BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Suka nufi Sauban gadan gadan zasu doka Masa sanda,
saurin zuwa gabansa tayi ta kareshi tana fad’in kada kucutar dashi ba magana yakemun ba Nima a Nan na tarar dashi bansan koshi wayeba.”

Tsaye Sauban Yake Yana kallonsu cike da mamaki da Al’ajabi,
Kallonsa sukayi domin ganin ko waye, domin idonsu ya rufe basu tsaya kallon fuskar ko waye ba,
Ido biyu sukayi da yarima,
Cikin sauri suka zubar da sandunan hannunsu suka zube k’asa suna fad’in “ranka ya dad’e ayi hakuri tuba mukeyi bamusan kaibane.”

Murmushi yarima yasaki ya Sanya hannu a Aljihu ya Ciro kud’i ya basu yace “zaku iya tafiya.”

Cikin sauri hannuwansu yana rawa suka k’arb’i kud’in suna godiya suka wuce cike da murna da jin dadi domin yau sunsamu kud’in Shan sigari????

Ajiyar zuciya ta sauke had’ida goge hawayen fuskarta ta d’aga Kai ta kalli Sauban Wanda idonsa akanta Yana kallonta,
Ido biyu sukayi tayi saurin janye idonta daga kallonshi,
shi kuma idonsa kyar akanta Yana k’are Mata kallo.”

Waigawa yayi bayansa yaga wani k’aton dutsi cikin muryarsa Mai taushi yace mutafi can yanuna Mata inda Yake nufi.”

Bamusu tabi bayansa tafiya yakeyi cike da mulki da Isa,
Ita Kuma sai Kare Masa kallo takeyi ta bayansa, tana fad’i a ranta ” iya had’uwa D’an binni ya had’u gashi kyakkyawa zuciyarsa Mai tausayi.”

Saman dutsin ya zauna itama ta janyo wani k’aramun dutsin da ya nuna mata da hannu a alamar ta d’auko shi ta zauna,
taje ta d’auko yayi Mata alamar ta zauna,
A gefensa ta ajiye dutsin ta zauna tare da sunkuyar da kanta k’asa,

Shanun da tafito kiwo Yake kallo yanda suke faman cin ciyawa, suna kiwonsu gwanin ban sha’awa.”

Juyawa yayi ya kalleta har a lokacin tana sunkuye da Kai tana Wasa da Zara zaran Yan tsun hannunta,
Cikin taushin murya yakira sunanta yace “Safna tayi saurin d’ago Kai ta dubeshi domin jitayi sunan yayi matuk’ar Dadi a bakinsa.”

Yace “kin yarda Dani?”
Kin yarda bazan cutar da keba?”
Kinaso na taimakeki na fitar dake daga kuncin da yake damunki?”

Daga Kai tayi “Alamar eh.”

Yace “ke wacece?”

Waye mahaifinki?”

wnn Jarmai din waye shi a wurinki?”

Share hawayen da suka zubo Mata a fuska tayi tace
“kamar yanda nafad’a maka sunana Safna,
Ni ‘yar garin Nan ce, mahaifina sunansa Jabiru ana kiransa da JAURO,
tinda na tashi bansan dad’in rayuwaba, a kullum cikin kuka nake da k’unci tare da wahalar rayuwa Mai tsanani a wurin uwar rik’o na,
Wacce a farko na d’auka itace mahaifiyarta sai daga baya da BABA yake fad’amun cewar ba itace mahaifiyata ba,
Sabida yaga irin wahala da tsangwamar da nakesha a wurinta
Yasa wata Rana ya zaunar Dani a lokacin Bata Nan tafita wurin biki,
Yake fad’amun cewar nayi hakuri da duk abinda INNO zatayimun nasani cewar ba itace mahaifiyata ba, asalima Bata tab’a haihuwaba Dan hakan yasa Bata San zafi da darajar ‘ya’ya ba,
Yace “SAFNA Kiyi hakuri da kaddarar rayuwa da tasameni domin kuwa har ni Nan banine mahaifinki ba,
Na tsinceki ne a k’ofar gari a lokacin nadawo daga kasuwa misalin k’arfe 8 na dare a lokacin nayo Daren dawowa gida,
Anan Naga wani kwali a jiye bakin hanya jariri Yana ta faman kuka a cikinsa,
Lek’a kaina nayi a cikin kwalin naganki kwance kina sanye sanye da kayan sanyi da hula da Safar hannu da k’afa masu shegen kyau
An dunkuleki da towel Mai kyaun gaske kasancewar lokacin sanyi NE hannunki Yana sanye da zoben zinari Mai tsadar gaske,

Tausayina ya kamashi ya duka ya daukeni ya rungumeni a jikinsa yanufi wurin maigari Dani,
Anan yayiwa maigari bayanin a inda ya tsinceni.”

