COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

@@@@@
Yau sati daya da auren Ubaidullah da Abi’atu, yau kuma ta kama jumma’a, an daura ranar jumma’a ne, sauri take yi zata fita aiki dan akwai labarin da take son yaɗawa sannan tasa a buga a jarida, labarin wani da yasa aka shiga aka yiwa matar makwabcisa fyaɗe.
Har ta gama shirinta ta fito ta samu Ummi na zaune a parlour tana cin abinci, durkusawa Abi’atu ta yi ta gaida mahaifiyarta, da kallo Ummi ta bita da shi ta ga tasa hijab dinta, murmushi Ummi ta yi ta ce.
“Yar gidan Abba sai ina kuma?”
“Wallahi Ummi sauri nake yi zan je aiki akwai labarin da nake son yaɗawa yanzu ne, shi yasa nake sauri na je.”
“Ayya Abi’atu kiyi hakuri kar ki fita, ki kirawo Shafa’atu (cousin sistern Abi’atu ce wanda suka yi skull tare, kuma waje daya suke aiki, Shafa’atu bata cika zuwa gidan su Abi’atu bane yanzu, saboda kunyar Ummi da take ji, tun sadda Safwan ya ce yana sonta har aka musu baiko) sai ki bata ta je ta yaɗa.”
Gaban Abi’atu ne ya fadi ta ce.
“Haba Ummi me ya sa, kwana biyun nan na lura kina son hanani fita meyasa to?”
“Akwai dalili ne Yar Abbanta,yanzu dai yi hakuri ki koma ki kirawo Shafa’atu” tashi Abi’atu ta yi kwalla taf a idonta.
“Ko dai su Ummi su na so na bar aiki ne?” take tambayar kanta bayan ta koma daki tayi wulli da takardun hannunta ta zube a gefen gado, sai da ta gama tunaninta kafin ta kira Shafa.
Su Ummi kuma so suke su bata mamaki dan sun dauka akwai soyayya mai karfi tsakanin Abi’atu da Ubaidullah ne, ba su san da cewa kullum idan suka hadu sai an kai ruwa rana ba.
@@@@@@
Yawancin kullum Hafiza idan Yayanta na gida to fa, sai ta ja shi izuwa gidan su Abi’atu, kuma idan sun je sai sun jima, duk da Ubaidullah yanzu baya zaman gida sosai, sabida binciken da yake zuwa yi yana sa ana kama miyagun mutane, dan ya ce ko ta haka Allah zai sa ya kama wa inda suka yiwa kanwarsa fyaɗe.
Ko da Ubaidullah ya je gidan su Abi’atu ba wani shiri suke yi ba, akwai ranar da Hafiza ta ja shi bayan sallar isha’i suka je gidan, tana ƙirawo masa Abi’atun ta saffe ta koma gida ta kwanta ta hau baccinta abunta.
Ranar har wajan karfe sha’biyu Ubaidullah su na zaune da Abi’atu ba tare da sun san dare ya yi haka ba duk da ba magana suke ba zaman kurame ne, su Abba da Ummi kuma basu damu ba tun da mata da miji ne, sai da Ubaidullah ya duba agogo ya ga sha biyu kuma ya ji shuru din Hafiza ya yi, yawa yau bata leƙo tace Yaya muje gida ba, sai da ya yatsine fuska kafin ya mike ya cewa Abi’atu ta je ta dubo masa Hafiza su tafi gida.
Ba tare da Abi’atu ta amsa va ta je ta gama dube dubenta bata ga Hafiza ba, dawowa tayi ta fada masa, hankalinsa ta shi ya yi, da zai kira Mama sai ya fasa ya kira mai gadi nan yake shaida masa Hafiza ta dawo tuntuni.
Tafiya Ubaidullah ya yi,ba tare da ya ce mata sai da safe ba, itama tabe baki tayi ta ce.
“Allah ya raka taki gona” tana shiga sukayi karo da Ummi gabanta ya fadi ta dauka Ummi zata mata faɗa ne harta fara tunanin kalar abun da za ta yiwa Ubaidullah idan Ummi ta yi mata faɗa sai ta ji ta ce.
“Ahh yar gidan Abba sai yanzu, ina Ubaidullah din sai yanzu ya tafi?”
Sosa keya Abi’atu tayi saboda kunya ta ce.
“Eh Ummi” daga haka ta shige dakinta da gudu Ummi tayi murmushi, itama ta fito daukowa Abba ruwa ne.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Ko da Ubaidullah ya koma gida sai da ya fara shiga duba Mama dan hakan har ya zame masa jiki, Mama ta ce.
“Daga Ina kake ne Yaya Babba?”
Ba tare da tunanin komai ba ya ce.
“Daga gidansu Abi’ah nake” ya fada yana masa sai da safe,Allah ya kaimu Mama ta ce dashi.
