COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Anya kuwa ma kuna sharing din buk din idan kuka karanta? ????
Sorry 4 d typing..error ycn bazan iya editing ba ????????????????
Momyn Ahlan Taku Ce????????
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
~UBAIDULLAHI~••~~•~•~•~
my wattpab@Fateemah0••••~~•
Special gift to my 5 ☆stars★
Samira bint Abdallah????
Fatima bintu Sagir????
Farhat Mrs M’J????
Princess (Nafeesat)????
احلام فاطمة????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
HAPPY HAPPY HAPPY????????????????????????????????, HAPPY ANNIVERSARY KAINUWA WRITERS ASSOCIATION, 3YRS ALHAMDULILLAH, YA ALLAH KA KARAWA KAINUWA DARAJA DA DAUKAKA, ALHAMDULILLAH KAINUWA DASHEN ALLAH MAHASSADANKI FADAWANKI ???????????????? KOMAI SU KAI KI BARSU DA ALLAH, YA ALLAH KA KARA BAMU IKON TSARKAKE ALKALUMANMU WAJAN RUBUTA DAI-DAI, ALLAH KA TSARE ALKALUMANMU DAGA RUBUTA SHIRME ABUN DA BA ZAI AMFANE ALUMMA ANNABI MUHAMMAD S,A,W BA, INA MIKO MIKI JINJINA DA DUBUN GAISUWA TARE DA FATAN ALKHAIRI SHUGABA JA GABA ANTY FAUZA YAR AMANAR KAINUWA, ALLAH YA IYA MIKI, INA GAISHE DA KOWA DA KOWA NA KUNGIYATA, ALLAH YA KARA HAƊA KAWUNANMU YA KAƊE FITINA A TSAKANINMU, ALLAH YA KARA MANA HAKURI DA FAHIMTAR JUNA, (ZAHRA ABDUL MOMYN AHLAN INA YI MANA FATAN ALKHAIRI) UP UP UP UP UP KAINUWA WRITERS ALLAH YA KARA BASIRA DA DAUKAKA????????????
YAU PAGE DIN FA NA KU NE ????????
@???????? MEMCY???????? and……..???? yasin sis bansan asalin sunanki ba ???? (Oriflime ne ko miye ne uhum ????) sonso fisabilillahi. ????????????
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
page°°°°°96&100
Duk yaƙin da zasu je,da ya ga an kashe wani soja,ya kan shiga damuwa da tausayin iyalansu halin da zasu shiga, har misali yake yi da kansa yanzu ace gawarsa ce za a dauka a kai gida ya Mama za ta ji? Gaskiya sojoji su na matuƙar bakin kokarinsu, da zarar ka shiga aikin soja, to fa ka din ga rayuwa da sanin cewa za a iya farmaka ko wani lokaci,shi yasa da yawan wasu mata basu cika son auren soja ba, dan zaka yi sallama lafiya lafiya da Iyayenka da matarka amma ka je yaƙi a dawo da gawarka.
@@@@
Kwanarsu uku a kasan babbar rafin kashmeer ba ci, sai dai sha, haka suka sake komawa aka ci gaba da takaddama, ya yinda sojoji sun kashe yan ta’adda da yawa, kuma rundunar sojojin india na yankin kashmeer sunji labarin sojojin nigeria sun kawo farmaki dan anyi garkuwa da yan matan kasarsu, amadadin su kawo musu dauki tunda su ma yan ta’addan sun addabesu amma sai suka labe dan tsoron makaman da yan ta’addan suke dauke dasu, sunji labarin wani jami’in soja wanda ke zubar dasu miyagu izuwa kasa wanda shine ja ragamar yaƙi,wa hakan ne suke son ganin wanene wannan jarumin.
Nan fa sai dai suka sake share sati daya ana yaƙi, nan da kwana goma an kashe sojojin Nigeria guda goma sha uku, in da mutane ishirin suka ce su kam guduwa za su yi, Ubaidullah yace shi kam ko zai mutu babu inda zai je dan ya ɗau alkawari sai ya kubutar da mata da yardan Allah.
