COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

@@@@

Abu kamar wasa yau watansu Ubaidullah uku, idan ka ga yadda suka koma abun ba a cewa komai, an kashe sojoji ashirin da uku, yayinda da yawansu suka gudu suka koma gida, acikin su dari da saba’in da bakwai, saura mutum sittin da tara, kuma yanzu alhamdulillah sun gano inda yan matan suke kwacosu suke son yi, su yan ta’addan sun kashe sojoji 23 amma su an kashesu ta yadda ba zasu kirgu ba, kuma ogansu ya gane Ubaidullah dan a cikin kashi dari na wa inda aka kashe musu Ubaidullah shi ya kashe kashi tamanin, dan haka suke son kashe shi amma abun ba mai sauki bane.

Cikin dare su Ubaidullah suka dirƙa musu ya yinda suka sake kashe wasu daga cikinsu, da kyar da gumurzu Ubaidullah ya fidda yan mata kwantena daya, wanda a daren suka baro kashmeer, inda Commender Isa Bala ya sanar da L-General nan kuwa da washe gari aka kwashi yan mata aka mai dasu kasarsu, inda wasu ke kukan murna da farin ciki dan har sun fidda ran zasu dawo mahaifarsu, a 9ja barracks aka ajiyesu inda ake musu tambayoyi su na kuka suke bada amsa, kafin su fara bada bayani sai da suka ta zubawa Ubaidullah addua, inda suke jawabi akan cewa siyar dasu ake yi a matsayin ƙaruwai, ko a siyar dasu bayi marasa galihu, su ma kuma idan bukatarsu ta tashi su na zuwa su zaba wacce suke so su keta mata haddi idan kuma ta ƙi amincewa su kasheta, sosai aka dinga naɗan rahotanninsu, inda a kwana biyu labarai ya karaɗe media, aka haɗa wasu da iyayensu.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Ubaidullah sai da suka sake diban kwana shaɗaya kafin da kyar da suɗin goshi suka sake kubutar da kwantena daya saura daya, inda sun sha baƙar wahala kafin su fidda na biyun, inda da yawan sojoji suka ce wlh ba zasu iya ba sunyi wa inda zasu iya yi, nan kuwa da yawa aka koma gida, su Ubaidullah wanda suka rage basu fi su ashirin da bakwai ba, Ubaidullah ya ce In sha Allah sai sun kubutar dasu, a wannan yanayi fa yan ta’adda sun ragu ba kaɗan ba, abun farautarsu kuma wanda suke nema ido buɗe ba ido rufe ba, shine Ubaidullah, wannan kwantena ɗayan da ya rage su Ubaidullah sun ji jiki matuƙar jin jiki, inda mutane goma suka sake mutuwa, nan suka rage su goma sha bakwai inda mutane goman su ma suka ce wlh su ma sun gaji suka gudu, su Ubaidullah suka rage su bakwai.

A ranar da Ubaidullah ya ballo kwantenar karshe su na kokarin guduwa ne ogan yan ta’addan ya harbi Ubaidullah yana kan gudu bayan yasa sojoji hudu sun gudu daga kashmeer da yan matan, sannan tun kafin ya fiddosu sai da ya kira rundunar sojojin yankin kashmeer akan azo a tafi da sauran yan ta’addan sun yi musu aiki mai wahalan, kafin sojojin su karaso shine ogan yan ta’addan wanda ake kira Zaffar ya harbi Ubaidullah a kafaɗa, dama su uku suka rage daga shi sai Zaidu da KB, dai-dai nan sojojin indian suka karaso, kafin su yi wani yunkuri Zaffar ya sake harbin Ubaidullah a damtsen hannu, da karfi Zaidu ya kira sunan Ubaidullah, ganin haka yasa Zaffar saita bindigarsa a saitin Zaidu zai harbi Zaidu ganin haka Ubaidullah cikin ɗauriya yasha gaban Zaidu aka sake harbinsa inda bullet din ya shige wajan gefen ƙirjinsa wanda yasa numfashinsa tsayawa cak!!, Zaffar na shirin sake harbi da gudu KB ya shaƙosa, kafin sojoji suka kamasa da sauran yaransa, Ubaidullah na tsaye sai zufar dake keto masa ta ko ina sabida azaba, sai da ya kalli Zaidu ya saki murmushi gami da cewa, “ALHAMDULILLAH!” sannan idanuwansa suka ƙisfe nan ya zube kasa wanwar.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

A lallaba ????

UMMU AHLAN TAKU CE????????

