COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

???????? Naji dadin karar’ku a gareni son so domin Rabbi, Allahu ya taya muku.????????????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

Na so na kira sunayenku wa inda suka min sharhi a page din da ya gabata kafin wannan amma Allah bai yi ba, dan haka duk wacce ta min sharhi ta saka a ranta wannan page din kyauta ce gareta, kuyi yadda ku ke so da page din dan naku my ppl’s ina so ku sani ni Zahra Abdul Momyn Ahlan taku ce inayinku.????

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

page°°°°°76&80

Kira Abi’atu ke yi ba ƙaƙƙautawa, sai da ta yi masa kira wajan takwas amma bai daga ba, dan lokacin da ta yi masa kiran farko da ya gani yayi tsaki sai ya mai da wayar cikin aljihun wandonsa, ya juya yana ba wa sojojinsa umarni.

Kukan tashin hankali Abi’atu ta saka gami da cewa.
“Yaya Safwa bai ɗaga ba fa, wayarka kuma netwrk ya dauke ya ƙi kawowa kwata-kwata!”

A fusace Safwan yana jan mota yana kan bin wa inda suka kwamushe Hafiza ya hau saukewa Abi’atu ruwan bala’i yana mata masifa dan hankalinsa a tashe yake ,domin ko da ya iskesu ance sarkin yawa ya fi sarkin karfi, su bakwai, shi ɗaya ai ba zai iya ba, idan aka taki rashin sa’a suka kashesa suka jinkiɗar da Hafiza da Abi’atun ai an bata goma ɗaya bata gyaru ba, sannan ace zai fara biyawa kiran yan sanda ai kafin su iskesu sun yiwa Hafiza Illa idan ma an kamasun kenan, dan yasan by tym da zasu iso idan aka ta ƙarƙare sun gudu.

“Iskancin banza da hauka! Numbern Mijinki amma ba ki da shi?Mijinki fa!? Da ace kuna da number juna har za ki din ga yi masa wannan kiran bai ɗaga bane, da ace kuna da numbern juna ya ga wannan kiran da kike masa yasan babu lafiya, ai sai ki ci gaba da kira, ko kuma ki nemi nerwrk a wayana ki ci gaba da kira, in kuwa ba haka ba, muna karasawa sai su kashemu duka a huta, mtswwww!”
Kira Abi’atu ta ci gaba da yi tana kan kuka.

Ubaidullah jirgi ya shige ya zauna, ana jiran jama’a su gama shiga jirgi ya tashi da zarar lokacin tashinsa ya yi, dabara ce ta faɗowa Abi’atu da sauri ta tura masa saƙo da cewa.
KAYI WA ALLAH DA ANNABI S,A,W) KA DAUKI WAYAR NAN, IDAN HAR BA KA ƊAGA BA, ZA A RASA RAYUKA (ABI’ATU CE)” ta tura masa, Ubaidullah ya ciro wayarsa yana shirin kasheta gaba ɗaya ya ga tarin miss calls da numbern dazu, mamakinsa bai gushe ba sai ga shigowar saƙo buɗe sakon ya yi, ya karanta sannan ya shiga wajan history yana shirin kiranta sai ga kiran nata na sake shigowa, ɗagawa ya yi, muryar kukan ne ya fara kaiwa dodon kunnensa naushi, gabansa ne ya shiga bugawa a kiɗime ya ce.
“Abi’ah! Meya faru? Meya sameki? Wa ya taba miki?” cikin sheshsheƙar kuka ta ce.
DAN ALLAH! DAN ALLAH! IDAN HAR JIRGIN’KU BAI ƊAGA BA KA DAWO AKWAI BABBAR MATSALA AN DAUKE HAFIZA!” wani wawan zabura Ubaidullah ya yi ya miƙe da gudu yana buge mutane, yana sauƙowa daga step din jirgin Sojojinsa ne suka kallesa “Mota” shi ne kawai abun da ya iya furtawa, nan aka miƙa masa Mota ya shige ya bata wuta, cikin tashin hankali Ubaidullah ya ce.
SU NA INAAAAA! INA ZASU KAI MIN ƘANWATA!?
“gamu nan mu na kan bin su ni da Yaya Safwan, kayi amfani da location, Dan Allah kayi sauri kar su cutar da ita, ga mu nan dai sun dauki hanyar fita daga cikin gari” da sauri Ubaidullah ya yi connecting yana bin su da gudu, sai ka ce zai ta shi sama jikinsa sai bari yake yi, hankalinsa idan ya kai dubu to a tashe yake.

