COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

@@@@

Da washe gari ma haka ta wuni a daki ko parlour ta kasa fitowa ta bangare uku kuwa shirin biki aka fara ba kama kafar yaro, Ubaidullah ya kira KB ya sanar da shi auren Zaidu dan haka ya yi kokari ya ga ya halacci auren, KB ya fadawa Ubaidullah ai idan bai zo auren Zaidu ba, bai cika amini ba, Abba shine ya zama wa su Ubaidullah Uba a komai, ana biki saura kwana biyar KB ya sauka a bauchin yakubu, tun ranar da aka sa bikin Hafiza bata sake ganin Zaidu ba, bata yarda sun hadu ba, shi ma bai nemeta ba, dan ba a natsuwar shi yake ba, bayan KB ya iso nan ya saka Mama dasu Umma a gaba shi ma wallahi ayi masa mata a bauchi, yanzu fa shi kadai ne kawai baya da mata, wallahi zasu saka shi a gaba ne, Inna ta ce.
“Zo nan dan Albarka” dan kuwa jinin KB ya zo daya da Inna, kasancewar KB akwai barkwanci “ina dai mata kake so ko?” KB ya ce.
“Eh Innata, gaskiya nima mata nake so”
“Ma sha Allahu! Nayi maka mata, amma sai kayi hakuri da ita, dan ba jin magana take yi ba” dariya KB ya yi ya ce.
“To Inna wacece?” sai da Inna ta murguda baki ta ce.
“Na baka Ifritu” Zaidu dake zaune kamar ba ya wajan ya ce.
“Inna ki daina batawa ƙanwata suna”
“Yoo to ni ina ruwana da iskancin banza da wofi, jama’a ba zaku dinga saka sunan mutane ba sai na aljanu,kai kam ma naga take takenka, tun da aka saka lokacin aurenka naga kana min wani jiji da kai, ita dai Hafizatun bata fini a komai ba, kuma duk arziki duk tsiya nicevta farko ehe” yawancin yan uwa da ake zaune a wajan dariya ake yi, Zaid ya mike a hankali yabar wajan Inna ta ce “Kabeeru, ina dai ka karbi zabina ko?”
“Ahh sosai ma Inna na karba hannun bibbiyu” da haka shi ma ya tashi.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Yau ta kama alhamis gobe ne kuma za a daura aure, yau ana ta shirin zuwa Family and friends, Amarya Hafiza tasha kyau dan kuwa Ummi ce ta dauko mai gyaran jiki ta gyarata a kwana goman nan, yau ma kuma Ummin ce ta dauko mai makeup ta fentawa Hafiza fuska tasa kayanta golden color, kawayenta su Afnan kuma sun saka maroon, sunyi kyau sosai su ma, Tun da aka fara hidimar bikin Hafiza Ubaidullah da Abi’atu basu samu zama ba, basu nan basu can, har aka gama shiryawa aka tafi, ana ta neman su Ubaidullah da Abi’atu ba a gansu ba, sai bayan da duk jama’a ana can wajan taro, har an dibi awa daya tukunna ka ji wani kiɗa na musamman na tashi, yayinda maroƙi ke wasa Ubaidullah da Abi’atu, jama’a an zuba ido ana jira aga wasu taurari ne haka ake koɗasu, kamar daga sama sai gasu sun shigo su na dauke ido cikin shiga ta alfarma, farar shadda ce bugaggiya fara sol da ita anyi mata aiki da bakin zare, Ubaidullah ya saka bakin hula da bakin takalmi baƙin agogo kirar gucci, Abi’atu kuma ta yafa bakin gyale bakin takalmi da jaka, sakarta dasu abun hannu da zobe duk bakake ta saka, wayyo jama’a zo ku ga maching iya maching, ihu aka sa ana basu hannu, basu zarce ko ina ba sai wajan ango da amarya, su na isa Zaidu ya mike tsaye suka rungumi juna da Ubaidullah, sannan Abi’atu ta rungume Hafiza wacce kanta ke kasa tun zuwansu wajan ta kasa hada ido da Zaidu kamar yadda shi ma bai kulata ba ko a mota, nan aka ci gaba da event, yayinda hankalin KB ya tashi ya ji shi ma aure kawai yake so, haka akayi taro lafiya aka watse lafiya, da washe gari bayan an sauko daga masallacin jummaa aka daura auren Zaidu da Hafiza in da a yau wasu daga cikin manyan sojoji sun halaccin daurin auren, bayan an daura ne aka wuce reception da yamma aka yi walima, da washe gari kuma aka yi Soldier Day inda jama’a aka yi shigan sojojin har da harba bindiga, taro fa tayi kyau sai dai fatan Allah ya bawa ango da amarya zaman lafiya, Allah ya mai da kowa gida lafiya, haka aka watse da washe gari kuma suka fara shirin komawa barracks dan yau saura kwana biyu su koma, kuma da matan su a can zasu zauna dasu, kamar Hafiza ita ma kam ta tafi kenan.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Da dare da sallama ya shigo bedroom dinta, tana tsaye a jikin madubi ta fito wanka daure da towel tana tsane ruwan jikinta da wani karamin towel din dake hannunta, tana ganinsa ta tsorata ta hau rurrufe wani bangare na jikinta,dariya ma ta ba shi, ya tsaya yana ƙyaƙyatawa, cikin tunzura ta ce.
