COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Tsaye take a gaban dress’mirror ta fito wanka ranta bace, rigimar da suka yi da Ubaidullah ne idan ta tuno yake bata mata rai, sabida maganar da ya gaya mata duk da a gabansa bata nuna taji haushi ba.

Towel ne a jikinta ta sincesa ya fadi kasa, tunowa da maganarsa ta karshe tayi in da yake ce mata.
“Kwaila, yo ke miye kike rufewa? Yaushe kika girman? Me kike dashi wanda za ki burgeni ko ki tafi da hankalina,miye a kirjin naki abu fili, yarinya yar firit dake sai baƙar jaraba da iyayi, ji be ki fa, yar abu dake!”

Rintse ido tayi ta ce.
“Hummm! Ni ce ka kira da yar abu? Zaka gane shayi ruwa ne, wallahi sai kayi yaren garinku in dai akwaita” ta dauki towel dinta ta daura ta bude wardrobe ta dauki english’wears dinta wando da riga, duka-duka wandon da kaɗan ya wuce mazaunanta, sai kuma wata yar fingilar riga marar hannu, wanda ko saman shafefen cikinta bai sauƙa ba, ta sharce gashinta ta zubo da wasu ta gaba, ta hada sauran ta tufke a tsakiyar kanta, ta shafa lipstick ta goge fuskarta, nan ta juyo ta kalli kanta a madubi tasan fa ta gama kyau ne, murmushi ta yi ta saka flat’shoe ta dauki humra wanda Ummi ta bata, ta mulkawa jikinta nan ta hau wani tashin ƙamshi wanda duk namiji mai lafiya idan ya ji sai tsuminsa ya tashi, wayarta ta dauka ta dauki earpiece ta saka, ga shi dai ba waƙa ta saka ba, a’a kawai zata je neman rigima ne tun da yanzu tasan ya shigo.

Ubaidullah na kwance a dogon kujerar parlour, ya baya tv baya, haka kawai yake jinsa wani iri, bai yi auni ba ya ji wani kamshi ya daki hancinsa wanda ta haifar masa da kasala gami da sha’awa, kamshin ya dakesa ne a lokacin da ta bude kofar ta fito, tana taku tana jijjiga, ga shi dama bata sa bra ba, ga wandon da ta saka sunan shi yaka muna wando ne.

Tsakiyar parlourn ta zo tana dan taka rawa tana lumshe ido tana satar kallonsa,a hankali Ubaidullah ya juyo ta yi saurin juyawa tana ci gaba da rawar tana jujjuyawa.

Dum!dum!dum! Gaban Ubaidullah ya buga sadda ya yi tozali da sintima’sintiman cinyoyin Abi’atu, a ransa ya ce.
“Wallahi wannan yarinyar ba za ki kasheni lokaci na bai yi ba.”

“Keeeeeeee!” ya buga mata tsawa, amma ko gizau Abi’atu ba ta yi ba, balle ta gwada masa alaman ta ji, a fusace Ubaidullah ya miƙe ya fizgota, ya fincike earpiece din ya jefar gefe yana aika mata da harara.

“Keee! Wannan wani irin iskancin shiga ne!? Na ce wani sabon iskanci ne!? Da za ki kama ki fito tsirara!?”

“Au yanzu kai dama tsirara ka ganni saboda filin yaƙi ya cinye maka idanu?” ta faɗi tana murguda masa baki.

“Ki wuce ki je ki sa kaya bana cike da iskanci!”

“Ni babu kayan da zanje na saka bayan wa inda suke jikina, to wai ma ina ruwanka ne kam? Da shigar da nayi, idan na gadama na fito ma tsiraran miye damuwarka,balle ma ba tsarara na fito ba da kaya a jikina, ni da nake ƴar abu kuma yarinyar yar firit barni nayi shigan da raina yake so, kuma wallahi idan na…..” maganar Abi’atu ne ya tsaya mata a maƙogoro bai karasa fitowa ba, sakamakon murɗe mata hannu da Ubaidullah ya yi, ta saki kara “wayyo Allah Mama hannuna, wayyo Mama zai karyani.”

“Eh ba dole ki ambaci sunan Mama ba, tun da kin lashe mata zuciya, duk babu wanda yake ganin laifinki,ai basu san marar kunya suka ɗaura min ba.”

Duk da zafin murɗe mata hannu da ya yi, ba shi yasa bakinta mutuwa ba.

“Dama INNA ta fada an hadani da mugu, ga shi yana shirin naƙasani, yo da kake maganar na lashe zuciyar Mama idan ma hakan ne alhamdulillah naji dadi, su Mama basu ga munina ba ehe.”

“Dama taya zasu gani tun da ba zama suke yi dake ba?”

