COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Anywhere I don’t care about ur manner Ubaidullah , i just know 1 something, ta sake matsosa sosai ta ce kasan miye shi kuwa?”I love you”

U are always in my heart Ubaidullah, bansan adadin son da nake maka ba.

Ta, Gefenta yabi zai wuce yaji an kira sunansa, lumshe ido yayi a hankali ya ce. “Ya salam”

Juyowa yayi yana watsa mata harara ita ma, ba kowa bace fa ce Rumaisa.

A hankali take taku har tazo gabansa , ta ce. “My luv ina zaka je”?

A dan hasale ya ce.

“In’da kika aikeni jiyan nan da banje miki ba shine yanzu nake so naje miki Ma.”

Turo baki Rumaisa tayi ta bude baki za tayi magana taji muryan Zeey tana cewa.

“Keeeee!
Dan ubanki waye sa’anki a nan wajan”?

A hankali Rumaisa ta waigo gefenta tana kallonta,kafin ta ce “eh gaskiya banga mate dina a nan ba infact mutane biyu ne a nan wajan”

” Rumaisa and her lover Captain Ubaidullah.”

Ji kake

Tass!tass!tass!

Zeey ta faskawa Rumaisa maruka uku a gefe daya.

Kafin kace me dambe ya ƙaraɗe waje.

Ladies barracks ana bawa hammata iska.

Kowacce fada ta keyi cike da kwarewa a salon training din da aka yi mata.

Tsaki Ubaidullah yayi ya wuce gaba yana cewa karnuka kawai.

Yana gaf da shiga office dinsa yaji ana kiransa a baya.

Sir!Sir!Sir.

A hankali ya juyo ya ce.

What’s wrong sergeant?

Sergeant ya ce.
Sir, “Major Usman ne ya ce na ce maka kaje , guardroom domin tambayar wani mai laifi an tambayesa yaƙi fadi.”

Okay, ina Captain Zaidu? and First lieutenant K,B?

Sergeant ya ce Sir,
“Major General ya aikesu Murtala Barracks.”

Okay kawai Ubaidullah ya ce sannan ya juya,ya dauki hanyar guardroom.

Yana isa guadroom ya samu wanda ake tuhuma da laifin yiwa yarinya yar 8yrs old fyade ana tuhumarsa amma ya kafe ya ce ba shi bane,ya aikata ,bayan shaidu sun tabbatar shi din ne.

Yana ganin Ubaidullah yaji gabansa ya fadi ganin fuskarsa babu alamun dariya

Ubaidullah ya ce.

Private first class?
Ya amsa ya shigo da sauri yana cewa “yes Sir”

Ubaidullah ya ce.
“Jeka kawo min kayan aikina”

Da sauri ya fita ko 4mnts bai yiba yadawo da sauri hannunsa dauke da ruwa jikin bucket da wayar wuta, ya a jiye, ya juya zai fita

Ubaidullah ya ce.

“Make sure ka rufe kofar nan da kyau.”

Private first class ya ce “ok sir”

Kallonsa Ubaidullah keyi na yan wasu lokaci kafin ya sake rikiɗewa,alluran sojarsa ta miƙe dan shi a rayuwa idan akwai abin da yafi tsana a duniya,to ace anyiwa yarinya ko budurwa fyade.

Ba tare da bata lokaci ba,ko yin magana, ya dauki ruwan bucket din nan ya watsa masa rabi,sannan ya ɗauki wayar wutan ya fizge bakin ya jona masa shocking ,yaja table ya zauna yana kallonsa.

Nan mai laifi ya fara diskon dole ,yayinda babu in’da bata jijjiga a jikinsa

Sai da yaga ya kusan sumewa kafin ya ɗauki babbar maduki ya bugesa dashi ya fadi bakinsa harta koma gefe.

Captain Ubaidullah
ya durƙusa a gabansa fuskarsa tamƙe tamau( wai soja mala’ikun duniya) naushi daya ya kai masa a baki take haƙorin mutumin guda biyu suka faɗi ƙasa,Ubaidullah yasa hannu ya ɗauka , ya damƙa masa a hannunsa,idanunsa sun ƙara ƙanƙancewa.

Ya ce.

“Ka faɗa min gaskiya kaine kayiwa yarinyar nan fyaɗe”! a tsawance yayi maganar.

“Idan kuma kasan ba gaskiya zaka fada min ba, to ina baka shawara daka ja min tsummar bakin ka kayi shuru if not wallahi humm zaka sake ganin ainihin true color din Ubaidullah.”

Cikin sarƙewar murya ya ce. “Yallabai kayi hakuri ni ne na aikata.”

Ran Ubaidullah ya sake baci ya rufesa da duka, sai da yayi masa jina-jina, kafin ya fita yana huci.

Direct office din Major Usman ya wuce ransa bace, ƙananun Sojoji sai sara masa su keyi.