“Me ya kawo ka bedroom dina har kake min dariya? Kuma ko excuse babu?” ta murguda masa baki, takowa gabanta ya fara yi yana cewa.
“Gani nayi na warke naji sauki, shiyasa nazo dan a ramawa kura aniyarta”
“Kamar ya?” ta tambayesa tana ja da baya yana sake matsota.
“Matsalata da yarinya rashin kunya ga uban tsoro kamar farar kura, idan za ki cire wannan tsoron gwanda ki cire dan soja kike aure”
“To sai aka gaya maka tsoronka nake ji ne?”
“Ahh dama ni ai bance kina tsorona ba” ya fizgota jikinsa da karfi, towel dinta ya tsince zai fadi ta riƙe towel din gam ,ihu ta kurma tana kankame jikinta ” to ke Madam miye amfanin ihun bayan ba tsorona kike ji ba? Kwantar da hankalinki jarumar mata” ya hau shinshina wuyarta tare da fara sauke mata zafafan kisa-kisai, tun tana mutsu-mutsu har ta hakura ta sake masa jiki, tsayuwar gagararsu tayi, suka zube bisa gado, zafafan sakonni Ubaidullah yake aika mata dasu masu wuyar fassara, tun tana dan biye masa tazo ta ji abun nasa ya fara zarce tunaninta, hankalinta bai gama tashi ba, sai lokacin da taji ya ja towel dinta ya yi jifa da shi, ya haye saman kanta tukunna ta shiga sambaɗa ihu da iyakacin karfinta tana ambatar sunan Mama dasu Ummi, Ubaidullah ya yi nisa dan kuwa yau a shirye yake da ya kashe arnan sama, ban da sambatu marasa kan gado babu abun da yake mata, wanda ita bata fahimtar me yake fadi, san da zai shigeta ta saki razananniyar kara ta shaƙo shi tana kai masa duka, naushi yaƙushi, cizo, amma Oga Captain ba shi da wannan labarin, sai da ya ji ya samu natsuwa kafin ya sauka a kanta ya koma gefe yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, wani farin ciki ne ya mamaye zuciyarsa wanda bai taba jin kamar shi ba, a hankali yasa hannu ya jawota ya ɗaurata a bisa faffaɗen kirjinsa yana shafa bayanta a hankalin alamun lallashi, kasa katabus Abi’atu tayi dan ji take yi gangar jikinta tamkar ba nata ba, bakinsa ya kai satin kunnenta ya fara mata magana cikin tsigar lallashi da dukar da kai tamkar ba shi ba.
