COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
COLONEL UBAIDULLAH COMPLETE HAUSA NOVEL

Mama ta buɗe baki ta kwalawa Hafiza kira.
Da sauri Hafiza ta fito ta ce. “Mama gani”
“Je ki kawo min ruwa mai sanyi”
Hafiza ta amsa da “to” sannan ta juya da sauri,ta dawo dauke da ruwa a glass cup ta miƙawa Mama.
Karba Mama tayi sai da ta gurb’a tukunna ta miƙawa Captain Ubaidullah, amma sam ya ƙi karba balle yasha, dan har izuwa yanzu jikinsa kyarma yake yi burinsa bai wuce ya ladabtar da y’an iskan samarin bakaro ba, masu ikirarin su yan sara suka ne.
Mama ganin fa tabbas Ubaidunta ransa ya baci ne ,ta sake kurban ruwan a bakinta, tukunna ta kamo kansa ta danna cup din ruwan bakinsa, da kyar ya iya karfin hali buɗe bakinsa, ya kurbi ruwan sannan ya sauke a jiyar zuciya mai karfin gaske, bakinsa yana fitar da tururi tare da hayaki.
Mamaki ne ya kama Mama sosai a zuciyarta ta ce.
“Tabdijam ni Salamatu gani ga ɗa, saboda bacin rai bakinsa harda hayaki? lallai kam da ake cewa soja marmari daga nesa.”
Da kyar Ubaidullah ya dawo hayyacinsa,ya ɗan sassaita natsuwarsa, ya miƙe tsaye ya ce.
“Mama ki shirya mu tafi hospital din”
Mama ta ce.
“Dama wani hospital ka kai su?”
“Rimi hospital, naga yafi kusa that’s why”
Mama ta ce.
“Ok to, ka shirya kayi sauri kaji?”
Ɗaga kai yayi, ya fice.
Mama ta bi bayansa da kallo, a fili ta ce. “Ubaidu Allah ya kawo zuciyarka sassauci dama tun da ya kake balle yanzu da ake ɗirka maka alluran sojoji ai sai ta Allah.
Mama ta ce.
“Hafiza ki shirya yanzu kafin ya gama, nima kaya kawai zan canza dan nayi wanka tun dazu,dan hankalina yana kan yaran mutane wallahi”
Hafiza ta ce.
“Mama nima fa nayi wanka tun tuni”
“To ki saka hijab dinki dan nasan ba jimawa zanyi ba zai fito” Mama ta fada tana shigewa dakinta.
Hafiza ma ɗaki ta shiga ta saka hijab dinta, ta dawo parlour ta zauna, bata jima da zama sosai ba, Mama ita ma ta fito.
Bayan zaman Mama kamar da minti biyar haka, sai ga Ubaidullah ya shigo parlour’n bakinsa dauke da sallama.
Amsawa Mama da Hafiza suka yi.
Mama ta ɗago ido tana kallon ɗan nata, sanye yake da wandon jeans and brown t-shart, mai ratsin tambarin sojoji a jiki, yayi matuƙar kyau amma fuskar nan jiya iyau.
A hankali ya buɗe bakinsa, cikin sanyin murya kamar ba shi ba ya ce. “Mama muje”
Tashi Mama tayi sai da ya ga tayi gaba tukunna ya bita a baya kafin Hafiza ita ma ta dauki basket din abinci ta bi bayansa ita ma.
Har yanzu samarin su na tsaye a gate, Ubaidullah yana musu kallo daya,ya saki dariyar mugunta wanda shi ka ɗai ya barwa kansa sanin manufar dariyarsa.
Ya buɗe mota zai shiga kenan sai ga Zaidu, wani farinciki ya sake mamaye Ubaidullah wanda shi kadai yasan hakan.
Mama tana ganin Zaidu ta faɗaɗa murmushin fuskarta, da sauri Zaidu ya ƙaraso ya duƙa a gaban Mama yana kwasar gaisuwa, cike da fara’a da sakin fuska tare da kulawa Mama ta amsa, gami da cewa.
“yasu Umma dasu Inna fatan kowa lafiya ko?”
Zaidu ya sosa ƙeya yana russuna kai ƙasa dan shi kunyar Mama yake ji.
“Kowa lafiya kalau yake,Umma ma ta ce na gaisheki sosai”
“Ayya Allah sarki ina amsawa”
Zaidu ya miƙe yana kallon abokin nasa, sannan ya juya yana kallon samarin da suke tsaye cike da neman tada zaune tsaye.
Zaidu ya buɗe baki zai yi magana Hafiza ta gaishesa ya amsa yana cewa.
“Lafiya kalau my dear sister Hafiza, where is my lovely sister Na’ila?.
kafin Hafiza ta basa amsa ya juya ga Ubaidullah ya miƙa masa hannu suka gaisa ya ce.
“My man wasu guys ne wa innan haka a bakin gate kuma ina zaku je?” ya tambaya yana kallon Mama da Ubaidullah tare da wa’innan samarin da yan matan.
Mama ta ce.
“Humm yanzu dai ba lokaci Zaidu muje asibiti.”
Zaidu ya waro ido waje ya riƙe baki yana cewa. “asibiti dai waye ba lafiya?”
