COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A BARRACKS.
ko da sojojin da aka bar wa Ubaidullah suka ga har jirgi ya ɗaga basu ga dawowarsa ba, nan suka kira Major Usman suka shaida masa ga yadda Captain ya bar airport, Major Usman kasancewar yasan halin Ubaidullah ya saka shi basu umarni akan su bar airport din su koma barracks, bai damu da ya kira Ubaidullah dan yasan shi baya wasa da aiki, barin ma idan abu ya shafi ceton rai, duk abun da zaisa ya bar airport to hakiƙa babban abu ne, sabida haka ya bada lokaci zai kirasa ko da zuwa yamma ne ko dare, tun da tafiyar ma sai nan da 2wks but su na bukatar ganinsa a barrack ne, babu wanda Major Usman ya sama da maganar sai Captain Zaidu da first Lieutenant KB,nan yake shaida musu kamar yadda shi ma aka shaida masa, dan haka ko da Zaidu ya yi waya da Mama ya bar amsar da ta ba shi kawai dan yasan yanzu sai Mama ta tashi hankalinta, dan haka tun yamma ake neman Captain Ubaidullah amma shuru, Major Usman ne ya bada excuse wa Ubaidullah a barracks kowa kuma ya karba, ko bayan da Dr ya yiwa su Ubaidullah bayanin Safwan zai ji sauki soon sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga tarin miss call na manya manya sojoji, ga na Aminansa, sai da ya fara kiran Major Usman bai boye wa Major Usman komai ba, nan take Major Usman ya ce zai yi magana da General Of The Army amma kafin nan Ubaidullah ya kira Lieutenant Genaral ya masa bayani, hakan kuwa aka yi bayan sun gama magana da Major Usman ya kira L.G, nan ya nemi afuwa na rashin dawowarsa yau sannan ya karo uzurinsa, nan kuwa L-General ransa ya b’aci ya ce wa Ubaidullah ya ba shi permit ya taho dasu barracks ya hukunta yan iska, gobe zai ba wa sojoji umarni a taho dasu shi kuma ya sake bin flight, Ubaidullah ya amsa da ok sir gami da cewa ayi masa uzuri nan da kwana biyu idan Brothernsa ya farka, L-General ya ce ba komai zai yi magana da General da kuma General Of da Army, Ubaidullah ya yi masa godiya, kafin ya kira Zaidu ya basa labarin duk abun da ya faru, Zaidu kamar zai yi hauka, haka ya dinga buge-buge yana Allah Allah a kawosu barracks su ci kwal ubansu dan kuwa sun tanadar musu azaba da gwale-gwale dan kuwa basu son wa suka tabo bane, dama ance kwana dubu ta barawo kwana ɗaya tak ta mai kaya.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Da washe gari da safe aka kira Ubaidullah, ya ga bakuwar number yana dagawa aka sara masa cikin girmamawa kamar yana gaban mai sara masan, nan yake cewa.
“Sir Captain Ubaidullah, Sir L-General ne ya ce mu kiraka, zamu tafi da masu laifi, ka fada mana in da kake mu zo mu dauke ka” a takaice Ubaidullah ya gaya musu, cikin ɗan lokaci sai ga su sun zo, nan Ubaidullah ya yiwa su Ummi, Abba, Mama Abi’atu da Hafiza wacce take zaune, sallama ya musu gami da yi musu bayanin yadda suka yi da manyansa Abba ya jinjina kai ya ce.
“To ba komai, nima yanzu gida zan wuce tun da sun ki yarda mu ga Safwan din kuma ku zo muje sai muyi wanka ayi girki a taho da shi, ga shi mun bar baƙi a gida, ina ga dai bikin nan ɗagawa za ayi tun da ga angon a kwance” Ummi ta jinjina kai, kafin Ubaidullah ya kalli Abi’atu da gefen ido ya ganta itama kamar wata marar lafiya so yake ya yi mata magana amma ba zai iya ba a gaban iyayensu dan haka suka fito a tare har da Hafizan, su na fita ya ga sojoji da wata babbar mota da kuma wata madaidaiciya duka kuma barracks car ne,yana fitowa suka ƙame su na sara masa, sannan suka bude masa gidan baya ya shiga ya zauna, suka tada motar suka fice daga asibitin, su ma su Abba mota suka shiga suka dauki hanyar gida.
A hankali suke tafiya hakan yasa Ubaidullah gaya musu su ƙara gudu, su na tafiya yana musu kwatance har suka iso,bude masa kofa sukayi, ya yi gaba suka take masa baya, ko da ya shiga ya gansu a galabaice, nan ya kunce musu baki yana binsu da wulakantaccen kallo, da kyar suke iya bude idanunsu, su ga sojoji tsaye a bayansa, ɗaya ne wanda yake ɗan dama-dama ya fara magana cike da tsoro.