“Am! Am! Am so sorry my everlasting, and i’m very happy today, Abi’ah kedin ta musammance a gareni, bansan me zan faɗa miki ba, kawai na gode, na gode, na gode, Allah ya miki albarka, farin cikin da kika sakani a yau, Allah ya dauwamar dake har gaban abada” ya sake rungumeta tsam a jikinsa, a hankali ya miƙe ya shiga toilet ya hada mata ruwan zafi ya zo ya dauketa cak ya shige da ita, sannan ya sakata a ruwan, ji tayi wani zafi ya sake ratsata da dasheshshen muryarta ta furta ” wassshhhh Allah na, Ummina ya kashe! Ya kasheni, wayyo ya kasheni” tana yarfe hannu, saura kiris ya rage dariya ya sub’ucewa Ubaidullah, amma ya yi saurin hadiyewa dan idonta ya kalla ya ga tana jin zafinsa sosai, tana mugun jin haushin abun da ya mata dan haka ya maida hankali wajan gasata, sosai ya gasata kuwa, daga karshe ya fita ya barta ta yi wankan tsarki, yaje ya gyara bedroom din ya canza bedsheet, sannan ya koma toilet din ya sameta zaune a bakin bath ta daura towel sai gyangyadi take yi, ga zazzabin da yake shirin rufeta, kallon tausayi ya bita dashi kamar zaiyi kuka ya zo ya dauketa ya mai da ita bedroom ya zaunar da ita ya dauki rigar da tayi niyyar sakawa Allah baiyi ba a lokacin, ya saka mata sannan ya gyara mata kwanciya shi ma ya kwanta ya rungumeta, sai da ya ji ta yi bacci kafin ya mike ya zo ya yi wanka yayi alwala ya yi sallah raka’a biyu ya hau rokon Allah ya basu zaman lafiya da matarsa Allah kuma ya kaɗe musu fitina, Allah kuma ya sa musu albarka a wannan raya sunnar da sukayi Allah ya azurta su da haihuwa, bayan ya gama adduoinsa ne ya tashi ya hau gadon ya kwanta ya jawota jikinsa ya sumbaceta kafin ya lumshe ido, nan bacci mai dadi ya kwashesa, da asuba shi ya fara tashi ya yi alwala ya tafi masallaci sai karfe shidda ya dawo, bayan ya dawo a hankali ya fara tashinta daga bacci, da kyar ta bude ido, murmushi ya mata ta galla masa harara, tashi ya yi ya sake haɗa mata ruwan zafi ya sake gasata kafin ta yi wanka ya daukota ta zo ta yi sallar asuban da ba tayi akan lokaci ba, bayan ta idar a wajan bacci ya dauketa, sai sha biyu ta farka ta ga abinci kala kala a dakin, dama bakar yunwa take ji, nan ta zo ta hau bubbudewa nan taci karo da wata gasheshshiyar kaza wanda taji yaji, gasu drinks kala kala, yawu ta hadiye ta sauko ta hau cin kazan nan ido rufe, tana ci har lumshe ido take yi, dan kazar tayi mata dadi, har ta kusan inciye ta ji muryarsa yana cewa.
“Kazar da dadi ko? Ta yi dadi sosai? Kuma kina jin dadinsa?” harara ta galla masa ta ci gaba da ci dan ya mata dadi, murmushi ya yi ya ce “gaskiya kam kazar nan da dadi, kuma dama haka nake so kiji dadinsa, dan nima naci dadi jiya da daddare, dan haka idan ma bai isheki ba a shirye nake na kara zuwa na siyo wasu ranki shi dade, dan kuwa kazar amarcinki kike ci” tofar da wanda yake bakinta tayi ta zo zata mike a masifance amma me kasawa ta yi ta zauna tana matsar kwalla.
” ahh yi hakuri, na tuba, yanzu dai zo kisha magani” ya fada yana zama kusa da ita, maganin ya bude ya bata, ba gardama ta karba dan tana bukata, sha ta yi sannan ta hau hauma alamun bacci, a hankali ta mike ta koma ta kwanta a gado ba jimawa bacci ya sake kwasheta, wunin ranar Abi’atu bata leka ko parlour ba, da an tambaya tana ina kuma Ubaidullah zai ce bata da lafiya, su Mama da Hafiza sun zo dubata tana bacci, dan Hafiza bata tare ba, bayan an gama hidimar biki a gida ta zauna tun da gobe zasu wuce Abuja in da zata zauna dindindin, shiyasa Umma tace a barta kawai tunda duka za a wuce kuma ita ba zata dawo bauchi ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button