“Ai kuwa sun fika zama dani, mutum dai marar godiyar Allah dama shi ai ba a taba masa abun…..” cak maganar ta tsaya sakamakon bakinta da Ubaidullah ya cafka yana aika mata da wasu zafafa kiss, sumar tsaye Abi’atu tayi jikinta ya dauki rawa, kafafunta suka gaza daukarta nan tayi yunkurin sulalewa kasa ya bi ta,kokarin turesa take yi amma ance karfin mace da na namiji ba ɗaya bane, kuma ya mata haka ne dan ya yi maganin rashin kunyar da take masa, dan wani lokacin idan su na cacan baki da ita har mamakin kansa ya ke yi, amma yana cafkar bakinta wani dadi ne ya ziyarce shi har ya manta da in da yake da wacce yake tare, ga humra da ta mulka a jikinta mai fizgar hankali.

Tun tana turesa tana kai masa duka har ta fara kuka.

Ubaidullah baya cikin hayyacinsa, karar wayarsa ce ta dawo da shi hankalinsa dan kuwa ita ce ta katse masa hanzari, da kyar ya saki bakin Abi’atu ya mirgina gefe idonsa lumshe yana sauke ajiyar zuciya, yana ɗagata ta mike da gudu ta yi bedroom har da saka key, dariya ce ta kwace masa ya ce.
“Ashe ke ƙaramar marar kunya ce, nan gaba abun da zan din ga miki kenan idan har zan faɗa ki fada” daga bedroom din ta ce.
“Mugu an gaya maka tsoranka naji? Kawai dai na ga kana shirin aikata abun kunya ne da yar abu, kuma wallahi kaci bashi abun da ka min”

Ubaidullah zai kuma yin magana wayarsa ta kuma yin kara, a hankali ya saka hannu ya janyo wayar dan jikinsa a mace yake murus, da jajayen idonsa na jaraba ya kalli screen din ya ga sunan My Man na yawo, da kyar ya dauki wayar ya saka a kunne ya kasa magana, cikin zolaya Zaidu ya fara gyaran murya mai cike da tsokana, Ubaidullah ya fahimci abun da yake nufi dan haka ya ja tsaki, cikin dasheshshiyar murya ya ce.
“Ka ga bana son iskanci, fadi abun da ke ranka ko na kashe wayata”

“Dama tun da na kiraka kam ai dole na fadi amma dai ina Madam bata kusa ko? Ko tana kusan ma ai abun farin’ciki ne” cikin tsokana Zaidu ke magana, shuru Ubaidullah ya yi, bai bawa Zaidu amsa ba, Zaidu ma baya da lokacin tsayawa su yi shirme tun da ga su General a wajan, nan ya shiga zayyano masa abun da ya faru tun daga AtoZ amma abun mamaki Zaidu na gama basa labari sai cewa ya yi.
“To sai aka yi me?”
“Sai aka yi ana so ka dawo bakin aiki mana”
“Bazan dawo ba! Na ri ga da na hakura da aikin soja!”
“Karya kake yi Ubaidullah! Sai dai ka fada ma wani amma ba dai ni ba, na san ka, ka sanni!”
“Ko da zan ci gaba da aikin soja ba dai a garin abuja ba, ba zan dawo barracks din abuja ba Zaidu pls ka kyaleni”
“Pls Ubaidullah ana bukatar taimakonka” nan Zaidu ya ba wa Ubaidullah labarin yan matan da aka yi garkuwa dasu, murmushin takaici Ubaidullah ya yi, ya ce.
“Sai da amfanina yazo kafin za a nemeni ko?”
“No, Ubaid..”
“Bana son jin komai Zaidu, magana ɗaya ce, bazan dawo ba!” ya katse wayarsa, ya cillar da ita ya rasa me ke masa dadi, tunanin yan matan da aka yi garkuwa dasu ya shiga yi, yanzu ace akwai kanwarsa a ciki ya zai ji? Kuma yasan dole fasikanci za a din ga yi dasu ana bata musu rayuwa ta hanyar yi musu fyaɗe, rintse ido ya yi, take a ransa ya ji babu dadi saboda tuno halin da kanwarsa ta rasa rayuwarta, kwalla ne ya cika a idonsa, dan Ubaidullah duk fadin ransa yana da rauni sosai ta wannan fannin, ya shiga tunanin mafita, kuma baya son komawa barracks din nan, tashi ya yi ya fice ya bar gidan gabaki daya, dan zafi uku ne suka hadu masa waje guda.

Duk yanda Zaidu suka yi da Ubaidullah su General sunji,ya yinda Major Usman ya ce.
“Kunsan dole ne ya ji babu dadi, dama kuma ga shi yana da mugun zuciya, ni a ganina ya kamata mu shirya tafiya gobe ko jibi muje har Bauchi mu basa hakuri a matsayinmu na manya wanda kuma basu kyauta ba, idan ba haka ba rayuwar yan matan nan su na cikin hatsari, kuma da an rasasu durkushewar barracks din nan yazo” kowa ya yi na’am da shawarar Major Usman, in da aka ce su General da brigadier lieutenant colonel da Major General zasu je har gidan su Ubaidullah,da haka meeting din ta watse in da Zaidu da KB suka din ga godewa Zeey su na jinjina mata, duk inda ka wulga zancan Ubaidullah ake yi yau a barracks, sai Allah yawadaran masu hali irin na Rumaisa da S Ema ake yi, masu son shi su na fatan sake ganinsa a barracks very soon.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button