“Dan Allah! Yallabai kayi mana rai kayi hakuri, wallahi bamu san kai soja bane, ba zamu sake ba mun tu ba, Dan Allah ka……” wani wawan naushin da Ubaidullah ya dunƙula hannu ya kai masa shine ya yi sanadiyar rashin karasa maganarsa wanda take jini ya taho da haƙorinsa uku, dan hannun Ubaidullah bai da kyau, ko ya ya ne ya taba mutum da shi sai ya fito ga hannunsa da mugun zafi, to balle wannan da ya kai masa naushin azafafe, kallon sojojinsa ya yi ya basu umarni da su tafi dasu, sannan duk wanda ya yi musu abun da bai musu ba a hanya su parker motar su ci Ubansa! Nan suka sake sara masa sannan suka dauki samarin suka fita dasu, wasu kuma ya sakasu kwashe masa lapton din yace a sama a mota ,amma kafin nan sai da suka yi ma abubuwan hoto har da kayan shaye-shayen, duk wasu kayan maye yace su tafi dasu but lapton da wasu memories ya ce a kaisa gida dasu,nan suka babbar motar ta dauki hanyar Abuja, wasu sojoji mutum biyu suka ja Ubaidullah izuwa gida.
Horn suka danna mai gadi ya bude musu gate, part dinsa ya wuce kai tsaye, yana shiga ua watsa lapton din akan kujerar parlour, bedroom din Abi’atu ya shige ya kwankwasa ya tura kofar bai ganta ba, nasa bedroom din ya wuce ya watsa ruwa shap-shap, ya sake saka kaya matasa nauyi ya fito ya yi part din Mama, a parlour ya samu Hafiza tana zaune Mama tana gefenta Abi’atu kuma tana zaune a kasa ta takure ga abinci a gabanta ta kasa ci, zama Ubaidullah ya yi kusa da Hafiza Mama ta ce.
“Har ka dawo? An tafi dasun?”
“Eh sai da suka wuce kafin aka maido ni gida” Mama ta jinjina kai ta miƙe ta yi kitchen,Ubaidullah ya sake sacin kallo Abi’atu wacce ta yi kamar bata san ya shigo ba, mai da idonsa kan Hafiza ya yi, ya shafo kanta a hankali ya ce.
“Are u feeling much better?” ta jinjina masa kai kanta a sunkuye dan videon da aka nuna mata na yar Uwarta yayi mugun ɗaga mata hankali dan har yanzu ba wai ta koma nml bane, a hankali Hafiza ta kama hannun Yayanta ta yi masa nuni da Abi’atu sannan ta miƙe ta shiga daki tasa kuka, Hafiza na shiga daki Ubaidullah ya miƙe ya zo gabanta ya kamo hannunta bata yi masa gardaman ba zata tashi ba,ya dauki abinci ya jata suka fita ya yi hanyar part dinsu, yana shiga parlourn ya zaunar da ita, yaja stool gabansu ya ajiye abinci, gamin yadda idonsa duk sunyi luhu-luhu ta lumshe da bude, dafe kanta ya yi ya ji da zafi raɗau, abinci ya fara mata amma ta ki bude baki ta ci, da kyar ya samu ta bude bakin amma tana shirin saka masa kuka ya yi saurin toshe mata bakin ta hanyar haɗewa da nasa yana tsotsa cike da salon kauna wanda bata taba tsammanin hakan daga garesa ba, take ta nemi kukan ta rasa, sai wani bakon yanayi da ya ji ya ziyarceta.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
????????????????????????????
DAN ALLAH MASOYA LITTAFIN COLONEL UBAIDULLAH KUYI HAKURI, WLH ABU NE KAMAR WASA YANA SHIRIN ZAMA GASKIYA ???????????? KWATA KWATA LITTAFIN YA FITA A RAINA SAI KACE WACCE AKA MIN ASIRI, BA WAI LOKACI NE BAN DASHI DA ZAN GAMA KAFIN SALLAH BA AA ???????????? BUK DIN NE KAWAI NAJI YA FICE MIN FITTTT!!!! DAN ALLAH KU TAYANI ADDUA NA GAMA MU HUTU, KU KU HUTA NIMA NA HUTA ???????????? ALLAH YASA MU DACE AMEEN.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
????????????????????????????????????????????
WANNAN JAN FUSKAN SHIMA BANGARENSA DABAN, A WAN CAN PAGE DIN NACE KUBAN SUNAYENKU NA BAKU KYAUTAR PAGE KUKAYI KAMAR BAKU SANNI BA KO ???????????? AI KUN HUTA SAI DE KU NEXT PAGE, ZAKU JI SUNAYENKU HAR DA MASU MIN SHARHI A WATTPAD, UMMU AHLAN TANA GODIYA GAREKU MASOYA ABUN ALFAHARI????????????????