COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
SAKON BAN HAKURI GA MASOYANA ???????? A TAYANI DA ADDUA BUK YAZO GANGARA AMMA GAMAWA YA ZAMA AIKI, BUK DIN NAN ZAI KAMMALU NE A CIKIN SATIN NAN DA YARDAN ALLAH, AMMA DA TAIMAKONKU MASOYANA, TA HANYAR ZUBA MIN SHARHI WANDA ZAI SAKANI POSTING SAU UKU A RANA ????????, INA KARA BAKU HAKURI, BARKANMU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA AMEEEN ????????????????????????
MOMYN AHLAN TAKU CE????????
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
~UBAIDULLAHI~••~~•~•~•~
my wattpab@Fateemah0••••~~•
Special gift to my 5 ☆stars★
Samira bint Abdallah????
Fatima bintu Sagir????
Farhat Mrs M’J????
Princess (Nafeesat)????
احلام فاطمة????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
????????????
OH ALLAH NA NI ZAHRA UWAR AHLAN, TUN BAN DAUKI MAGANAR DA WANI MAHIMMANCI BA DA ZANYI MAGANA AKAI, AMMA SAKON DA NA ISKE A PC DA KUMA KIRAN WAYA YA SA ZANYI MAGANA, AKAN PAGE DIN DA YA GABATA KAFIN WANNAN, WAI KAR NA KASHE UBAIDULLAH IDAN YA MUTU LABARI YA B’ACI, TO INA DA YAR TMBYA, “SHIN YA SUNAN BUK DIN NAN NE KAM? INA CE SUNAN SHI COLONEL UBAIDULLAH NE? KUMA HAR YANZU UBAIDULLAH YANA CAPTAIN NE BAI JE COLONEL BA, TO IDAN YA MUTU MA NI ZA A NAƊAWA COLONEL DIN? ???? ) DUK MA BA WANNAN BA, A RAYUWA BA KOMAI KAKESO YAKE ZUWA MAKA YADDA KAKESO BA, INA SO KU FAHIMCI HAKAN PLS, KAR MU DIN GA RAYUWA AKAN SON ABUN DA MUKE SO DAN ZA TA IYA KASANCEWA BA ALKHAIRI BANE, DA YAWA WASU BA WAI SU NA KARANTA NOVEL DAN SAKON DA YAKE CIKI BANE, WASU SU NA KARANTAWA NE DAN NISHADI KAWAI, PLS AND PLS, KAR MU DIN GA TAFIYA A NISHADI, A TAFIYA ANA SO A DIN GA WAIWAIYE( HAUSA CE) FATAN KUN FAHIMCENI, AHA MASOYANA MUJE DAI A CI GABA DA KAFTAWA ????????♀️????????♀️????????♀️????????♀️????????♀️
page°°°°°101&105
“Ubaidullahhhhhh!!!?” Zaidu ya furta da karfi ya dagosa yana jijjigasa cikin tashin hankali, da sauri shi ma KB yazo suka rungumi Ubaidullah su na ambatar sunansa cike da tashin hankali, cikin gaggawa sojojin india suka yo kan Ubaidullah, nan suka taimaka aka saka shi a mota sai asibiti ma fi kusa da Kashmeer, nan aka wuce emergency da Ubaidullah, faɗin halin da su Zaidu suke ciki abun baya misaltuwa, ko da suka sanar da barrack dinsu an harbi Ubaidullah nan barrack ta rikice, kafin kace me labari ya karaɗe barrack akan sojojin 9ja barrack sunyi nasara amma an harbi jarumi Ubaidullah.
Likitoci su na ta faman kokarinsu wajan ganin sun cuto rayuwar Ubaidullah in da babu bata lokaci suka shiga yi masa aiki dan cire masa bullet din da yake jikinsa, kasancewar kasashen waje sun fi kasarmu bada attention akan marasa lafiya, kusan kwana suka yi su na aiki akan Ubaidullah dan harbin da aka masa wajan gefen ƙirjinsa kiris ya rage bai wuce ya huɗa masa zuciyarsa ba Allah ya taimaka, amma da ace Zaffar ya sake harbinsa wajan saitin wajan ba ma kawa da ya mutu, bayan sun gama yi masa aiki ne suka saka shi a cormer dan kuwa yana cikin mawuyacin hali.
Satin Ubaidullah ɗaya a comer har yanzu bai san inda yake ba, dan ba fiddo shi aka yi ba, harta su Zaidu sai dai su hangosa ta glass, sosai yake samun kulawa wajan jami’ai da kuma hukumar sojojin india da na ƙasarsa nigeria, su ma su Zaidu sosai suke bawa Ubaidullah kulawa dan burinsu bai wuce su ga Ubaidullah ya samu lafiya ba.
