar zuci take yi.

Tasowa Ubaidullah ya yi ganin yanda ta tsaya bata da alaman juyowa balle ta sa niyyar dawowa,gabanta ya zo yana dan kallonta sama-sama dan bai son ya cika kallon mace saboda kar zuciyarsa ta ƙitsa masa abun da ba shi kenan ba.

“Uhum amm dama na zo ne na baki hakuri akan maganar da kika fadi akan cewa ba zaki sake zuwa gidanmu ba, ko ba komai saboda ke Hafiza ta fara magana, na yi farin cikin haka sosai, ga shi Mama tana yabonki sosai ko ma ba danni ba ya kamata ki janye maganar ba zaki sake zuwa ba, tun da naga alama duk kin sace zukatan yan gidanmu, fatan kin fahimci abun da nake nufi?”

Tun da Ubaidullah ya fara magana dodon kunnen Abi’atu yake mata guɗa, yanda yake furta magana ɗaya bayan ɗaya abun ba karamin burgeta yayi ba, barin ma sexy voice dinsa wanda taji yana shirin sakata bacci, a fili kuma, motsa dan ƙaramin bakinta tayi ta fara magana, zubawa bakinta idon Ubaidullah ya yi, a cikin ransa ya furta. “ya salam! Yarinya yar ƙanƙanuwa amma sai kisisinar tsiya”

“Dama ai ba dan kai din bane zan koma, fatan kai ma ka fahimceni?” ta fada gami da juyawa zata fita a ranta ta ce.
“Ka ji fa, wai ya zo bani hakuri amma bai furta min yi hakurin ba” juyawar da ta yi suka yi karo da Hafiza zata shigo ita kuma, tsayawa Hafiza tayi tana musu kallon tuhuma, daga masa gira Hafiza tayi ya kau da kansa gefe ya ce.

“Hafiza muje ko?”

Caraf ta ce.
“Yaya, muje ka gaishe da Ummin, Abba ma ya dawo, Anty Abi’atu dan Allah karasa sai na biku a baya” da mamaki suka kalli Hafiza ta tura baki, dukkan’su basu ce komai ba, Abi’atu tayi gaba Ubaidullah ya bi ta a baya, har cikin parlourn su.

Abba da Ummi su na zaune, su Abi’atu su na shigowa Safwan yana fitowa, nan suka yi musabaha da Ubaidullah ya yinda Ubaidullah ya dukar da kansa kasa sosai ya russuna ya gaishe da Abba da Ummi tamkar ya je gaisuwan surkai.

Amsawa Abba da Ummi suka yi cike da fara’a, sannan Ubaidullah ya mike da sauri ya fice Hafiza tayi musu sallama tabi bayansa, Abi’atu ta zauna Ummi ta ce.

“Ke Abi’atu wannan wani irin shirme ne? Mutane su zo wajanki zasu tafi ba zaki taka musu ba?”

Ba dan Abi’atu ta so ba, ta miƙe ta fito wajan gate ta ga har sun dan yi nisa, tsayawa tayi na wasu lokaci kafin ta koma cikin gida.

Ubaidullah su na zuwa sai da ya ga Hafiza
Ta shige kofar parlour kafin ya shiga motarsa yabar gida, dan kuwa sauri yake yi akwai aikin da zai je mai muhimmanci.

Ubaidullah bai dawo ba sai tsakar dare wajan sha biyu da rabi, amma duk da haka sai da ya fara shiga ciki dan ya ga lafiyar Mahaifiyarsa da Kanwarsa, Hafiza a dakin Mama ta yi bacci, Mama kuwa idonta biyu,har sai da ta ga Ubaidullah kafin ta ji karfin guiwar samun damar kwanciya.

    @@@@@

Da washe gari bayan Ubaidullah ya shigo sun gaisa da Mama yake faɗa mata in da ya je jiya, akan cewa ya samu wasu manyan shaguna ne a kasuwar wunti guda hudu ya siya, har ya bada other za a kawo kayayyaki yau za a zuba, sabida ya san yana da wani sana’ar da zata din ga kawo masa kudi, dan kar kudin hannunsa ya kare su rasa yadda zasu yi.

Adduar Allah ya sanya alkhairi da Allah ya rufa asiri ya kara buɗi Mama ta yi masa, ya amsa da ameen, har ya tashi zai fita Mama ta ce.

“Ubaidullah, shin Alhaji Adamu yasan da cewa kabar aiki?”

“A’a Mama, bai sani ba, yanzu kusan shekaransa ɗaya da rabi kenan baya ƙasar, shi da iyalansa,su na Cairo”

“Ayya, sai yau she kuma zasu dawo?”