Mama tace .
“Ƙanwarka Na’ila”
Zaidu, zai kuma yin wata maganar Ubaidullah ya buga tsaki gami da cewa.
“Oh my god dalla! malam ka wuce mu tafi kai ba ɗan jarida ba, but sai shegen uban questions din tsiya, idan muka je ai zaka ga abun da ya faru da idanunka.
Mama ta riƙe baki tana kallon Ubaidu.
Zaidu ya sa dariya ya ce.
“Wallahi Ubaidu zaka ji dashi”
Zaidu ya juya Ubaidu ya ce.
“Zaidu pls dauki Mama da Hafiza da wa’incan ladies din, ni kuma zan ɗauki guys din nan ne.”
Zaidu ya ce.
“Okay Mama and my sister let’s go.”
Har zasu shiga mota Ubaidullah ya kira Hafiza tadawo jikinta na b’ari dan wani bala’in tsoron Yayan nasu take yi yanzu, dan gabaki’ɗaya ya sake burkice musu.
Hannunta ya kamo ya mata raɗa a kunne, ɗaga kai kawai tayi sannan ta juya da gudu tayi cikin gida.
Duk akan idon Mama, tana so ta fahimci wani abu amma ta kasa, dan haka ta saka zuciyarta salama, ta danganta hakan da yayi mantuwa ne, ya aiketa.
Hafiza ko cikakkiyar minti biyu bata yi ba, ta fito ta miƙa masa abu ya karba ya shige mota, sai da Zaidu ya tada motar suka fita sannan Ubaidullah ya juyo da motarsa yana kallon gefe, ba tare da yayi magana ba.
Daya daga cikin samarin yayi tsaki sannan ya shige gaban mota, sauran biyun kuma suka shiga bayan mota.
Tun daga gate Captain Ubaidullah da yawani fizgi motar sai ka rantse da Allah duniyar taurari zasu.
Wanda hakan yayi sanadiyyar faɗuwar gaban wa’innan samari, Ubaidullah da gayya yayi hakan ,dan sai ya ci ubansu hankalinsa zai kwanta, dan bai dauki raini a barracks ba ma, balle kuma ba a barracks ba.
Cikin kaɗuwa na gaban ya kamo sitbelt zai ɗaura, saboda wani uban gudun da Ubaidullah yake sharan titi dashi yana tada ƙura.
Har ya sa hannu zai jone Ubaidullah ya janyo yar ƙaramar wuƙa a gefen takalminsa wanda ake musu ikirari da boost ya datse sitbelt din.
Sannan yayi wata smiling na gefen baki wanda zaka iya yi masa inkiya da mugutar soja.
A madadin Ubaidullah yayi Rimi Hospital, amma sai ya juya kan mota ya ɗauki hanyar filin unguwar rafin zurfi.
Da ɗan nisa a tsakani ,amma kasancewar gudun da yake bana wasa bane kamar giftawar ido da bismillah, sai gasu a filin rafin zurfi.
Sosai Ubaidullah ke juya mota, yana shatale’tale, dasu.
Ba ƙaramin jijjiga suka yi ba.
Kafin Ubaidu ya tsaida motar ya fito yana huci.
A hasale ya ce.
“Duk ku fito.”
A galabaisa suka fito su na sauke wahalalliyar numfashi tare da ajiyar zuciya da kyar.
Ruwa Ubaidu ya ɗauko ya basu, da sauri suka karba, ko wannen su sai da yasha 2bottle.
Sannan Ubaidullah ya ɗane bayan motarsa ya zauna yana kaɗa kafarsa ɗaya.
Murya a sheƙe ya ce.
“Ku maimaita abun da ku ka ce dazu, ina so na tabbatar da cewa eh tabbas maza ne a gaba na idan kuma ba haka ba to ina muku albishir da cewa dole ku shafawa bakin ku wannan lipstick din, wasa za a buga tsakanin haziƙi gawurtaccen soja, da haziƙan tantiran y’an sara suka.”
Ya fada yana jujjuyawa jan bakin da ya aike Hafiza ta ɗauko masa, a hannunsa ya wulla sama sannan ya cafke.
Tsoro ne ya gama mamaye zukatan maza uku, su har ga Allah basu yi tunanin soja ba ne.
Gashi yanzu sun taro wa kansu jafa’i.
Kallon-kallo suka hau yiwa juna options daya ne garesu shine su basa hakuri.
Ai kuwa nan suka shiga koro ruwan hakuri.
Ubaidullah ya ce.
“Haba maza ya ku ka yi saurin yin sanyi haka tun ba a kafta wasan ba?”
“Dan Allah yallabai kayi hakuri wallahi bamu san kai soja ba ne.”
Ubaidu ya numfasa kafin ya fara magana
“Haƙiƙa na ɗaki ƙannan ku wanda a halin yanzu su na gadon asibiti tare da ƙanwata wanda ina mutuwar sonsu da kaunarsu, amma ni bana sake da ƙanne na saboda sha’anin rayuwa, ace yara ko shekara sha biyar basu kai ba amma wai sun tafi walima tun rana har karfe taran dare!” ya fada a tsawance zuciyarsa na sake yi masa zafi.