COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri ya isa gareta, ya cire hannunta daga kumatun’ta, kafin ya ce.

“Ki yi hakuri idan na bata miki Mama, I don’t mean to hurt you pls, but Na’ila tana bukatar hakan, bcox duk abun da ya same ta, ya same mu ne, amma ba za ta gane haka ba, ba zata iya hango tsananin son da muke mata ba, Mama har nawa Na’ila take duka-duka shekarunta goma fa Mama, amma take neman fin karfin mu?”

Mama ta share hawaye ta ce.
“Haka ne yanzu su na ina”

Na kai su asibiti”

Mama ta dafe ƙirgi ta ce.
“Ubaidu asibiti dai, asibiti fa kace? har da ƴaƴan mutane ka daka fa? shi ne duk ka kai su asibiti?”

“To Mama ai hakan shi ne daidai, baki ga ba saboda rashin kula irin na iyayensu akwai wanda ya zo nemansu ne? ba su zo ba ,ni a tunani na hakkin iyaye ne idan ba su ga y’ay’an su ba ko min dare ya kamata su je nemansu, amma ba su zo ba.”

Shuru Mama tayi kafin ta ce.
“Ni fa wallahi bana son tashin hankali da ka bar yara sun tafi gidan iyayensu, bana son abun magana da ƙanwarka kaɗai ka hukunta.”

Wani murmushi ya saki kafin ya miƙe ganin har karfe hudu ta gauta ,ya ce.
“Mama ba ki jin dadi ,ba ishashshiyar lafiya gare ki ba, yanzu ki kwanta ki huta gobe sai mu koma asibitin mu dubo su”

Mama ta ce.
“Yaran mutane kuma fa?”

Ya ce.
“Mama sai magana kike yi a kan yaran mutane , na ga fa harda Na’ila”

Girgiza kai tayi ta ce.
“Je ka huta, yau ka zo amma ko hutawa baka yi ba, Allah dai ya sa ka ci abincin ma”

Dan sosa ƙeya yayi.
“Wallahi Mama banci ba, zan ci idan Allah ya kai mu anjima”, yana fadi ya sa kai ya fice a dakin,Mama ta bi bayansa da kallo kana ta ce.

“Allah ya daɗa shirya min ku”

      ~~~~~~~

ta ban garen Hafiza ma ba ta yi bacci ba, tana jin yadda y’ar uwarta ta dinga ihu tana kuka, ita ma haka ta dinga kukan a daki, ko da taji shuru tsoron fitowa take yi karya haɗa da ita.

     ~~~~~~~~~

Da washe gari.

Da safe misali karfe tara.

Ubaidullah ya dan koma bacci bayan yayi sallar asuba kafin zuwa sha biyu su je asibiti” ana tunanin kenan.

Cikin bacci yake jin kamar hayaniya na tashi, amma sai ya danganta hakan da mafarki, jin abun bana ƙarewa ba ne ya saka shi tashi ya dauki jallabiyyarsa ya saka ya fito, can wajan gate ya hango Mama da Hafiza tsaye gefe daya mai gadi da wasu samari su uku da yan mata biyu.

Cike da takun isa da izzan jarumtaka na ƙarfeffen soja ya ƙaraso mai gadi na ganinsa ya sara masa ya koma gefe.

Hafiza tana ganin Yayan nasu tayi saurin matsawa gefen Mama.

Cike da ɗaure fuska ya ce. “lafiya kuwa meke faruwa?”

Daya daga cikin samarin ne ya nuna Ubaidullah da yatsa yana cewa.

“Kai dalla malam, ma su waye zaka fito kana ciccin magani, idan kana gadara kai namiji ne ai muma ba ka ganmu da jan baki ko dan’kwali ba, ina ƙannan mu?su muka zo nema, kuma ance sun zo nan tare da ƙanwarka, yanzu kuma mun zo muna jin wata zance da bamu ganeta ba.”

Ran Ubaidullah ya baci sosai ya tsaya yana masa wani kallon raini,

Kafin ya kalli Hafiza ya ce.
“Wuce ki shiga ciki”

Da gudu ta juya tayi abin da ya umarceta kafin ya kamo kafadar Mama ya juya da niyyar ya shige da ita ciki ita ma, sai ya ji daya daga cikin samarin yana cewa.

“Kaiiiiiii! ina ga baka san su waye ake kira da yan’bakaro ba, babu unguwar da ta kai mu sara suka a cikin garin Bauchi, idan baka fito mana da ƙannan mu ba, to wallahi sai mun yi gunduwa-gunduwa da kai.”

Cak Ubaidullah ya ja ya tsaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur jikinsa ya ɗauki b’ari.

==============

MANAGER PLS

COMMENTS
&
SHARE

BY MOMYN AHLAN✍????????????‍♀
[8/19, 10:56 AM] Zarahh: COLONEL UBAIDULLAH
( the story about a young gentle man)

ᏚᎢᎾᎡY ᏔᎡᏆᎢᎢᎬN ᏴY✍????

