BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

K’auyen Lassa basa Wasa da Al’adunsu na fulani wad’anda suka tarar anayi suka gada tin daga iyaye da kakan ni hakan Kuma suna girmama Wanda Yake d’aukar Al’adunsu da muhimmanci .”


D’aya daga cikin kujeren dake jere a wurin Sauban yaje ya zauna ya d’ora k’afa d’aya Kan d’aya daga cikin kujerar Yana sauke murmushin farin ciki, domin idan bai Manta ba rabonsa da gidan gonar Nan ya shekara uku.”

Fadawansa tsaitsaye a kansa Suna gadinsa, inda safwan Yake can wurin Mai gadi Yana surutu saboda yasan koda yazo wurin Sauban ba wata Hira zasuyiba Kuma shi mutum ne Wanda bayason yaji anyi shuru da baki.”

Hannu ya d’agawa fadawa alamar kowa ya Kama gabansa suje su huta
Tare da nuna masu d’aya daga cikin d’aku Nan dake jere a wurin ya furta idan Kuna buk’atar wani abin kushiga ciki zaku samu dukan abin bukata ya nunawa jami’an tsaron d’aya d’akin yace kuma idan kunada buk’atar wani abin kushiga nan akwai komai ,
snn yace “duk Wanda Yake buk’atar yaci duk abinda yakeso yashiga cikin gidan gona babu shamaki ya tsinka dukan abinda Yake buk’ata kowa yayi abinda ransa yakeso.”

Yana gama fad’in hakan ya Sanya Kai yanufi d’akin da yafi ko wanne ado da kyau yayi shigewarsa.”

Suna ganin ya shiga suka shiga yimasa godiya cike da farin ciki snn ko wanne ya nufi cikin gidan gonar domin tsinkar ‘ya’yan itatuwa.”

Da shigarsa d’akin Kai tsaye wurin k’aton hoton mahaifiyarsa yanufa Wanda Yake lik’e a gaban bangon d’akin,
Wanda tayishi tin tana budurwa kafin tayi aure tana sanye da Alk’yabbarta ruwan Madara tana murmushi a fuskarta tamkar kakirata ta amsa.”
Hannunsa yasaka yashiga shafa hoton tare da runtse idonsa Yana tsananin kewar mahaifiyarsa, sai da ya d’auki kusan minti biyar a hakan snn ya bud’e idonsa ya nufi wurin d’aya hoton Wanda sukayi a tare a lokacin Yana Dan shekara uku tare da mahaifinsa, inda Yake zaune a kan k’afarta ta Sanya hannu biyu ta rungume sa a jikinta tana kallonsa cike da k’auna,
shi Kuma mahaifinsa yana kallonsu dukansu suna sakarwa juna murmushi cike da burgewa a hakan aka d’auki hoton.”

Rungume hoton yayi hawaye suka shiga zuba a idonsa yashiga fad’in “Allah ya jikanki umma Allah ya Kai haske a kabarinki.”

Hakan yabar wurin yanufi Kan lafiyayyen gadon dake d’akin ya kwanta rigingine yayi filo da hannuwansa ya dulmiya cikin duniyar tunani.”

Sautin hayaniya yaji a Bayan window wacce take kallon k’ofar baya da alama rikici akeyi domin yaji sautin muryar macce kamar tana magiya.”

Mik’ewa yayi yanufi jikin window domin ganin abinda Yake faruwa yad’an zuge labule ya rik’a k’arfen window da hannu biyu Yana hango abinda ke faruwa.”

Wata farar yarinya ya hango ‘yar kimanin shekara goma Sha biyar, tana sanye da kayan fulani a jikinta kanta ba d’ankwali sai Yar sarkar da suke sanyawa a tsakiyar Kai anyi mata kitso Wanda ya zubo gaban fuskarta zuwa gadon bayanta, hannunta dauke da fanteka alamar ruwa takeso ta d’iba maigadi ya hanata shine take Masa magiya Akan ya barta.
Sai fad’in yakeyi cikin hausarsa ta fulani marar dad’in Jin “Allah SAFNAH Bazan barki ki d’ebi ruwa a dai dai wnn lokacin da yarima D’an birni yake hutawa ba,
Wato so kikeyi ki janyo mun kura daga aiki na kenan,
Yanuna ta da sanda Yana fad’in “Safna kiyi tafiyar ki tin muna shaida juna”

Durk’ushe takai a gabansa tana magiya idonta Yana zubar da hawaye domin tasan yau idan Bata d’ebo ruwan Nan ba kashinta ya bushi.”
Tashiga fad’in sale ka taimakeni kabar Ni na d’ibi ruwan Nan.”

” Ya kuma har zuka Yana fad’in wlh Allah bazan barki ba, Safna kiyi tafiyar kawai.”

Sautin muryar yarima yaji a bayansa Yana “fad’in zoki d’iba,
Ya juya ya kalli sale yace “dama hakan kakeyiwa Al’umma idan suka zo dibar ruwa?”

