COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ayya dan albarka Allah ya kawosa lafiya,ya amsa da amin kafin ya ce.
Mama ina Na’ila ?
Mama ta ce.
“Hafiza ina Na’ila dan dazu tare na bar ku”?
Cikin in-ina Hafiza ta ce.
“Dazu bayan kin shiga daki kawarta Munira ta zo ta jata wai sun tafi walimar wata kawar Munira”
Mama ta hau salati tana tafa hannuwa,” Oh Allah na me Na’ila take son zama ne ? shi ne ta kama hanya ta fice baza ta iya zuwa ta fadamin ba? ko dan ta san ba zan barta bane?”
Ita dai Hafiza ban da zare ido Babu abin da take yi,ga wani uban tsoron da ya lullubeta ganin yanda fuskar yayansu ya rikid’e ya canza kala jijiyar wuyarsa duk sun tashi da ka kalle sa ka ga bacin rai k’arara, jinjina kai yayi sannan ya hau wurgawa Hafiza harara ,ai nan Hafiza ta k’ara tsurewa.
Ta kanta ya fara
“A kan me kina kallo za ki bar Na’ila ta fita iye?
Hafiza tayi shuru sai zare ido take yi ta kasa bada amsa, sai ja da baya ta keyi yana binta, ganin yana shirin cafkota ne ya sa ta ɗiba a guje ta yi bayan Mama ta saki kuka.
Mama ta ce.
” a’a wallahi karka taba Hafiza in dai Na’ila ce ba jin magana take yi ba, dan da tana jin magana to wallahi ba za ta fita a gidan nan ba,tun da nice nan na hanata fita da kuma kai, to ba ta ji maganata da taka ba, har za ta ji maganar Hafiza?”
“Kuma na tabbata bata san za ka zo yau ba, da ba za ta fita ba.”
Ba tare da Ubaidullah ya yi magana ba ya juya ya fice ransa ɓace.
Har yayi wanka ya shirya ya kwanta, Hafiza ta kawo masa abinci amma ko kallon abincin bai yi ba har aka yi sallar magriba, Na’ila ba ta dawo ba hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba.
Ya je daki ya samu Hafiza tana karatun Alƙu’ani kasancewar sun kusan yin sauka, tana ganinsa ta dasa aya.
Tambayarta yayi, ya ce.
“A ina ne suka walimar”?
Jikin Hafiza na kyarma ta ce.
“Nima ban sani ba yaya.”
Ba tare da yayi doguwar magana ba ya juya ya fice.
Yana fitowa ya samu,Mama a parlour ta kasa zaune ta kasa tsaye.
Nan suka zauna jingum-jingum
Har akayi sallar isha’i, su Na’ila basu dawo ba.
Kafin wannan lokacin, Captain Ubaidullah ya fara tunanin kalar salihin dukar da zai yiwa ƙanwarsa.
Sai wajan karfe tara suka shigo gidan.
Ubaidullah,Mama,Hafiza duk suna zaune a parlour.
Na’ila da kawayenta su biyar suka shigo
Sun fara sallama kenan.
Assalamu alay…..!!
Sallamar ta tsaya a maƙogaron Na’ila sakamakon tozali da yayanta, yana mata kallon za ki ci Ubanki yau!!
==============
GASKIYA ZAN AJIYE TYPING DIN LITTAFIN NAN, ZUWA WANI LOKACIN DA NI KARAN KAINA BAN SANI BA,
GA MASU ƘORAFI AKAN ABUN DA NA FADI DUK INA SAURARONKU……..
COMMENTS
&
SHARE
BY MOMYN AHLAN
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)
ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????
Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)
( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????
dedicated to my brother
U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶••••~~
MARUBUCIYAR
HALITTA DAGA ALLAH NE
GUDU A JEJI
SHUHADA
NIDA ƘANNAN MIJINA
TYPING… WA’YA KASHE ZAHRA’U? #200(My No ga masu bukatar siya 08165550116)
my wattpab@Fateemah0
QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????
Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako????????
Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????
بسم الله الرحمن الرحيم
________________________
????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________
page°°°°9&10
A hankali Ubaidullah ya tashi yana ci gaba da yi mata kallon yau na lahira sai ya fiki jin dadi.
Ba iyakar Na’ila wacce ta yi laifi ba har ta Hafiza sai da hantar cikinta ya kaɗe ganin yanayin Yayan nasu.
Juyawa yayi ya kalli Hafiza murya a daƙile ya ce.