Sosai maigari ya girgiza da maganar,
Hakan safiya ta waye a ka shiga cigiyata ko Allah yasa za’a Gane iyayena a tunaninsu Koda barayine suka shiga wani gida suka satoni idan iyayena sukaji sanarwa zasuzo su karbeni.”
.shuru ba Wanda yazo yace yasan ko Mai Kama Dani,
Washe gari maigari ya yanke shawarar akaini birni a ajiyeni a gidan marayu.”

Baba ya nuna Yana sona zai rik’eni domin baitaba haihuwa ba, shekararsa 20 da matarsa,
Hakan maigari ya Amince yabawa baba ni,
Ya kaima matar sa INNO.”

INNO batayi farin cikin amsoni da baba yayi ba, Dan da farko cewa tayi bazata amsheni ba, sai da taga zata rasa igiyar aurenta snn ta amsheni.”

Tin Ina makaramata nasan wahalar rayuwa domin da zarar nayi Kashi ko fitsari Inno zata dinga dukana tana zubamun ruwan sanyi a jiki,
Tin baba Yana fad’a Yana magana har ya Kai ya daina yashiga Jin shakkunta Wanda da alamar takaishi an d’aure Masa baki a wurin boka.”

Hakan na girma duk wani aiki na gida nice keyinsa Dan Gane da girki d’ibar ruwa kiwo faskaran iccen da za’ayi sawwa dashi duk nice keyinsa,
lokaci take d’ibarmun da zarar lokaci yacika bandawoba zan Sha wahala a wurinta zata Sanya bulala ta dakeni daga k’arshe bazata bani abincin da zanciba a ranar da yunwa zan kwana”

Allah yayi Mai farin jinin jama’a
A yanda naji ana fad’a cewar ni kyakkyawa ce duk cikin k’auyen Nan ba Wanda ya kaini kyau, Dan hakan ake mantawa da rashin asalina saboda kyawona masoya suke turuwa a kaina.”

Duk Wanda yazo neman aurena INNO take korarsa musamman idan ta fahimci Dan gidan mutumci ne, Wanda tasan idan ya aure Ni zanje na huta.”

Duk abin Nan da akeyi baba bai San abinda akeyiba,
Shi a ganinsa rashin samun mijin aure da banyiba,
Wata k’ila Aljanu suka aure Ni, Dan kuwa duk sa’ata sunyi aure wasu har sun haihu, Ni har yanzun shuru ba miji gani kyakkyawa ajin farko.”

Mutum d’aya ne ya jure korar jummai da tsangwamarta ya nace akaina cewarsa tinda Yana Sona sai ya aureni babu Wanda ya Isa ya Hana,
Sunan shi AUDU.”

Audu D’an sarkin kiwo ne dake cikin k’auyen mu,
Sosai Yan matan garin suke ruguguwa a kansa domin yace Yana sonsu bai furta hakan ba sai a kaina.”

Bana son Audu sam a Raina domin ni duniyar ma gaba d’aya taficemun a Rai fatana Akoda yaushe Allah yayi mun mafita, ta Alheri ya bayyanarmun da iyayena domin naji dad’in da yasa suka jefar dani a lokacin da nake da buk’atarsu.” Hakan Nan nake kula Audu nasanyawa rayuwata zan aure shi Koda bana sonshi, kodan na huta da azabar Inno.”

Ana hakan D’an maigari JARMAI JAN WUYA shima yafito neman aure na,
Sosai Inno tayi farin cikin fitowar Jarmai domin tasan da zarar sun Kara da Audu wurin shad’i,
ba makawa zai cinye Audu, dele a d’aura mun Aure da Jarmai,
duk yarinyar da jarmai yace Yana so a garin Nan sai ya aureta Koda Bata sonshi Dan kuwa, za’ayi zab’en fidda gwani a filin shad’i kamar yanda Al’adarmu ta fulani take duk akayi shad’i Jarmai keda nasara,
duk mutunen garin sun San da hakan,
Yanzun shekara 7 kenan duk shad’in ‘akayi shine ke cinyewa, Kuma a Nan take za’a aura Masa yarinya, dare D’aya Yake farketa batare da yaji tausayintaba sai ya gama biyan buk’atar gareta har na tsawon sati daya snn yake sakota wasu yaran mutuwa sukeyi wasu Kuma sukan kamu da ciwon yoyon fitsari, wasu Kuma Allah ya taimakesu su gyaru,
yarinya bakwai Jarmai ya aura a cikin garin Nan duk hakan yake masu.”

Ta share hawayen fuskarta taci gaba da cewa, “yanzun saura wata biyu ayi shad’in mu, zasu Kara tsakaninsa da Audu duk Wanda yacinye shi zan aura, nasan jarmai ke da nasara domin duk mutanen gari sun shaida hakan.”

Tin daga ranar da aka saka ranar shad’inmu duk Wanda yagani, ya rabeni da sunan yana sona, ko yana mun magana indai namijine sai Jarmai yayi Masa bugun mutuwa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button