DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
Kallon da Jamila tabi Sauban dashi cikin firgita yasa Hajjah ta d’ora a alamar tambya a kanta, hakan Anna wacce ta anyana a ranta tabbas mutuwar Bintu lokaci d’aya akwai wata sarka’nkiya a cikinta Amma insha Allah komai zai bayyana gaskiya zatayi halinta.”
Saitin muryar Hajjah ta kumaji tana fad’in ” Sauban ba zai mutu a yanzun ba sai ya hau kujerar mulkin mahaifinsa bayan yayi murabus, kalaman Hajjah kenan karo na biyu.”
Zaro Ido Jamila tayi cikin sarkewar murya tace “tuba nakeyi ranki ya dad’e nayi kuskure abinda akacemun kenan.”
Ta Kuma kallon Sauban tace “zo Nan yarona hak”ika nayi farin ciki da ganinka Cikin k’oshin lafiya Allah ya jik’an mahaifiyarka.”
Ko kallon inda take Sauban baiyiba domin ko can dama baya yarda da ita, basa Zama inuwa d’aya da ita,
Sabida duk suka had’a wuri d’aya daga ita sai shi sai tayi Masa mugunta
Musamman idan Abdullah ya d’aukoshi ya shigo dashi sashenta bazai fitaba sai ta fakaici idon Abdullah tayi Masa muguntar da zata sakashi kuka har ya daukeshi ya mayar dashi wurin mahaifiyarsa.”
Ganin ko kallon inda take Abdullah baiyiba, taji haushi ta mik’e tsaye tana fad’in Allah ya bamu hakurin rashin bintu.”
Bayi suka amsa da Amin gimbiya Allah ya biya ya k’are Mana lafiyarki.”
Muryar Hajjah taji tana fad’in Allah yasa da gaske akeyi komai zai fito fili asiri zai tonu za’ayi hukunci marar dad’in ji da sauraro idan gaskiya tayi halinta, daga Abdullah sai Sauban a fagen sarauta domin sune suka cancanta, ko bayan ran kowa a wurin nan.”
Murmushin da yafi kuka ciwo Jamila tayi Bata tankawa Hajjah ba illah ma tayi kamar bada ita takeba ta wuce ta fita.”
Tana shiga sashenta tashiga cire Alk’yabbar jikinta tayi jifa da ita tashiga Kiran jakadiya, cikin hanzari jakadiya ta zube gabanta,
Jamila ta dubi jakadiya tace “asirinmu Yana shirin tonuwa domin Hajjah ta sakarmun magagganu masu Kama da gugar zana,
Babban tashin hankalinmu d’aya ne Ashe Sauban bai mutuba.”
“Bai mutuba ranki ya dad’e to ya akayi hakan ta faru?”
“Abinda nakeso nasani kenan, lallai ansare macijine ba’ayar da kansa ba,
Dole ne mubi ta wata hanya wacce zamu salwantar da rayuwar yaron can,
Domin tin yanzun anfara yimun gorin sarauta cewa daga Abdullah sai.Sauban,
Dafe k’irji jakadiya tayi tace waye yace maki hakan,
Cikin d’aga murya Mai cike da tashin hankali da damuwa tace “waye ya Isa ya furtamun hakan bayan hajjah.”
Ta Kuma sakin wata irin dariya tace “ki kwantar da hankalinki Hajjah dake da Sauban duk a lokaci d’aya zan aikaku lahira domin kune damuwata a gidan Nan.”
“Kinyi tunani Mai kyau ya uwargijiyata Amma shawarata a Nan a d’an jira har mutuwar Bintu ta lafa sai a aiwatar da wnn aikin,
Wnn karon aikin bokanya ne domin Bintu kad’ai ta gagari bokanya, tinda ankawar da ita komai zai zo cikin sauki, ta Kuma sunkuyar da Kai tace ya uwargijiyata ki natsu ki dinga saita kanki kada a gane wani abin dangane dake,
Ina ganin ko Hajjah wani abin ta hango a idonki shiyasa tayi maki wnn kalamin.”
Shuru Jamila tayi tana nazari,
Ganin tayi shuru yasa jakadiya tashi tayi Mata sallama tafita.”
Bayan mutuwar Bintu Sauban ya koma hannun Hajjah da Anna Wanda suke bashi kulawa suke taka tsantsan dashi a duk inda zai tafi da Kuma duk abinda zai Sha ko Kuya ci.”
Bayan wata bakwai da mutuwar Bintu a lokacin Sauban Yana da shekara hud’u har ya Fara zuwa makaranta Wanda Yardajen direban sarki Yake kaishi ya Kuma tsaya har a tashi ya d’aukoshi ya dawo dashi gida cike da kulawa, Wanda Sauban yarone Mai kaifin basira malamansa suke tsananin sonshi da Alfahari dashi a makarantar.”