Z͢A͢H͢R͢A͢ A͢B͢D͢U͢L͢ (ᴹᴼᴹᵞᴺ ᴬᴴᴸᴬᴺ)

( y̾a̾r̾ s̾a̾r̾a̾r̾i̾n̾ k̾a̾i̾n̾u̾w̾a̾)
???????? SAHIBAR KAINUWA????????

dedicated to my brother

U̶B̶A̶I̶D̶U̶L̶L̶A̶H̶I̶
•~~
MARUBUCIYAR

HALITTA DAGA ALLAH NE
GUDU A JEJI
SHUHADA
NIDA ƘANNAN MIJINA
TYPING… WA’YA KASHE ZAHRA’U? #200(My No ga masu bukatar siya 08165550116)

my wattpab@Fateemah0

QAUNAR KU DABAN YAKE
ANTY HAUWA MMN USWAD
&
ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA
ALLAH YA RAYA ZURIA MY ANTY’S????


Alhamdulillah ina qara godewa Allah a ko da yaushe salati da daukaka da tsira da aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi muhammad S,A,W da iyalan gidansa da sahabban sa da ma goya baya har izuwa ranar sakamako????????


Ya Allah kabani ikon gamawa lpy????????

بسم الله الرحمن الرحيم
________________________

????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION????????
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

________________________

page°°°°13&14

A hanya su na tafiya Mama sai mita take a ina Ubaidullah ya tsaya.

Zaidu ya ce.
“Mama maybe akwai abun da ya tsai dashi ne shiyasa a yiwa abokina uzuri”

Mama ta girgiza kai kawai, ta ce.
“Mu fara biyawa mu a jiye ƴaƴan mutane kafin mu wuce gida”

“To Mama” abun da Zaidu ya furta kenan.

Sai da suka a jiye yaran mutane a gidan iyayensu, Mama da kanta ta shiga tayi musu jawabi, wanda zasu fahimta sun fahimta, masu toshewar kwakwalwa kuma sun kasa fahimta, suka rufe Mama da ruwan bala’i, ganin yanda jikinsa ƴaƴansu ya kumbura da shatin belt, bisa alamu duka ba bana wasa ya musu ba.

Mama har sai da ta ji dadi da Ubaidullah bai zo ba,dan tasan wani abun kam sai dai a kunna ƙaramin yaƙi.

Zaidu ya ce.
“Mama wai mai ya faru ne kam haka na kasa fahimtar komai fa?”

Mama ta ce.
“Ai gata nan a gabanka sai tsilli-tsilli take yiwa mutane da ido, na rashin gaskiya, ai tukunna ma sai mun koma gida ki sake haduwa dashi”

Na’ila tayi rau-rau da ido alamun zata yi kuka.

Zaidu ya ce.
“No no my lovely kar kiyi kuka kinji ai gani nan ina nan bazan bari ya sake dukan ki ba.”

Da haka har suka koma gida.

Mama tana tambayar mai gadi akan cewa “Ubaidullah bai dawo gida ba?”

Ya ce.
“Eh Mama ai tun da ku ka fita shi ma yaja mota wanda ya sakani tsinkewar zuciya ya fice bai dawo ba.”

Girgiza kai Mama tayi sannan ta ce. “Allah ya kyauta”
Suka shige cikin gida, Zaidu ya ce.

“Mama ni zan koma part dinsa na zauna kafin ya dawo”

“To Zaidu ka huta kafin ya zo ma na gama muku girki, tun da yanzu kam sai dai abincin rana.”

    ~~~~~~~~~~

Ta bangaren Ubaidullah ko da ya je hospital din aka tabbatar masa da an sallamesu, sun tafi tun dazu.

Wayarsa ya dauka ya bugawa Zaidu, a lokacin Zaidu na zaune a 2sitter yana latsa systerm dinsa.

Daukar wayar yayi yasa kunne.

Ubaidullah ya ce.
“ya ne, kun koma gida ne”

“Ah no Captain Ubaidullah muna hospital muna jiranka.”

“Mtswwwww, Zaidu bana son raini fa”

Wani dariya Zaidu ya kwashe dashi wanda yasa Ubaidullah rumtse ido, kuma da gangan Zaidu yayi dan kawai ya sake ƙular dashi.

“Oh Allah, Yayana Ubaidu baka son raini, ni kuma kasan ai ina son raini, ka ga idan zaka dawo gida ka dawo, dan mu kam har mun manta da wai munje hospital yaran jama’a kuma mun kai su gida.”

Ubaidu bai sake magana ba illa tsakin da ya ja, ya katse wayar.

Zaidu ma dariya yake yi, ya a jiye wayarsa a gefensa ya ci gaba da aikin da yake yi a systerm dinsa.

Sallaman samarin yayi gami da cewa su tafi gida, ƙannan su an kai su gida,kafin shi ma ya shiga motarsa ya dauki hanyar gida.

  ~~~~~~~~~

Wajan Mama ya fara wuce wa,tana ganinsa ta hau mita.

“Tun dazu muka fita tare da kai Ubaidu,amma kai sai yanzu ake ganinka, ina ka tsaya ko kuma nace ina ka wuce?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54Next page

Leave a Reply

Back to top button