Da sauri sale ya zube gabansa Yana fad’in “ranka ya dad’e kayi hakuri ba halina bane ba hakan nake masuba, yau ne kawai ko yau din Dan naga kazo kana hutawa ne gudun kada su dameka.”

Shuru yayi bai tankawa sale ba,
Idonsa Yana kan SAFNA wacce sai Jan ruwa takeyi a rijiya tanayi tana share hawayen fuskarta da alama tana cikin damuwa.”

Kyawon yarinyar da farinta yake kallo Domin Fara ce fes har Farinta ya fara sir kawa da yellow,
kyakkyawa ce ajin farko sai dai k’azantar jikinta abin kyamata ce, don kuwa kayan da ke sanye a jikinta na fulani fararene da alama Amma akan daud’a har sun koma ruwan k’asa.”

Yana tsaye a wurin ta kammala cika fantekar ruwanta ta d’auka ta d’ora a saman Kai ta juya cikin sauri zata fita,
Karaf sukayi Ido biyu da yarima Yana tsaye Yana kallonta, jikinta ya soma rawa domin duk a tunaninta yayi tafiyar sa,
Hankalinta Yana kan dibar ruwa burinta tayi ta cika tanufi gida domin gudun azabar da da isko,
A gabansa tazo dauke da fantekar ruwan a kanta ta durk’usa tana fad’in nagode D’an birni Allah yabaka abinda kake buk’ata.”

Kallonta Yake a can k’asan lab’b’ansa ya amsa da “Ameen.”

Wanda tuni Safna tanufi hanyar fita daga wurin cikin sauri domin ta Isa gida takai ruwan tin kafin lokacin da aka d’ibar Mata yacika.
Sai da yaga tab’acewa ganinsa snn ya juya ya kalli Sale yace tashi a gabana daga yanzun duk Wanda yazo dinar ruwa kabarshi, musamman macce,
Saboda macce darajar gareta ba’a wulak’anta macce.”

Kayi hakurin ranka ya dad’e bazan sakeba,

Bai Kuma saurarensa ba ya juya yayi tafiyar sa.”

Juyawarsa yaci karo da Safwan ya nufo shi Yana murmushi Yana fad’in “yarima me kakeyi anan naje nemanka baka d’ak’i.”

Bai tankawa safwan ba sai da yayi gaba Yana tafiya snn yace naxo zagaya.”

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 18

“Rok’onsa taci gaba dayi, tana Kuka tana fad’in “dan Allah kayi tafiyarka, nagode da taimakonka, mutane da yawa sunyi k’ok’ari wurin su taimakeni Amma daga k’arshe basu Kai labari ba,
Banason wani abin yasameka na rokeka kabar wurin nan tin kafin su kuma dawowa su tarar da Kai.”

Ganin duk ta firgice yasa hankalinsa ya k’ara tashin tausayinta ya yashigesa yaji Koda zai mutu bazai tab’a barinta cikin wannan Halin ba.”

Rik’eta yayi da hannu biyu,
Domin ganin a firgice take, yashiga girgizata domin tadawo hayyacinta,
cije lebonsa na k’asa yayi Yana kallon kyakkyawan fuskarta Mai cike da kwarjini,
Sannu a hankali yakira sunanta cikin taushin murya “SAFNA ki natsu Mana babu abinda zai sameni, ko sunzo wurin Nan ba abinda zasuyimun.”

Girgiza Kai tashigayi domin tasan Halin Jarmai Sarai ga duk Wanda yagani Ya rab’eta ko Yana magana da ita.”

Ta kwance hannunta daga rikon da ya Mata tana kallonsa tare da ja da baya tana girgiza Kai tana fad’in kayi tafiyarka ce nagode da taimakonka, kabar ni a yanda ka ganni.”

Kafin ya Bata amsa a can ta hango ta wagarsu JARMAI sun nufota, hakan Yake da zarar tafito kiwo ko dibar ruwa zai dinga zagayenta, yanaso ya Kama Wanda zaigani yana Mata magana,
mudun ya Kama Wanda tsotsayi ya hau kansa a ranar sai dai wuyarsa ta haifi wani domin sai ya mashi dukan mutuwa.”

Tana ganinsu ta Kuma firgicewa ta rud’e cikin tashin hankali,
tashiga tura Sauban Bayan wani iccen bedi tana fad’in “boye a nan gasu nan zuwa, idan suka tarar da Kai dukanka zasuyi.”

Tura Sauban takeyi alamar ya boye, sai gani tayi yayi tsaye ko motsi ba yayi,
Ganin hakan ta fashe da kuka domin tasan kwanan Sauban a yau ya K’are,
Suna k’arasowa wurinta suka hango shi a gabanta,
Ai Kuwa gaba d’ayansu suka daga sanduna suna fad’in wani Mai k’aranren kwana ne Yake magana dake.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button