Nayi nan sai kuma gobe in Allah ya kaimu ????????????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️????????‍♀️
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

~UBAIDULLAHI~
•~~•~•~•~

my wattpab@Fateemah0
•~~•
Special gift to my 5 ☆stars★
Samira bint Abdallah????
Fatima bintu Sagir????
Farhat Mrs M’J????
Princess (Nafeesat)????
احلام فاطمة????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

________________________

SAKON BARKA DA SALLAH GA DAUKACIN YAN KUNGIYATA ABUN ALFAHARINA, TUN DAGA IYAYENA YAYUNA, ƘANNENA, KAWAYENA ANA TSAFTAR TARE KO BA WUYA, ALLAH YA KARAWA KAINUWA BASIRA DA DAUKAKA ????????

Anty Fauna ƴar amana
Batul Adam Jattako
Ummy On top
Kadija Usman Ta me gari
Maryam Umar (mmn Yusuf)
Ummu Fatima
Hauwa’u Salisu Haupha
Real Nana Aisha
Manab ƴar baba
Rasheedat Usman (Ummu Nasmah)
Fauziya Auwal Alin Baba Jingau
Nabilancylv
Fiddausi S.bak’i (Smart Feenat)
Haleemat Hassan Leemat
Jamila Sumaila Yusufa
Zahra Faruk
Hussy Sani
Amina Fistlady
Pretty Mardy
Maryam Marsad
Deeja Alkali
Maman Noor
Nimcylv

INA YINKU, ALLAH YA KARA HADA KAWUNAN MU ????????????