Sojoji 20 da suka koma gida su ne suka bada labarin tashin hankalin da sojojinsu suke ciki, tare da sunaye da hotunan wa inda aka kashe, sosai hankalin General Of The Army da sauran manya ya tashi, dan kuwa sojoji masu nagarta aka zaba aka tura, Major Usman ne ya ce.
“Su Captain Ubaidullah fa?” nan wani soja ya ƙame yana bawa Major Usman amsa da cewa.
“Haƙiƙa Captain Ubaidullah jarumi ne yawancin yan ta’addan da aka kashe shine ya kashesu, kuma yace ba zai dawo ba ko da kuwa zai mutu sai ya karbo yan matan da aka yi garkuwa dasu, gaskiya shi din jarumi ne gagara gasa” murmushi Major Usman ya yi, nan aka fara shawarar ƙara tura wasu jami’ai amma kowa saffewa yake yi, dan ga shi nan wasu sun gudu, su kuma sai su kai kansu.
Tun basu dawo ba, labari ta baza duniya na mutanen da aka kashe a india, wanda suka yi jarumta suka mutu a fagen yaƙi.
@@@@
Zaune take gabaki ɗaya ta rame tayi duhu, da ka ganta kasan bata cikin walwala da kwanciyar hankali, hayaniya ke tashi bisa alamu dai shagali ake yi, dago ido tayi ta kalli Mama wacce take ta murmushi a cikin jama’a amma a zahirin gaskiya idan ka kalli cikin kwayar idonta kasan itama ba bata tare da natsuwarta, yan uwana ake ta shige da fice, ana shirin zuwa lunching na Safwan da Shafa’atu, Ummi ce ta ratsa cikin mutane ta zo gaban Abi’atu tana kallonta, ita kam ma Ummi kallon mai ciki take yiwa Abi’atu,
“Ke Abi’atu ba za ki je lunch din bane? Kin zauna da kayan bacci kin kasa wanka? Ga jama’a da yawa a gida, ki tashi kije kiyi wanka ki cire wannan kayan bacci da hijabin ki zo, idan ma ba zakije lunch din ba kiyi wanka ki zama mutum a cikin mutane, ke ma Hafiza kin zo kin zauna a nan tashi kije ki shirya kema, tun da babu igiyar kowa a kanki, ita da take da igiya a kanta take fama da guntayen ciwuka sai ta zauna a gida” mikewa Hafiza ta yi ta amsa da “to Ummi” ta fice daga parlour tana fitowa gate wani soja ya rakata har izuwa bakin gate din gidansu kafin ya tsaya a gate din, Abi’atu kuwa haɗe rai tayi sosai ko kallon Ummi ba ta yi ba, Mama ta yi dariya ta ce.
“Ummi , ki fa bar min yarinya tasha iska”
“Haba Mama wani irin shan iska dan Allah, gida da mutane amma ta zauna da kayan bacci da hijabi?” Mama ta sake murmushi dan itama ta dauka Abi’atu ciki ne da ita, amadadin Abi’atu ta tashi sai ma gyara kwanciyarta da tayi dan wani irin haushin yan shagalin bikin take ji, Mijinta na can yau kusan wata ba ta ji lafiyarsa ba, amma wai su na shagalin biki, shagalin banza shagalin wofi, to wallahi ba zata yi wankan ba ma yau gaba ɗaya, har wa inda zasu tafi lunch suka gama shirinsu suka tafi abun su Abi’atu tana kwance bata saka lahadin tashi ba, rintse ido tayi tana taro dukkan moment dinsu da Ubaidullah har izuwa ranar da zai tafi ya furta mata kalmar yana sonta, wasu zafafan hawayen ƙauna ne suka wanke masa fuska, ta yi saurin gogewa ta jawo wayarta ta shiga cikin galary, pics dinsa ta hau kalla tana murmushi dan abun da yake iya sanyaya mata zuciya kenan, pic dinsa ta saka a wallpaper na screen din ta da kuma na WhatsApp dinta, kunna data ta yi ta shiga media, abun da ta fara karo dashi shine yayi matukar gigita mata hankalinta da natsuwarta Facebook twitter Instagram yawancin kafofin sada zumunta hotunan sojojin da aka kashe a india ne, Abi’atu tana gani ta saki wani kururuwan da sai da gidan gaba ɗaya ya amsa,a kiɗime aka yi kanta, ihu take tana ” wayyo Allah Mijina!” Ummi ce ta zo da sauri ta rirriƙeta tana tambayarta menene, nan ta nuna musu abun da ta gani, Ummi ta ce.