“Go and close the door”
Jikin Hafiza na kyarma ta wuce a sabule, ta je ta kulle kofar, har ta juya ya ce. “ciro keys din, ki kawo min”
Hafiza ta cire keys ta kawo masa, ta miƙa masa jikinta na rawa.
Na’ila da kawayenta Allah ne kadai ya san kalar tashin hankalin da suka shiga, Na’ila har ta fara zikiri a cikin zuciyarta dan ta san ba makawa sai taci ubanta yau, yanda ya sa aka kulle da kawayenta ta san su ma yau sun kawo kansu, dan yanda zai jibgeta, haka zai jibgesu.
A hankali ya kalli Mama wanda ta buga tagumi tana kallonsu dukkan’su, tana hararan Na’ila ,wacce ta kama hanya ta fice tun rana sai yanzu karfe taran dare ta dawo da sunan wai sunje walima.
Durƙusawa Ubaidu yayi a gaban mahaifiyarsa hannun da ta sa a kumatunta ya cire sannan ya ce.
“Mama pls ki shiga daki” ya fada ya kamo kafadarta ya miƙar da ita.
Har cikin daki ya kaita ya zaunar da ita a bakin gado, sannan ya juya ya fita ya kulleta da waje.
Yana fitowa parlour ya samu Hafiza har ta fara kuka ganin ya kai Mama daki ta san yau babu mai taimakon su Na’ila sai Allah.
Wani harara ya galla mata da wani irin kalar ido wanda ba ta taba gani ba, kafin a tsawance ya ce.
“Keee!!! Dan ubanki!! shiga daki idan kuma kina so na haɗa dake to bilmillah!”
Ai da gudu Hafiza da ta yi daki har tana tuntube kafin ya juya ga Na’ila wacce ta fara kuka wiwi tun ba a kai ga dukarta ba.
“Dan Allah Yaya ka yi hakuri na tuba ba zan sake ba wallahi ba zan kara ba Yaya ka yi hakuri kar ka dake ni”
Nan Na’ila ta hau magiya kamar ranta zai fita, ganin ya ciro belt ya sakata fara kiran sunan Mama da Hafiza.
Ya ce.
“Wato tun baki tafasa ba kina so ki ƙone ko? tun baki kai ko ina ba kina so ki ƙarawa Mama hawan jini a kan wanda take dashi? Na’ila tun baki kai ko ina ba kina so ki gwada kamar kin fi karfinmu ko?”
Yana maganar yana matso su , su na ja da baya.
Na’ila ta ce.
” a’a Yaya wallahi ba zan ƙara ba,am really sorry”
Shut up!!
Ya fada da karfi.
Kawayenta suka haɗa baki su na cewa . “dan Allah kayi hakuri mu dai a barmu mu je gida”
Su na gama fadin haka Ubaidullah ya rufesu da duka.
Shata musu belt din kawai yake yi, ta ko ina ya samu dan idonsa a rufe yake, ba’a son ransa yake dukan Na’ila ba, zai so Na’ila ta zama kamar yar’uwarta Hafiza amma ya ga alama sai ya mata dukar da zata yi jinya tukunna.
ya gwammace ya karyata idan ya so ya kaita asibiti ya yarda, ya kashe kudi akan wani abu ya sameta wannan rayuwar da bata da tabbas din.
Tun su Na’ila da kawayenta su na kuka su na ihu, har ya zamto basu iya katabus.
sosai Captain Ubaidullah ya musu rugu-rugu.
Sai da ya ga ba su motsi sosai tukunna ya dakata yana huci.
Mama tun tana kiran sunansa tana bugun kofa, domin jin yanda yaran mutane ke ihu su na cewa zasu mutu,da ta ji abun nasa ba na ƙarewa ba ne ,ta hakura ta koma ta zauna, ta zubawa sarautar Allah ido.
Bayan ya gama jibgarsu ya ga sun kasa ihu da kuka basu motsi tukuna,ya kwashe su ya saka su a mota, sai RIMI HOSPITAL.
Su na isa a ka basu taimako tare da yi musu,treatment saboda ya faffasa musu jiki da belt.
Gado a ka basu, sai karfe uku na dare Ubaidullah ya koma gida, bayan ya tabbatar an yi wa su Na’ila allurar bacci sunyi bacci.
Yana zuwa ya je ya bude Mama ya sameta zaune ta buga tagumi, har wannan lokacin ta kasa bacci, (ALLAH SARKI UWA).