COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

@@@@
Sai dare su Ubaidullah suka sauka a airport din abuja, sojoji ne birjik aka zo tarbansu, da ɗima-ɗima motocin barrack, nan jama’a ake ta sarawa Ubaidullah masu mika masa hannu su na mika masu, Major Usman yana zuwa ya rungumesa Ubaidullah ya danyi kara kadan wanda Major Usman ne kawai ya ji, duk sun bi sun rame tamƙar basu ba tsantsar wahala da tashin hankali, nan aka shiga mota sai barrack, direct aka wuce da Ubaidullah part dinsa dan ya huta tun da baya da lafiya, bayan su Zaidu sun taimaka masa ya yi wanka ya fito yana dingisawa dan harta kafarsa na hagu a kumbure yake dan wajan faɗa akwai wanda ya buga masa ƙotan bindiga, zama ya yi a gefen gado ji yake kamar ya rufe ido ya gan shi a gida amma ba hali, muryan Zaidu ya ji yana tsokanarsa da cewa.
“Alhamdulilah mun tsallake teku da baya, dan mu kam ba zamu ce rijiya ba, wannan yaƙi da tashin hankali, wlh ban sa ran zan dawo a raye ba, gaskiya Malam ka dawo da matarka ta karasa jinyarka dan Madam ce kawai zata iya yi maka wasu abubuwan, amma mu kam ba zamu iya ba” harara Ubaidullah ya gallawa Zaidu duk da na wasa ne dan rabon da Zaidu ya masa irin wannan wasa tun Na’ilah na raye, ga shi baya jin dadi balle ya biye masa su dan capta, dan haka maganinsa yasha ya kwanta.
@@@@
Da washe gari bayan kananun sojojin sun zo sun yiwa Ubaidullah ya jiki, da misalin karfe biyu Major Usman ya zo shi ma, da sauri su Zaidu da KB suka miƙe su na sara masa, murmushi Major Usman ya yi ya kalli Ubaidullah, shi ma sara masa ya yi da gefen hannu da kyar ma yake iya motsa hannayen nasa, takardu Major Usman ya mika musu dukkansu, suka karba suka buɗe KB ne ya fara ihu da ya karanta, ya miƙe tsaye yana tsalle kamar karamin yaro, Zaidu ma haka murna ne ya cika shi, ticket Major Usman ya sake miƙa musu, nan Zaidu ya bude ya ga jirgin yamma na yau, bai san lokacin da ya kama kafar Major yana godiya ba, kallon Ubaidullah Zaidu ya yi ya ce.
“My Man gida zamu tafi yau an bamu hutun wata daya da iyalanmu, muje su ganmu” murmushi ne ya bayyana a fuskar Ubaidullah ya kalli Major Usman ya ce.
“Sir, nasan wannan dukka kokarinka ne,mun gode sosai”
“Haba dai, ku daina godiya,ni ina amfani da abun da ya kamata ne, shiyasa kuna dawowa jiya na samu General Of The Army muka tattauna da shi, kuma kai Ubaidullah kana bukatar kulawa, kunyi matukar kokari, dan haka ku koma gida ku huta, Ubaidullah zaka fi samun kulawa, In sha Allah a wata daya jikinka yayi kyau, sai ku dawo da iyalanku dan kuzo ayi liyafan karramaku” sosai suka din ga zuba masa godiya ba shiri suka mike suka hau tattara kaya, Zaid ne ya taimaka ya hadawa Ubaidullah na shi nan suka yi sallama da barracks aka wuce dasu airport, mintinsu talatin jirginsu ya daga izuwa bauchi, shi kuwa KB dan Kaduna ne dan haka suka yiwa KB sallama su suka wuce abun su.
