COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Hanan!Hanan!Hanan!
Wata yar budurwar yarinya mai ƙarancin shekaru dan ba zata gasa 17yrs ba ta fito tana yatsine fuska tana binsu Ubaidullah da kallon banza.
Hajiya Jamila ta ce.
“Hanan je ki cewa dadynki yaransa su na nemansa, turo baki tayi tana ƙunƙuni ta juya ta haura upstairs din daddynta, kamar da minti bakwai suka sauƙo tare.
Yana ganinsu yayi murmushi ya ce.
“Ah Captain Ubaidullah and Captain Zaidullah I hope dai everything is fyn,na ganku at this tym”?
Sara masa suka yi kafin suka haɗa baki wajan cewa “yes sir everything is fyn Alhamdulillah mun zo neman permission ne, b4 mu tafi border muna so muje gida.”
General ya ce.
“Okay no problem kuna iya tafiya next 2morrow”
Godiya suka yi sannan suka miƙe zasu tafi har sun kai bakin kofa ,general ya ce.
Hope ba daɗewa zakuyi ba?
Zaidu ya ce.
“Eh sir 5days ne kawai”
Jinjina musu kai yayi sannan suka fice ,Hanan sai kallon Ubaidullah takeyi tasan tana da ji da kai da girman kai amma bisa alama Ubaidullah zai fita zafi ,duk da ta yi musu kallon banza amma taji wani abu aranta akan Ubaidullah.
******agurguje
Yau ne su Ubaidullah zasu je ganin gida sun shirya tsaf K,B ya ce.
“Wallahi da nasani dana tambaya na biku amma nasan halin general yanzu kam ba zai barni ba”
Zaidu ya kwashe da dariya ya ce.
“Sunan ka sorry kawai”
bye bye sai mun dawo, K,B ya kai masa dukan wasa ya kauce yana dariya ,a tare suka fito ya rakosu har mota suka shiga yana ɗaga musu hannu suka fice daga barracks , suka ɗauki hanyar garin BAUCHI STATE…..
~~~~
SAI FA HAKURI???? MY FANS INA BUKATAR ADDUARKU AKAN WANNAN LITTAFIN DAN WLH TYPING …YANA BANI WUYA
COMMENTS
&
SHARE
BY MOMYN AHLAN✍????????????♀
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶••••~~
MARUBUCIYAR
( HALITTA DAGA ALLAH NE)
( GUDU A JEJI)
( SHUHADA)
( NIDA ƘANNAN MIJINA)
TYPING…( WA’YA KASHE ZAHRA’U?) #200
my wattpab@Fateemah0
QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????
Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako????????
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________
page°°°°7&8
Su na shiga garin Bauchi Ubaidullah ya jinginu da sit ya lumshe ido yana shaƙar ƙamshin garinsa, da shike yanzu Zaidu ne ke driving din motar, dan bayan sun tsaya a jos suka yi sallah Zaidu ya karbi driving din kasancewar Ubaidullah ne ya ja su daga Abuja to jos, shi kuma Zaidu ya ja su har garin Bauchi.
Dukkan su sun yi shuru babu mai magana wa dan uwansa, ko wannen su da abun da yake tunani.
Ubaidullah sai cool smiling yake saukewa a beautiful face dinsa , ga wani happiness da yake ciki.
Zaidu ne ya ƙatse shurun ta hanyar cewa.
“Ubaidullah dan Allah zan fara sauƙa a gida”
“Okay Captain Zaidu tun da kasan ni ai ban yi missing din gida ba, kai ne kayi missing,mtsww”
“Oh Allah, Ubaidu Allah ya shirye ka, ni fa ba wani abu nake nufi ba, kaga motar ka ce, ni kuma wallahi a gajiye nake ba zan iya mu fara zuwa gidanku ba, ka bar ni da wangale baki”
“Kai dai kasani,” cewar Ubaidullah.
Har suka shiga sabon unguwarsu mai suna jahun, sai da Zaidu ya sauƙa tukunna Ubaidullah ya koma mazaunin driver yana shirin yiwa motar wuta, Zaidu ya ce.
“Ba za ka shigo ku gaisa da su Umma da Inna ba? iwarhaka na san baba ba ya gida.”
Ba tare da yabawa Zaidu amsa ba ya fito yayi gaba Zaidu yana binsa a baya da jakarsa da ya rataya ta a kafadarsa.