Ya shiga ya ƙame yana sara masa “Sir mai laifi yayi jawabi ya amsa laifinsa.”

“Nyc job Ubaidullah keep it up Ina alfahari da kai, you can go.”

Ubaidullah ya sake sara masa kafin ya juya ya fice.

ya tafi office dinsa yana zama kamar da 10mints sai ga su Zaidu, da K,B sunyi sallama ya basu damar shigowa, hannu suka bawa juna su kayi musabaha.

Zaidu ya ce.
Captain Ubaidu how is work?

Smiling yayi ” we tnk god Captain Zaidu and u?

Zaidu ya ce.
“Alhamdulillah”

K,B ya ce.

“To abun kuma ƙi dangi ne”?

Ubaidullah ya ce.
“Menene kuma ƙi dangi”?

“Ah to ba dole na ce ƙi dangi ba, naga ni yau ba ayi niyyar yimin magana ba, ba’a kulani ba”

Gaba’ɗaya suka kwashe da dariya,Ubaidullah ya ce.

“Wallahi Allah ya shiryeka K,B yau kuma sharri kake ji dashi zaka ce na ƙi kulaka”?

K,B yana dariya ya ce.

“Ah to ba gashi yanzu na saka ka dariya ba, dama bana so naga ka haɗe rai sosai din nan.”

Ubaidullah ya ce.

” ai ba a san soja da dariya ba”

Zaidu ya ce.

“Yes of course , ba’asan soja da dariya ba but today you look very sad what’s wrong my dude”?

Ubaidullah ya numfasa yana jan iska mai zafin gaske yana fuzarwa,zuciyarsa yana masa soya.

Ya ce.

“Wallahi a rayuwata na tsani naji kalmar an’yiwa mace yarinya ko budurwa fyade, dazu an saka wani yaro matashi a gurdroom ana tuhumarsa da laifin yiwa yarinya, yar’ 8yrs old fyade, dan rashin kunya ana tambayarsa ya kafe ya ce ba shi ya aikata ba, shine Major yasa naje na tambayesa, ina zuwa na jona masa shocking nan take yake gayamin akan cewa shi ya aikata, wallahi har yan zu abin yaƙi fita raina.”

Zaidu ya numfasa ya ce.

“Naji case din tun jiya ake zarginsa yaƙi magana, ashe kai kana zuwa ya ƙoro maka jawabi”?

Ubaidullah yayi tsaki ba tare da ya kuma yin magana ba, illa Zaidu da K,B da suke jajinta lamarin, amma shi kam tunani ya keyi yanda za’abi a magance yiwa yan’mata da yara fyade a wannan zamanin ,dan yanzu abun ya zama ruwan dare, bata ya’ya’ mata ta hanyar rabasu da budurcinsu, yana ta faman thinking about this matter, har su Zaidu suka yi masa sallama suka tafi office dinsu.

Da washe gari

Ubaidullah da Zaidu, suka shirya zuwa office din General Of The Army domin neman permission, zasu tafi ganin gida b4 suje in’da aka turasu kama yan’ta’adda, wato border.

Har office suka je amma yau general of the army bai zo office ba,nan ake shaida musu yau bai fito gida ba, dan haka suka juya suka fita.

Zaidu ya ce.

“Ubaidu muje gidansa kaga lokaci yana ƙure mana kuma kasan halin general, amma ya kace.”?

Tsaki Ubaidullah yayi sannan ya ce.”okay muje amma gaskiya ba son zuwa nake yiba”

Zaidu ya ce.

“Na sani ai”

Sunyi tafiya mai ɗan tsayi kafin su ƙaraso,gate din gidan General Of The Army,wanda duk inda ka wulla idanunka sojoji ne, ana ganinsu Ubaidullah aka ware musu gate ana sara musu, CAPTAIN UBAIDULLAH & CAPTAIN ZAIDU.

har suka karasa bakin kofa wani soja ya bude musu yana sara musu gami da cewa ” wlcm sir Ubaidullah and sir Zaidu”

Zaidu ne ka dai yake amsawa , amma Ubaidullah sai dai ya jinjina kai da kar yake kallon kowa a barracks yasan wa inda suke sonsa da wanda basu sonsa.

A parlour sukayi sallama

Wata haɗaɗdiyar mata ce ta sauko daga kan step tana taku cike da izza da nuna isa da gadara ,kayan dake jikinta ma abun kallo ne, daka ganta kasan iyayi ya zauna ko ba a fada maka ba.

Humm, HAJIYA JAMILA KENAN MATAR GENERAL OF THE ARMY ABDULKARIM.

mata mai jida kanta gami da alfahari da nuna ita watace.

Tana karasowa su Ubaidullah suka sara mata su na gaisheta , sai da ta dauki som minutes kafin ta amsa.

Ubaidullah bai ce komai ba, Zaidu ne ya ce. “Madam Oga sir muke nema”

A hankali ta kira sunan yar’ta cike da yanga.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button