Su na ta binsu har suka yanki kwanar bayan gari, sun dan yi tafiya kaɗan cikin wata yar jeji, kafin suka iso wani kangon gida, daga nesa Safwan ya parkar motarsa suka fito da Abi’atu, ya kamo hannunta su na tafiya a hankali su na labewa, maƙalewa suka yi, in da suka hango samarin sun fito da Hafiza sai fizgarta suke kamar kaza suka yi cikin babban kangon nan da ita, ganin sun shige da Ita yasa su Safwan mara musu baya, tuni Abi’atu ta hau video recording da ɗayar babbar wayar Safwan, wayarta kuma Ubaidullah yana amfani da location, a hankali suke bin ta bayan kangon su na duƙawa dan kangon mai girma ne, shiga ciki suka yi su na duddubawa, ga uban daƙuna a kangon, duk in da suke tunanin zasu ga Hafiza basu ganta ba, hankalinsu ne ya sake tashi, kafin nan wayar Safwan netwrk ya dawo, nan ya sake kiran Ubaidullah, yana ɗagawa ya ce.
“Safwan! Ina Hafiza!?”
“Kayi sauri kazo kawai Ubaidullah dan gamu nan a cikin kangon da suka shige da ita, sai dubawa muke yi amma bamu ganta ba dan kangon yana da girma” a hankali Safwan ke magana gudun kar su jiyo su, tun da su mafakar su ce sun san kan abun su.
“Ina Abi’ah!?” cewar Ubaidullah Safwan ya ce.
“Gata nan a gefena muna kan shiga ciki”
“Pls Safwan karka bari ta yi nesa da kai, ka kula da ita dan taurin kai gareta irin na yan jarida ba ko da yaushe take jin magana ba, gani nan na kusan isowa wajan, ku ci gaba da duba kangon a hankali, kar su muku illa na kusan isowa!”
“Eh muna kan dubawa, ina tunanin…..” Safwan bai karasa maganarsa ba ya jiyo ihun Hafiza, wanda ya yi sanadiyyar sakin wayar daga kunnensa karar da Hafiza ta saka harta Ubaidullah sai da yaja wawan burki a tsakiyar hanya, ya yinda ya haɗa motoci garuwa, jikinsa ya dauƙi bari idanuwansa suka zazzago suka yi waje, hawayen ma ya ji sun ƙafe daga idanunsa, take jijiyoyin jikinsa suka fito raɗa-raɗa barin ma na kansa da wuyarsa kamar zasu tsinke, dan ihun da Hafiza ta saka kamar wacce aka farke mata gaba ne, kamar namiji ya shigeta, Mutanen da Ubaidullah ya saka su gwarene suka fara masifa ba tare da Ubaidullah ya bi ta kansu ba, ya wani figi motar sai da wuta ta fi daga salansa, ya ci gaba da sharara gudu, Safwan kuwa ihun Hafiza ne ya saka su juyowa saitin wani windown da suke a nan ne suka ɗaure Hafiza, ihun da ta saka kuma na matse mata nono da daya daga cikinsu ya yi ne, dan tun da take babu wanda ya taba yi mata abu makamarciyar wannan, ihu kuma sun kunci mata bakin da suka ɗaure mata ne, dan idan sun kawo yarinya sukan kunci mata baki dan duk ihun da zata yi babu mai jinta balle ya kawo mata taimako, kasancewar bayan gari ne, kuma cikin jeji, a nan ne suke sheƙe ayarsu da yaran jama’a, Abi’atu ta buɗe baki zata kwallara kara da sauri Safwa ya toshe mata baki, ya jata suka duƙa kasa, bakinsa yasa a saitin kunnenta cikin raɗa ya ce.
“Karki yi ihun da zai sa su ganmu dan za ki bata mana plan, ki ci gaba da video din ni kuma zan san yadda zanyi, ke yar jarida ce kinsan kan bincike baya son tonon asiri dan haka ki kula sosai, ki sa a ranki kece kika fito yaƙi da miyagu, kin fahimceni?” ta gya ɗa masa kai ta goge hawayenta, suka miƙe a tare ya sake cewa.
“Duk abun da za ki ga sunyi min karki sake kiyi ihu ko ki shigo har sai Ubaidullah ya shigo kinji? Dan ina so ne na dauke hankalinsu kar su cutar da ita” tana hawaye ta jinjina masa kai ta cigaba da video din, ya zo zai wuce ya shiga ta ji gabanta ya fadi da sauri ta riƙo hannunsa tana girgiza masa kai, a hankalin ya zare hannunta ya lumshe mata ido alamun ta kwantar da hankalinta ,sannan ya shige yana neman kofar da zata sadashi da windown da suka ga Hafiza, ga dai kofofi amma ya rasa wace kofa ce, shawara a yanke kawai ya din ga bin ko wacce yana dubawa Adduarsa daya Allah ya kawo Ubaidullah yanzu karsu cutar da Hafiza.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button