Basu sauka da wuri ba sai wajan bakwai, tun kafin jirginsu ya sauka sojoji suka zo daukarsu, dan haka su na sauka sojoji suka sara musu sannan Zaidu ya ce zai raka Ubaidullah gida, amma sam Ubaidullah ya ƙi yace kawai ya wuce gida shi ma ya tabbata su Umma sunyi kewarsa su na son ganinsa, kawai su tafi idan yaso ya zo gobe, da haka suka yi sallama aka bude musu mota suka shiga Zaidu ya dagawa Ubaidullah hannu, shi kuma ya ɗaga masa kai, nan driver yaja su sai gida.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Kwance take a parlour akan 2sitter duk ta rame ta yi duhu itama, idonta a lumshe kamar mai jin bacci ta rufu da hijabinta, kamshin turaren da take kwana dashi ta tashi dashi, shine ya mata sallama wanda ya yi sanadiyyar zaburanta ta mike zaune, nan ta gansa tsaye a bakin kofar parlour wanda shi ma wa ita ya zubawa ido yana kallonta, murje idanunta ta yi ta rufe ta bude still dai ta ga ba gizo bane a hankali ta miƙe jiri na dibarta ga kyarman da jikinta ya ɗau lokaci guda, hannunsa daya Ubaidullah ya miƙa mata alamun tazo, a hankali take taku yayinda idanunta hawaye yake ambaliya har tazo gabansa tasa hannu ta shafi gefen fuskarsa, nan ta tabbatar da eh lallai shi ne, ihu ta saka tana kiran sunan Mama da Hafiza, dan dama a parlourn Maman take kwance, bata san lokacin da ta rungumesa da gefen da baya da rauni ba tana kuka mai tsuma zuciya, shi ma Ubaidullah din hawaye ne suka hau wanke masa fuska, Hafiza wacce take wanka ta ji Abi’atu na kwala kira haka bata gama wankan ba ta fito ta daura zani, ta saka hijabi, parlour ta fito ta tsaya turus ganin Yayanta, shima kallonta ya yi ya mika mata hannu da gudu tazo ta rungumesa gefe daya tana kuka itama, ɗaga kai Ubaidullah ya yi ya ga Mama tsaye kofar dakinta tana ta faman kuka, sake su Hafiza da Abi’atu Ubaidullah ya yi yaje gaban Mama yana kallonta yana murmushi tare da hawaye, bakin Mama na b’ari cikin raunin murya ta ce.
“Yaya Babba?” da sauri Ubaidullah ya rungumi mahaifiyarsa yana hawaye.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
A lallaba bani da chaji ????
UMMU AHLAN TAKU CE????????
[8/19, 10:59 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
~UBAIDULLAHI~••~~•~•~•~
my wattpab@Fateemah0••••~~•
Special gift to my 5 ☆stars★
Samira bint Abdallah????
Fatima bintu Sagir????
Farhat Mrs M’J????
Princess (Nafeesat)????
احلام فاطمة????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan????????
________________________
page°°°°°106&110
Sun jima haka kafin daga bisani Mama ta dago tana shafa fuskar Ɗan nata, tana jin farin cikin sake ganinsa, Hafiza ce ta kira Anty Ummu ta sanar mata akan cewa Yaya Ubaidullah ya dawo, Anty Ummu ba shiri ta zari hijabi takalmi ma daban-daban ta saka ta fice, Hafiza ma ficewa tayi da gudu ta je ta kirawo su Ummi ta ce Yayanta ya dawo, kafin ka ce me maƙota an cika parlourn Mama ana yiwa Ubaidullah jaje da ya jiki tare da yi masa fatan alkhairi akan nasarar da suka samu, har Anty Ummu ta iso tana zuwa ita ma da kuka ta tari ƙanin nata, idan ka kalli fuskokinsu a yau kasan su na cikin farin ciki matuƙa, har wajan karfe goma gidan Mama ana hayaniya, har da yan mata, musamman suke zuwa ganin jarumi Ubaidullah ya yinda da yawa su na fatan su shiga zuciyarsa su samu matsuguni a gidansa, Ubaidullah gajiya ya yi da hayaniyar, nan ya miƙe yana musu sallama ya ce zaije ya yi sallah yasha magani ya kwanta, Mama ta ce.
“Abi’atu tashi ki taimaka masa, idan kuma ba za ki iya ba ki fada min” a kunyace Abi’atu ta miƙe ta kama Ubaidullah suka fice, itama Anty Ummu sallama ta yiwa su Mama akan cewa zata zo gobe da safe daga nan aka fara watsewa, har gidan ta yi tsit,
Ubaidullah kuwa su na shiga part dinsu bedroom dinsa kai tsaye suka wuce, bedroom din a gyare tsaf dashi, zaunar da shi tayi a bakin gado kanta a sunkuye dan haka kawai ta ji wani masifaffar kunyarsa take ji, a hankali ta yi magana ta ce.
“Ka fara watsa ruwa kafin kayi sallahn” ta juya zata shiga toilet ya riƙo ta da hannunsa mai lafiya din ya ce.