Tana tunanin ai gwanda matarsa ta tare kawai, ya fi wannan sintirin da yake yi kullum kar su jawo kansu abun magana tun da dai har an daura aure ai babu abun da ya yi saura.
@@@@@
Da washe gari Mama ta kirawo Ubaidullah ta ce ta ba shi nan da sati ɗaya ya gyara part dinsa Matar shi zata tare, cike da rashin fahimta ya kalli Mama ya ce.
“Mama ni da banyi aure ba wace mata ce gareni da har zata tare?”
“Ka ji shashancin banza, in ji waye yace baka da mata, to auren yau kwana goma kenan, kuma har fada musu zata tare nan da sati daya yau din nan, idan ma akwai wani abun da zaku shirya kuyi gwanda kuyi sirkata ta dawo gareni gabaki’daya”
Ka sa fahimtar maganar da Mama take fadi Ubaidullah ya yi, ya ce.
“Mama kina ta maganar ina da aure wacece matar kam?”
” ABI’ATU“
dum!dum!dum gaban Ubaidullah ya fadi sai kace mace, zai kuma yin magana Hafiza wacce take maƙale tana jin maganar da Mama da Ubaidullah ke yi ita kuma su na waya da Zaidu tana fada masa abun dake faruwa saurin katse wayar ta yi ta ce.
“Yaya zo ka ji” ta ja hannunsa suka fita waje nan ta kwashe komai ta fada masa yanda auren nasa ya kasance, kwafa Ubaidullah ya yi, ya fice dan shi baya da ra’ayin aure yanzu amma yarinya ta mayince sai da ta aure shi, to zata gane kuranta ne.
Ta bangaren Abi’atu itama drama aka yi da ita sosai da aka fada mata cewa tana da aure zata tare nan da sati daya nan ta dinga musu bori ,abun har mamaki ya din ga bawa su Ummi, suka hau tantama ko da ma ba soyayya suke yi ba, sunyi kuskure ne da basu tambayeta ba, wai su a nufin su zasu bata Mamaki dan tayi farin ciki ashe comedy ne za a kwasa.
Ana saura kwana uku babu yanda su Afnan ƙannan Zaidu ba su yi ba, akan zasu yi party amma Ubaidullah da Abi’atu sun ƙi ƙememe, an dai samu anyi walima ƙayatacciya wannan ma Anty Ummu ce ta hada Inna kuwa sai cewa take yiwa Abi’atu.
” Yarinya kin shiga uku an haɗaki da mala’ikan duniya.”
Mama da kanta ta kai Abi’atu ɗaki tayi mata nasiha sosai, tace kuma karta dauke ta a matsayin surka dan tana auren ɗanta har kwanan gobe ita tamkar mahaifiyarta ce wacce ta haifeta a cikinta.
Abi’atu tasha kuka Anty Ummu sai tsiya take mata tana cewa bayan ko ihu kikayi Ummi zata ji ki, ai ke kam auren dadi kikayi, dan ma za ki ji ki kamar ma ba aure bane duk da aure ya wuci wasa ayi hakuri da juna, sosai Anty Ummu ta yiwa Ƙaninta da Matarsa fadan su zauna lafiya, su Zaidu basu samu damar zuwa ba.
Hummm ango shi ka dansa ya zo ko kallon dakin amarya baiyi ba, itama amarya ana watsewa ta rangaɗa wankanta tabi lafiyar gado.
Tun da aka kawo Abi’atu a matsayin matar Ubaidullah rashin shirinsu ya sake bunƙasa, dan kuwa zaman doya da manja suke yi.
A badadi su na gara juna har aka ɗibi wata uku.
Mama kuwa da Hafiza da Anty Ummu sosai suke jin dadin zama da Abi’atu, duk lokacin da taso zuwa gida kuwa zata zari hijabinta suje ita da Hafiza, yanda Hafiza take mu’alama da yar uwarta Na’ilah haka Abi’atu ta zama dan ta farantawa Hafiza rai, hakan kuwa Abi’atu ta kara samun daraja a idonsu Mama.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Tsaye suke sun ƙame waje guda, daga kansu kasan meeting ake yi, yayinda General Murtala ke jawabi.
Ban da kakin sojoji babu abun da yake kashe maka ido.
Cikin tashin hankali General Murtala ke magana akan yan matan nigeria kwantena uku da aka yi garkuwa dasu a kasar india a yankin bangalo, ana neman jami’ai wanda zasu je domin su dawo da wa in nan yan mata, nan aka shiga lissafo wa inda zasu je, amma abun takaici yawancinsu sun ce ba zasu iya zuwa ba, saboda mutanen da suka yi garkuwar su na da mugayen makamai.
Ran General Of The Army ya baci sosai, nan ya hau masifa, har yana cewa, tun da Ubaidullah yabar barracks komai ya daina tafiya yanda ake so.