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

page°°°°°91&95

Azaba iya azaba, sun sha ta a wajan Ubaidullah da Zaidu, har wajan kwana uku, a yau ne kuma zasu bakunci lahira, videos din fyaɗe Ubaidullah ya kira Abi’atu ya bata aikin yaɗawa a ƙafofin sada zumunta, sannan ta yaɗa labarin masu ta’addanci da b’arna a doron ƙasa, masu lalata ƴaƴan jama’a, wanda yake sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu, da yawan mutane anyi commemts inda kowa ke tofa albarkacin bakinsa, yayinda mutane da yawa suke bawa sojoji goyon baya akan idan an kama masu laifin a kashesu kawai ko za a samu a rage mugayen iri a cikin jama’a, dan har yau bamu ji wani hukunci mai tsanani da ƙasarmu nigeria ta dauka ba akan masu fyaɗe, yayinda rundunar sojojin su Ubaidullah ta samu ƙwarin guiwa dari bisa dari, mota suka shiga dasu, sannan suka dauki hanyar jejin nasarawa, tafiyar awa daya ce da yan mintoci ta dauke su, ya yinda suka isa jeji suka fito dasu, jera su suka yi, Ubaidullah yana binsu da kallo yana kallon videon yaran mutane masu ihu su na neman akawo musu dauki, daga cikin har da na kanwarsa NA’ILAH, abun da yake kara tunzura shi, da aka tambayesu wai tsautsayi ne da sha’awa, to idan sha’awa ne why not ka je gidan karuwai ka dauko karuwa ka biyata kayi da ita da son ranta? Amma sai ku din ga bin yaran mutane ƙanana kuna keta musu haddi, a kalla wa inda suka mutu sun kai hamsin, dan ko wata babbar mace ba lallai bane ta iya dauke bukatun Namiji balle yara kanana wanda babu wa inda suka haura shekara sha hudu ƙasa da haka a cikin yaran da suka yi wa fyaɗe, Ubaidullah ne ya saita bindigarsa akan saitin goshin daya daga cikinsu, har yaja kunnaman bindigar zai saki ya ji wayarsa ta dauki ruri, da kamar ba zai duba ba, sai kuma ya duba ya ga bakuwar number, nan zuciyarsa ta shiga waswasi ya ɗaga ne ko kar ya ɗaga, nan dai wata zuciyar tace masa ya ɗauka, yana dagawa yaji ana gargaɗa masa kasheɗi da kakkausar murya.
“Hloo!!! Da Captain Ubaidullahi nake magana!?” sai da Ubaidullah ya shaƙi iska kafin ya amsa cike da izza ya ce.
“Wanene kai!? Me kake neman Ubaidullah din zaka masa!?”
“Kaiii!! Yaro!! Dama ance min kana da ji da kai, sabida kana fama da yarinta, abun da nake so da kai shine kayi gaggawar sako min yarona ya dawo gida, zan biyaka koma nawa ne, amma Ɗana daya tilo ya dawo gareni, karka sake ka cutar min da yaro, idan ba haka ba ko hummmmmm!!!!” wani ƙalulun baƙin ciki ne ya taso ya tokarewa Ubaidullah maƙoshi, ya ce.
“Wanene kai!?ya sunanka!? kuma ya sunan Ɗan naka!?”
“Ni ne ALHAJI MADUGU UBAN KUƊI sannan UBAN BANGIS ina so ka sako min yarona, dan shi kadai na mallaka zan iya sadaukar da dukkan dukiyata a kansa, duk abun da yarona ke so shi nake so, dan ina da kudi, ina so ka kai case dinsa kotu, karka sake wani abu ya samu Ɗana!!” ya fada cike da tsawa, b’acin ran da Ubaidullah ya shiga baya misaltuwa, wai gargaɗi yake masa kar wani abu ya samu Ɗansa, shi kuma Ɗan nasa da ya cutar da yaran mutane su ba da jini aka yi su ba kenan?, kallon Zaidu ya yi da jan ido sannan ya yiwa Zaidu alamu da hannu ya matso sannan ya matso kusa da samarin yana kallonsu, bude handsfree ya yi ya ce.
“A cikinku waye Bangis!?” a wahalce Bangis ya ɗago da sauri da kyar yake iya bude baki ya amsa da shi ne, dan fuskokinsu a kumbure suke dan Ubaidullah sun canza musu tsarin zubin halitta, Ubaidullah ya ce.
“Alhaji Madugu kake ko wa ma? ga Ɗanka nan, tabbas zan baka Ɗanka, ba ma sai anje kotu ba, amma GAWARSA ZAN BAKA ka zo jejin narasawa ka ɗauki gawar yaronka!!!”
“Kada ka sake kayi wannan gangancin Captain Ubaidullah!! Ina gargaɗinka!! kar wani abu ya samu yarona!! Za ka jefa kanka cikin masifa da bala’i, dan baka san waye ake kira da ALHAJI MADUGU UBAN KUƊI BANE!!
“Tirrrrr!! Da masu hali irin naka, kai ma baka san waye aka kira da CAPTAIN UBAIDULLAH BANE!! ALHAJI MADUGU!!! BANA TSORONKA, YARONKA KUMA NA GAYA MAKA KAZO KA DAUKI GAWARSU SHI DA ABOKANSA A JEJIN NASARAWA!!
“Captain, kar yarinta ta jefaka aikin danasani!!! Kar wani abu ya samu yarona!!!” kallon Bangis Ubaidullah ya yi ya ga ma shine wanda ya fara yiwa Na’ilah fyaɗe a cikin su bakwai din nan, idonsa jajayen hawaye ne kwance, cikin ƙunar zuciya Ubaidullah ya ce.