“Ina da magana” sake yin ƙasa da kanta ta yi.
“Hummm, to wannan dukar da kan da kike yi na miye ne?” shuru ta yi bata ba shi amsa ba illa wasa da yar yatsar hannunta da take yi, da ya ga bata da niyyar magana ne ya saketa, yana saketa ta shige toilet da sauri har tana tuntube, tana shiga ta lumshe idanunta tana murmushi, daga Allah sai ita tasan irin kalar murnan da take ciki wanda baki ba wai iya furtawa ba, ruwan ta haɗa masa ta fito ta zo gabansa tana kallonsa ta ji gabanta na faduwa, dan da alama jikinsa bai yi ƙwari ba danyen ciwo ne, yanzu ya zata yi, ko ta je ta kira Mama ne? Take tambayar zuciyarta, bata gama tunaninta ba ta ji yana cewa.
“Kin gama haɗa ruwan ne?” ta gya ɗa masa kai alaman eh, ya ce.
“To zo ki cire min kaya ki min wanka” zaro idanu waje ta yi tana kallonsa ta ce.
“Iyeeeee!?” ya ce.
“Eh! Nace ki zo ki ciremin kaya ki min wanka” turo baki ta yi tana dan kunkuni ya ce.
“Magana kike yi?”
“Eh magana nake yi, taya zan maka wanka?, kafin kazo wa ke maka wanka? ni gaskiya sai dai naje na kira Mama ta maka wanka, amma ni kam ba zan iya maka wanka ba, babba da kai”
“To ai ba hakkin Mama bane jinyata ko kula dani ba, hakkin ki ne, a matsayinki ta Matata” da sauri ta kallesa ya kashe mata ido daya tare da mika hannunsa ta cire masa riga.
“Ni fa da gaske nake yi bazan iya maka wanka ba”
“Ohh!! Abi’ah na fa faɗa maki banyi sallah ba gashi yanzu har sha ɗaya saura ki hanzarta” juyawa ta yi zata fice ta ji yana ce mata.
“Au dan bani da lafiya shine za ki gujeni ba za ki iya kula dani ba ko? Ashe duk kukan da kike min na dawo kinyi kewata ashe duk yaudara ce? Wai ni an turoni gida matata ta yi jinyata ta kula dani ashe ma ba zata iya min komai ba,da na sani ma da ban dawo ba, da na zauna a barrack masu so na su kula dani su yi jinyata har na warke” jiki a sanyaye ta juyo ta kallesa ta ga ya haɗe rai yana faman kokarin cire riga amma ya kasa sabida dayan hannunsa dake sagale a wuyarsa gabaki daya baya iya amfani da bangaren hannun, tausayinsa ne ya kamata ta dawo jiki a sanyaye ta sa hannu zata cire masa rigar ya tureta gami da cewa.
“I don’t needed just leave me alone, ki tafi abunki” sake kai hannu ta yi zata kama shi ya daga mata tsawa wanda ya yi sanadiyyar fashewa da kukan da ta yi ta kama kunnenta ta durƙusa a gabansa ta ce.
“I’m sorry, bazan sake ba, sorry plssss” still bai kalleta ba, ya ci gaba da kokarin cire rigarsa, ya daga hannun kenan yana so ya cire dayan hannunsa ya bugi ƙirjinsa da ɗan karfi ya furta “wasssshhhhhh Allah” da sauri ta tazo ta kama hannun nasa a wannan karon bai tureta ba, kuma bai mata magana ba, cikin dauriya ta cire masa rigan ya rage vest a jikinsa, jikinta na kyarma ta cire masa vest din, a hankalin ya miƙe tsaye ya dan dafa bango, kallon kafarsa ta yi taga kafar a kumbure ta dago ta kallesa taga har yanzu fuskar nan tasa tamau take Ubaidullah ko hawainiya ba zata gwada masa canza kala ba, ta faɗa a zuciyarta sannan ta shiga cikin waswasin cire masa wando, da kyar ta yi jahadi ta cire masa belt ta zare kafin ta hau balle masa aninin wando gabanta na dukan tara tara, haka ta gama ta ja masa wandon kasa, sannan ya ɗaga kafarsa, ya rage da ga shi sai boxers, kama shi ta yi suka yi hanyar toilet bayan sun shiga ta ja ta tsaya ki ƙam tamƙar gunki dan bata san me zata yi masa ba kuma, a dan fusace ya ce “ba ki san yadda ake yiwa mutane wanka bane? Idan ba ki sani ba pls fita min anan ki ban waje malama” kin fita ta yi illa ƙura masa ido da tayi tana kallon fuskarsa dan ta kasa kallon gangar jikinsa, hawaye ne ke zuba a idonta, tsaki Ubaidullah yaja da dan karfi kafin ya juya baya yasa hannunsa daya zai zare boxers dinsa, da sauri ta riko hannunsa ta ce “dan Allah karka cire zan maka wankan amma karka cire, ance haramun ne kallon tsiraici pls” a mugun mamakince Ubaidullah yake kallonta amma tama raina masa wayau, wallahi badadin baya da lafiya ba da taji maza yau din nan ba sai gobe ba, amma haka ya kyaleta, nan ta hau murza masa soso da sabulu tana wankesa cikin daraba, sun bata lokaci dan sai sha biyu suka fito daga wanka, zama ya yi kan stool dinsa ta goge mi shi jiki ta shafa masa mai,ta saka mi shi jallabiya sannan ya tada sallah, ganin yadda yake sallah duk sai tausayinsa ya kara kamata, bayan ya idar ne ta tambaye shi ko yana bukatar wani abu zata tafi, cikin daga murya ya ce.