“Haba Abi’atu sai kace ba musulma ba?za ki saki wannan kururuwa haka, su yan uwansu da suka ga gawarsu su kuma su yi yaya kenan? Ko kin ga Ubaidullah a cikinsu ne?, ki ci gaba da masa addua a matsayinki ta matarsa, Allah ya basu narasa su dawo a sa’a, su kuma wa inda suka mutu Allah ya gafarta musu, sosai Ummi ke lallashin Abi’atu dan hankalinta ya kwanta duk da itama Ummi hankalinta a tashe yake bata so ta nunawa Abi’atu hakan ne, dan Abi’atu bata iya tsorata ba, yanzu sai ta ri ga Ubaidullah din ma mutuwa idan shi bai mutu a yaƙi ba, to Abi’atu sai ta mutu a fargaba, ga shi tana tsoro kar wani abu ya sami abun da yake cikinta, a cewar Ummi, bata san babu abun da ya taba shiga tsakaninsu ba balle aje ga ciki, lallashi iya lallashi babu wanda ba ayi wa Abi’atu ba amma sam kamar ba da ita ake yi ba, tace ita tana so ne ta ga mijinta, har yan lunching aka dawo aka saka Abi’atu a gaba, dasu Mama, nan dai aka nemi number ta barracks din su Ubaidullah aka kira, Safwan ne ya yi magana akan cewa ko akwai hanyar da zasuyi magana da Ubaidullah? Da taimakon Major Usman aka tura dan sako zuwa ga Ubaidullah ana so aji lafiyarsa, su na tsaka da yaƙi sako ta iskesa, dama shima yayi missing dinsu amma baya da halin zaman da zaiyi waya dasu, abun da ya sani shine kullum su na zuciyarsa, da kyar ya koma gefe ya samu nertwork ya kira gida, Mama ce ta fara ɗagawa tana jin muryarsa ta kasa magana, da kyar ta iya bude baki ta ce.
“Babban Yaya kana lafiya?” murmushin karfin hali ya yi ya amsa da ina lafiya Mommana, fatan kuna lafiya dukkanku?” Mama ta amsa da eh sannan ta mikawa Abi’atu, tana karba ta saka masa kuka, ya rintse ido a hankali ya ce.
“My Muahh, menene abun kukan?” kasa magana ta yi, jin ba zata yi shuru ta daina kukan da tayi masa magana ba ya ce.
“Idan ba ki min magana ba, zan ajiye wayata, me kikeso?” cikin sheshsheƙa ta ce.
“Ina so ka dawo”
“Bayan wannan fa?” ya tambayeta cike da damuwa.
“Ina so na ganka”
“Okay bari na kiraku video call” ya fada ya tsinke wayar ya kira ta video call da suka gansa da ace a hanya suka hadu zasu rantse ba shi bane, dan wani baƙin da ya yi ga wani uban rama, Mama bata san lokacin da kuka ya kubuce mata ba ta tashi da sauri ta fice, Ummi ma sai da suka share hawaye, nan kukan Abi’atu ya tsananta ganin yadda mijinta ya koma duna baƙin wake, nan ta shiga yi masa magiya ya dawo, da kyar ya kwantar musu da hankali, su na kan magana nertwork ya dauke, Zaidu ma ya samu ya yi waya dasu Umma, Inna kuwa itama harda kukanta dan basu taba tafiya yaƙi mai azaba irin wannan ba.