“Alhaji Madugu!!, yadda na rungumi Gawar Ƙanwata na sakata a karkashin ƙasa a sanadiyyar bata garin ƴaƴanku, kaima ina mai farin cikin sanar da kai da cewa za ka rungumi gawar Ɗanka ka saka shi a karkashin ƙasa, bari ma na fara maka alama yanzu ka jiiii!!” Ubaidullah ya faɗa gami da harbin Bangis a kafa, ihu Bangis ya saka gami da ya kwalawa mahaifinsa kira, ya yinda hankalin Alhaji Madugu ya yi muguwar tashi jin karar bindiga da ihun ɗansa, nan Ubaidullah da Zaidu suka buɗe musu wutaa!! Nan suka shinfiɗe su matattu( INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN, YA ALLAH KA RABAMU DA MUMMUNAR KADDARAR RAYUWA, BIJAHI NABIYYUL RAHMATI AMEEN) ajiyar zuciya Ubaidullah ya sauke sannan yasa wayar a kunnensa ya ce.
“Alhaji Madugu ya ka ji Kururuwar Ɗanka? Shin abun ya maka dadi? Nima haka na ji na Ƙanwata, har lokacin da take ihun azaban fitar rai, dan haka kaima ka ji ƙunar da muka ji, ina kara gaya maka, ka zo jejin nasarawa ka dauki gawar danka da abokansa” Ubaidullah ya faɗa yana shirin ajiye waya ya tsinkayo muryan Alhaji Madugu yana cewa.
UBAIDULLAH!!! HAƘIKA KA TAROWA KANKA YAƘIN DA BA ZAKA IYA DA ITA BA, NA RANTSE DA ALLAH!! NA RANTSE DA ALLAH!! NIMA SAI NA DAUKE ABU MAFI SOYUWA A GAREKA, SAI NA RABAKA DA FARIN CIKI NA HAR ABADA, TUN DA KA KASHE MIN ƊANA, KA RUBUTA KA AJIYE, ALHAJI MADUGU UBAN KUƊI BAYA YAFIYA BAYA MANTUWA, ZA KA SAN CEWA KA KASHE GUƊAN JININA!!!”
Murmushi Ubaidullah ya yi ya ce.
“Game over Alhaji Magudu, duk wanda ya kashe a kashesa, ko ba komai watakila zamu samu sa’idan fyaɗe, karkayi yunkurin shiga rayuwata Alhaji madugu, dan kuwa zaka ƙare rayuwarka a gidan mazaa!! Ubaidullah ba kamar sauran mutane bane wanda ka sani, dan haka kai ma ka kiyaye!!” sannan ya katse wayar ya durkusa akan guiyoyinsa gami da fashewa da kuka, dan shi kaɗai yasan tashin hankalin da yake ciki, Zaidu ne ya dagosa shima kukan yake, da kyar Zaidu da KB da wasu sojoji mutum uku aka kamo Ubaidullah aka saka shi a mota suka koma barracks, sun yiwa Lieutenant colonel bayanin komai sannan ya ce su bar case din kawai an rufe an gama da shi, aiki na gaba da zasu faɗa shine wanda zasu tafi india, Ubaidullah an yi masa magana akan su Rumaisa ya ce baya da lokacinsu, dan haka Zeey ne da kanta ta sa aka kori su Rumaisa daga barrack, duk abun da ya faru Ubaidullah yana waya da gida kuma yana sanar dasu duk halin da ake ciki, Mama hankalinta ya tashi jin yadda Ubaidullah suka yi da Alhaji Madugu, cikin tsoro Mama ta ce.
“Yaya Babba kana ganin babu wata matsala kuwa? Dan gaskiya naji hankalina bai kwanta ba, karka manta fa, ba kasan wanene shi Alhaji Madugun nan ba fa!?”
Murmushin takaici Ubaidullah ya yi ya ce.
“Mama, shi ma bai san wanene Ubaidullahi ba, ki kwantar da hankalinki, ko ba komai yanzu zuciyata ta yi lafiya na hukunta wa inda suka kashemin Ƙanwata da kakina, adduarki kawai nake bukata, yau saura kwana uku mu tafi aiki, ban sani ba Mama ko zan dawo a raye” jikin Mama ne ya yi mugun sanyi ta ce.
“Karo na farko kenan daga fara karya min guiwa, karkasa zuciyata ta tsinke, nina san wanene yarona kuma na yarda da shi,kamar yadda shi ma ya yarda da kan shi, a ko da yaushe kana tare da nasara Ubaidullah, Allah ya muku albarka” ya amsa da ameen, Mama ta kuma cewa.
“Dazu fa naje na samu su Umma da Inna, mun jima muna magana, gani nayi me zai hana Zaidu ya auri Hafiza? Tun da na ga ya so Yar Uwarta amma Allah bai yi da rabon aure a tsakaninsu ba, kuma da Hafiza da Na’ilah tsantsa ɗaya suka fito, su Umma da Inna dai sunyi na’am da shawarata, kuma na gayawa Ummu itama tayi na’am, ban san kai ya zaku dauki abun ba kai da Zaidu, amma idan Hafiza tayi aure ta zauna a gidan Zaidu hankalina zai fi kwanciya dan nasan Zaidu zai kula da ita tamƙar Yar Uwarta, amma kai ya ka gani?” gauron numfashi Ubaidullah ya ja gami da cewa.
“To shi kenan Mama, zan yiwa Zaid din magana, nasan ba zai ƙi Hafiza ba, amma dudu fa Hafiza she’s 14 ne fa kawai yanzu take kokarin shiga 15yrs Mama ba ta yi ƙarama ba kuwa wa Zaidu?” murmushin Manya Mama ta yi ta ce.
“Ubaidullah kenan! To idan kana ganin ta yi karama zata karasa girman a gidansa” ya sake yin ajiyar zuciya, nan dai suka ci gaba da tattaunawa a karshe suka yi sallama, ko da Ubaidullah ya samu Zaid da maganar bai damu ba, ya nunawa Ubaidullah amincewarsa dan da kunya yace masa aa , amma a can kasar zuciyarsa har ga Allah Na’ilah ce dan yarinyar ta kasa fita a ransa, dama yara masu kiriniya shiga rai ne dasu, dan haka Ubaidullah ya sanar dasu Mama Zaid ya amince idan Allah ya yi dawowarsu sai asha biki, ko da Hafiza ta ji labarin za a hadata aure da Yaya Zaid hankalinta ya tashi dan tasan irin son da Yaya Zaid ke yiwa Sismie dinta, su Afnan kuwa murna suka hau yi Hafiza zata dawo gidansu da zama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button