“Ki tashi ki tafi mana, na hanaki ne ko na riƙeki ne?” jiki a sabule ta miƙe ta fita, Ubaidullah ya rintse ido gabansa na faduwa aransa ya ce.
“Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!! Ba dai Abi’atu bata sona bane? Da na shiga uku ji Ubaidu, da ace tana so na ba zata min wannan tarban ba, wata biyar fa bamu tare na dawo kuma da ciwo amma ba zata nuna min kulawa ba?” ya sake rintse ido “dole ne na fahimci kina so na ko baki so na” wayarsa ya jawo ya duba yaga su miss calls har da na Zaidu da KB dasu yan barracks, Mama ya kira yana tunanin ma ko sunyi bacci, ringing biyu Mama ta daga ta ce.
“Yaya Babba, ya dai kana bukatar wani abu ne?”
“A’a My Momma, bana bukatar komai, amma dan Allah turo min Hafiza” Mama ta amsa da to, ta kira Hafiza tace mata Yayanta na kiranta, ita kuma Abi’atu tana fita dakinta taje ta watsa ruwa tana tunanin rashin kyautawar da bata yi ba, dan haka bayan ta fito wanka ta shirya ta fita kitchen tana haɗa masa simple food bai dan ruwa ruwa wanda zai ji dadin ci, wanda ba zai damesa ba, tana girkin ne taci alwashin zata kula da shi zata cire kunya tayi jinyarsa tunda mijinta ne, jikinta ne ya yi sanyi tuno ce mata da ya yi, ta tashi ki tafi ai bai hanata ko ya riƙeta ba, a ranta ta ce “laifina ne, zan ba shi hakuri” baya ta gama ne ta haɗa masa coffee mai kauri da madara tasa a karamin trey ta yi hanyar dakinsa da sallama ta turo kofar ta ga Hafiza na ba shi magani, nan jikinta ya sake sanyi ta ajiye tray din hannunta akan karamin center table din dake dakin tana cewa.
“Hafiza ba kiyi bacci ba?”
“Eh wallahi Anty da har zan kwanta Mama tace Yaya na nemana” jinjina kai tayi ba tare da ta sake magana ba, Hafiza tana gama ba shi maganin tayi musu sai da safe ta fice abunta, ko kallonta bai yi ba ya fara shirin gyara kwanciyarsa ta ce.
“Ga shi fa nayi maka girki ne shap-shap” ya ce.
“Am ok, bana jin cin abinci” shuru ta yi kafin ta miƙe a hankali ta dauki tray din ta fice ta koma kitchen ta dau supboil ta zuba masa kadan sauran kuma ta juye a rabo ta sa a freezer dakin ta dawo ta haura gadon nasa ta kwanta, Ubaidullah da ya rufe ido kamar mai bacci ya ji shigowarta bai gama mamakin me ya dawo da ita ma ya ji ta hayo gado ta rungumesa cikin sanyin murya ta hau basa hakuri tare da alkawarin ba zata sake ba, da kyar ta shawo kansa ya kalleta ta dinga rokonsa ya ci abinci, kafin ya tashi yaci ta taimaka masa ya yi brush suka kwanta.