“Wallahi, Mama ban sani ba, duk da muna waya dashi lokaci zuwa lokaci muna gaisawa, amma ban faɗa masa abun da ya faru ba.”

“To shi kenan, Allah ya zaba abun da yafi alkhairi a rayuwa”

“Ameeen Mama, ina Hafiza ne?”

“Ba su jima da tashi anan ba ita da Abi’atu” jinjina kai ya yi, ya fice.

 @@@@@

Masha Allah kwana hudu aka dauka ana gyaran shagunan Ubaidullah ya yinda aka zuba kaya masu kyau da tsada da arahar kudi, wanda ana ta neman sunan da za a sa wa shagon amma an rasa, Hafiza ta tambayi Abi’atu sunan da ya dace a sawa Shagunan.

Nan Abi’atu ta ce, a sawa Shagunan suna, ABDULLAHI’S FAMILY, sosai kuma sunan ya burge Ubaidullah dan ya ji dadin sunan sosai.

Cikin ɗan ƙankanin lokaci Allah ya sakawa shagunan albarka, nan da nan Abdullahi’s Family Shop jama’a aka san da zamansa a garin bauchi, barin ma yan mata, dan kuwa an zuba su kyale-kyale, jakukkuna ne takalma atampopi shaddadu materials su cosmetics, babu abun da babu a shaguna guda hudun ne.

Haka rayuwa ke tafiya da sauri-sauri duniya tana gudu, yau shagunar Ubaidullah watansa ɗaya da budewa kuma Alhamdulillah yana samun kudi sosai kudi su na shigo masa masha Allah, dan har mota ya siyawa MAMA da Hafiza, duk da shi ba zaman shagon yake yi ba ya samu masu zama masa dan shi har kwanar gobe baya da sha’awar wani aiki ko kasuwanci wanda ya wuce aikin soja, duk abun da ke faruwa Ubaidullah su na magana da amininsa Zaidu, ba laifi Zaidu ya fara warewa amma ba sosai, ta bangare daya su na kan bincike akan wa inda suka yiwa Na’ila fyaɗe, yanzu tsawon wata hudu kenan, da rasuwar Na’ila amma babu wani haske, Ubaidullah ya yi kukan baƙin ciki dan kuwa ya fara cire rai, a wannan wata hudun ne kuma Mama ta je ta samu ƙanin mahaifin su Ubaidullah akan ya je ya nemawa Ubaidullah auren Abi’atu, hakan kuwa aka yi, inda Ƙanin Baba ya je nemawa Ubaidullah auren Abi’atu ba tare da sanin Abi’atu ko Ubaidullah ba, amma kowa ya sani daga ciki kuwa har da Hafiza duk da Mama tace babu wani gayyar da za’ayi daura aure ne kawai, Hafiza kuwa ita ce ma a kan gaba wajan ganin auren ya tabbata.

Abba cewa ya yi, ai Ubaidullah tamƙar Safwan yake dan haka ba komai ai, ya basa Abi’atu, har aka tsaida ranar biki ba mai tsayi ba, wata daya kacal.

Mama tasa Ubaidullah ya haɗa akwati a shagonsa kayan lefe masu rai da lafiya, amma ba tare da ya tambayeta nawaye bane, dan ko da kayan shagon duka Mama tace tana so, zai kwaso ya kawo mata balle ta ce ya hado lefe ya kawo, har biki ya rage sati daya Ubaidullah bai sani ba tun da bai cika zaman gida , Abi’atu ma bata sani ba, tun da ba shale aka yi ba, yan uwa ma da suka ji suka ce tun da ba taro za’ayi ba, wasu ba sai sun zo ba.

Ko da aka tashi ranar daurin Aure Ubaidullah baya nan tun da ba wani jama’a aka tara ba, sai su Umma dasu Inna da sauran yan uwa da abokan arziki haka ma gidan su Abi’atu.

Ranar da aka daura aure Ubaidullah ba a gida ya kwana ba, sai da ya yi kwana biyu baya gida har yan uwa wa in da suka ɗan leko suka fara watsewa, tun da Mama ta ce babu wani shagali da za’ayi yanzu sai ta tashi tarewa.

@@@@@

Ko da Ubaidullah ya dawo gida babu wanda ya gaya masa cewa anyi aurensa, Hafiza ce dai ta kira su Zaidu ta fada musu amma ta ce kar su fada masa dan shi ma bai sani ba auren yazo a baibai ne, ai kuwa Zaidu ya din ga yiwa Ubaidullah tsiya shi da Hafiza da KB su na dariya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button