Tura kofar suka yi su na sallama Umma (mahaifiyar Zaidu) ta ce .”ah maraban ku oyoyo mazan fama”
Kakarsu Zaidu (ta wajen Uba)ta miƙe da sauri har tana tuntube zaninta ya kunce amma ba ta bi ta kansa ba tana cewa .
“Oyoyo, oyoyo mugun mai gida sannu da zuwa mugu oyoyo mugu,ta zo za ta rungumesa, sai kuma ta fasa,Zaidu ya ce.
“Ah Inna me ya faru kuma, kin fasa oyoyo din ne”?
“Mtsww oho maka kuma ban sani ba sau nawa zan fada maka idan zaka zo ka daina zuwa da wannan kayan naku ( kakin sojoji) haba idan mutum ya kallesu sai zuciyarsa ta tsinke ai wannnan mugunta ne da rashin imani,ga shi yanzu kasa ina jin zawo, ta fada ta juya tana kan mita ,ai gwanda ma kai kana dariya akan wannan abokin naka mai fuskar zaki ” ta shige daki.
Ubaidullah ya yi murmushi ya duƙa ya gaishe da Umma ta amsa cike da kulawa ƙannan Zaidu suka gaishesa tare da yi musu sannu da zuwa, Ubaidullah ya miƙe yana yiwa Umma sallama a kan cewa zai wuce gida.
Umma ta ce.
“Ah Ubaidu har za ka tafi gida ka tsaya kaci abinci mana “
” a’a Umma na gode na gaji ne ba na so na zauna ne kar na kasa tashi a kan lokaci ,dan wallahi bacci nake ji”
Umma ta ce.
Ai dole ku ji bacci kullum ana abu daya Allah dai ya kare mana ku”
Suka amsa da ameen
Ya juya zai fita, Zaidu ya bi bayansa ,ya ce” to kai kuma ina zaka je da ka wani rakoni a baya “?
Dariya Zaidu yayi
“Wallahi Ubaidu kai dai ba’a yi maka gwaninta wai fa zan dan taka maka ne”?
“No I don’t needed tnx,” ya fada yana wucewa gaba.
Zaidu ya ce.
“Ok ka gaishe min da mama kafin na shigo an jima”
“Ok za ta ji sai ka zo”
Zaidu ya juya ya koma cikin gida, daidai nan Inna ta fito tana yarfe zani tana riƙe ciki, Zaidu ya ce. “Subhanallah matar meya faru”!
“Uwarka ce ta faru mugu kawai idan kana so na kula ka , ka je ka cire wannan kayan naka sai ka zo mu yi gaisuwa, ” ta fada tana murguda baki Zaidu ya kwashe da dariya,Umma ta hararesa ta ce.
“Ka fa dawo kenan ko? za ka fara saka Inna ciwon baki? to wallahi ba zan lamunta ba ka shige bangarenka.”
Zaidu yana dariya ya ce. “To shikenan Inna kwantar da hankalin ki na tafi”
“Eh din na ji je ka mana, kar Allah ya sa ka dawo idan kaga dama, kafi ruwa tafiya”
~~~~~~~
Ta bangaren Ubaidullah ,parking din motarsa yayi a bakin madaidaicin gate din gidansu, black shadow din dake face dinsa ya cire,yana smiling.
Turo ƙaramin kofa na jikin gate ya yi gami da sallama, amma shuru bai ga kowa ba, abun har mamaki ya basa, ko ina mai gadin da ya a jiye oho.
Har ya kai kofar parlour kafin ya hau kwaɗa sallama, amma ya ji shuru ,har ya juya zai tafi part dinsa, sai ga Hafiza ta fito da hijabi, tana ganinsa ta saki dariya ta taho da gudu tana cewa.
“Oyoyoo Yaya, rungumeta yayi sannan ya saketa tana ta murmushi (Allah sarki dan uwa gudan jiki) ya ce.”ina Na’ila”?
“Wani faduwar gaba ne yazo ma Hafiza ta hau tsilli-tsilli da ido dan Na’ila dazu kawarta ta zo ta jata wai sun tafi walimar wata kawar, kawarta.
Ba ta kai ga ba shi amsa ba, sai ga mama ta fito,
da sauri Ubaidullah ya mai da hankalinsa gareta,cikin murna da farin ciki ya je ta rungumeta, mama ta ce.
“Oyoyo ɗana na kaina , barka da zuwa, bana kai kadai ka zo ne ,ina Zaidu”?
Murmushi yayi kafin ya ce.
“Zaidu na a jiyesa a gida amma ya ce na gaishe ki kafin an jima ya zo”