Babban burin Jamila a Koda yaushe tayaya zata salwantar da rayuwar Sauban takeyi,
Bokanya ta Bata maganin da zata zuba Masa a abinci da zarar yaci to sai dai wani ba shi ba,
Abinda yafi d’aga Mata hankali shine,
Taga Sauban a idonta wuya Yake Mata sai dai daga nesa baya zuwa wurinta Sam, snn ga wasu bayi da kuyangi manya manya majiya k’arfi da aka zuba a b’angaren Hajjah Wad’anda duk Wanda yazo shiga basa barinsa, Daga ciki Kuwa har da ita, duk da dai Bata tab’a yunkurin zuwa wurinba labari ne yazo mata a kunnenta cewa har ita idan taje bazasu barta tashigaba wnn umurnin Hajjah ne”
Ana hakan wani dare ta tashi da amai da zawo sai shekashi takeyi ba sauki,
Hankalin Abdullah ya tashi yashiga kula da ita Yana tausayinta domin duk a tinaninsa itama mutuwa zatayi ta barsa kamar yanda bintunsa ta mutu ta barshi.”
Cikin sauri ya d’auki wayarsa yakira family doctor dinsu,
Minti ashirin saiga doctor yazo d’auke da Kayan aiki, yashiga Bata kulawar gaggawa awon farko ya tabbatar masu da tana d’auke da ciki na tsawon wata hud’u Bata saniba.”
A zabure Jamila ta mik’e zaune tana zarar Ido tana fad’in “ciki likita nice keda ciki har na tsawon wata hud’u?”
“Kwarai Kuwa ranki ya dad’e cikine dake d’an wata hud’u,
“Alhamdulillah Tashiga furtawa tare da Abdullah Wanda sai murmushi yakeyi Yana dariya tare da yiwa likita babbar kyauta.”
Washe gari gidan ya d’auka Jamila ciki ne da ita d’an wata hud’u,
Masu murna sunayi wad’anda ko ajinsu sunfi masu murnar yawa, bayinta da kuyanginta basuji dad’in samun cikin nataba domin sunsan da zarar ta haihu wata sabuwar azabace zata kuma lunkuwa a kan wacce take basu a yanzun,
Domin sun san Akan abinda ta haifa komai zata iya aikata masu, don wani sabon mulkine zata shinfid’a tare da abinda ta haifa d’in.”
Labari yakai har cikin fada cewar Jamila tana d’auke da ciki,
Sarki yayi murna sosai sai da yabawa Dan Aiken kyauta Mai tsoka,
Hakan da labari ya Sami Hajjah mere Baki kawai tayi domin ita da haihuwar Jamila da rashinta duk d’aya ne a wurinta.”
Samun cikin Jamila shine ya janye Mata hankali wurin salwantar da rayuwar Sauban domin tana ganin da zarar ta haihu idan namiji ta haifa Dole ne ya gaji sarauta.”
Anan hakan cikinta ya girma ya shiga watannin haihuwarsa,
Wani dare ta tashi da nak’uda ta haifi d’anta namiji,
Sak ita komai nata da d’an iri d’aya ne.”
Murna a wurinta da danginta abin ba’a magana,
Ranar suna yaro yaci suna SADEEQ.”
Anyi bikin suna na kece raini,
Amma Sam ko k’adan bai Kama k’afar bikin sunan Sauban da akayiba,
Hakan akayi aka watse lafiya, taci gaba da renon d’anta Wanda ta d’auki burin duniya ta d’ora a kansa,
Bata Bari kowa ya d’aukar Mata yaro, hatta jakadiyarta Bata Bata Sadeeq a cewarta za’a iya Bawa jakadiya kud’i masu yawa Dan ta salwantar da SADEEQ Dan ta lura da jakadiya bak’in kwad’ayine da ita da Kuma son abin duniya,
duk a tunaninta abinda takeyi shi kowa keyi.” Hatta da sarki idan ya aiko a d’aukar Masa shi, Bata bayarwa sai dai tace acewa sarki bacci yakeyi idan ya tashi zata aiko dashi,
Har sarki ya daina aikowa a d’aukar Masa sadeeq
Wanda Hajjah ko da Wasa Bata tab’a aikowa a d’aukar Mata Shiba indai Abdullah ya d’aukoshi yashiga dashi wurinta zata amshesa tayi Masa Wasa har tabawa Sauban shima yayi Masa Wasa idan zai fita ya daukeshi ya fita dashi.”
Ana hakan Sadeeq Yana cika shekara biyu a duniya a lokacin Sauban Yana da shekara shidda, Jamila ta Kuma samun wani cikin ta Kuma haihuwar d’a namiji aka sanya Masa SAGEER, Kuma haihuwar d’a namiji da tayi ta dingajin kanta tafi kowa a gidan daga ciki kuwa har da hajjah jitakeyi tafita
Sai wani sabon salon iyayi ya tashi a gidan ganin d’iyanta biyu duk mazane gado nata ne.” Dan hakan. In har tana raye ba Wanda ya Isa yayi mulkin masarautar nan bayan Abdullah sai yaranta domin ko a lissafi Bata Sanya Sauban domin ta San wurin da ta ajiyeshi kallon matance take Masa.”