@@@@
Da yawa mutanen nigeria sunji labarin cewa jaruman sojojin sun kwato yan matan da akayi garkuwa dasu, kuma da ake zantawa dasu sun fadi wanda ya fiddosu amma abun daurewar kai din shine ina CAPTAIN UBAIDULLAH din yake ? Dan kuwa ance kar a faɗi abun da ya same shi ya zama sirri har sai ya ji sauki tukunna.
A gida kuwa ganin labarai ya karaɗe yan mata sun dawo kasarsu da yawan sojojin ma sun dawo, daga ciki har da commender’n yaƙin amma babu Ubaidullah ba Zaidu ba KB, nan fa hankalinsu Mama ya tashi fiye da misali, nan suka din ga azalzalan yan barracks din su Ubaidullah inda a karshe Major Usman ya ce kawai a fadawa duniya gaskiya tun da Allah yasa Ubaidullah din bai mutu ba, nan kuwa aka yi kiran manema labarai inda Major Usman ya wakilci 9ja barracks da Abacha barracks ya yi jawabin akan mashahurin sojan nan wanda yake sadaukar da rayuwarsa wa kasarsa inda Major Usman yake cewa masoyan Ubaidullah su taya shi da Addua dan lokacin da ya kubutar da yan matan kwantenan karshe aka harbesa yanzu haka yana asibitin kasar india yana samun kulawa, a yankin kashmeer wajan kusa da inda suka yi yaƙin, kuma a halin yanzu yana cikin comer dan Allah masoya a taya shi da addua Allah ya tashi kafadunsa, domin ace an rasa mutane kamar su Ubaidullah ba karamin babbar asara aka yi ba, da haka jama’a suka gamsu yayinda kuma suke yiwa Ubaidullah fatan samun lafiya.
@@@@
Ko da Abi’atu ta ji labarin an harbi mijinta yana cikin comer a take ta zube kasa sumammiya, ruwa-ruwa aka yi da ita asibiti, ko da ta farka kuka ta din ga yi tana kiran sunan mijinta, kwananta uku aka sallamota, nan suka koma gida amma hankalinsu ba a kwance yake ba.
@@@@
Satin Ubaidullah biyu aka fito dashi daga comer inda ya farfado jikinsa da sauki amma da alama yasha wahala ya ji jiki, kwanarsa uku da fitowa ya fara shirin komawa kasarsa, kafin ya farka manyan sojojin nigeria duk sun zo duba shi, a daren ranar da zasu koma nigeria nan shugaban sojojin india yazo ya samu Ubaidullah da wani zancan, kallon marar hankali Ubaidullah ya masa kafin yayi wani murmushi mai wuyar fassara,ba wani abu bane illa su na so su siye Ubaidullah ya dawo kasarsu da zama ya shige cikin rundunarsu, dan sun yaba da jarumtarsa, ba yaudara ba boye-boye Ubaidullah ya ce.
“A yawan kasashe na duniya, dukkan dan ƙasa yana kaunar ƙasarsa,amma babu wanda suke nuna fiffiko akan kasarsu sama daku, kun mai da kasarku uwa kamar yadda kuke furtawa, babu abun da ba zaku iya yi ba akan kasarku sabida kishinta da kukeyi, nima hakan take a wajena, ina aikine wa ƙasata ba dan albashin da nake dauka ba, illa alƙawari da rantsuwan da nayi na kare ƙasata da dukkun baiwar da Allah ya bani, dabadin gumi na halak da nake ci ba, da sai na bar karban albashi, sabida son ƙasata da nake yi nima, ALLAH YA ƊAGA NIGERIA!!” Ubaidullah ya fada yana sarawa shugaban sojojin india, ba karamin sanyi jikinsa ya yi ba, haka ya tashi ya fita yabar Ubaidullah, ko dasu Zaidu suka tambayesa wani magana ne sukavyi da shugaban sojojin india dariya kawai Ubaidullah yabyi kafin ya basu labari, zare ido KB ya yi jin makuɗan kudin da zasu biya Ubaidullah, Zaidu ya ce.
“Su fa naga alama sun raine mutane wallahi” Ubaidullah ya ce.
“Manta dasu kawai” nan suka ci gaba da shirinsu, ko da washe gari da zasu baro india a motar asibiti aka kai Ubaidullah airport, su Zaidu ne suka taimaka masa lokacin da zasu shiga jirgi, an saka masa bandage a wuyarsa wanda aka rataye masa hannunsa, bayan sun zauna Ubaidullah ya lumshe ido yau yana cikin farin ciki marar misaltuwa zai je ya ga iyalansa wata kusan biyar kenan rabon shi dasu, su Zaidu ma haka murna suke yi.