BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

masarautar Adamawa masautace Mai Adalci wacce take tafiyar da mulki dai dai yanda Addini ya tsara tare da tsantsan Adalci,da sanin ya kamata.”

Sarki Abdullah Yana da mata hud’u Jamila itace matarsa ta farko wato Fulani wacce ‘yace a wurin wani hamshak’en Mai kud’i dake Nan cikin garin Adamawa, auren soyayya sukayi da Fulani, Wanda had’uwarsu ta kasance tin a makaranta a lokacin Yana mataki na k’arshe ita Kuma tana mataki na farko,
Lokacin da yazo da zancen aurenta sam
Mahaifinsa Abdulsalam bai so auren ba,
domin yafison d’ansa Abdullah ya auri ‘yar sarki,a Aurensa nafarko Amma Abdullah ya kafe akan cewa shi sam Jamila Yake so bayajin zai iya auren wata macce a duniya bayan Jamila.”
Hakan sarki Abdulsalam ya hakura ya shige Masa gaba a wurin neman auren nasa.”

Mahaifin Jamila yayi murna da farin ciki sosai najin cewa d’an sarki Abdulsalam zai auren ‘yarsa ko ba komai za’a dama dashi a gidan sarauta wanda ya dad’e yana kutsa kansa bai samu shigaba,
Snn yasan ‘yarsa zata huta itama a dama da ita.”

Anyi bikin aurensa da Jamila lafiya aka dauko Amarya daga gidan mahaifinta aka shigo da ita cikin gidan sarauta a b’angaren da sarki Abdulsalam ya ginawa Abdullah domin ya zauna tare da iyalinsa.”
Tin zuwan Jamila gidan ta kyallara idonta taga yanda ake tafiyar da mulki da sarauta a Nan take abin ya burgeta domin tun farko ita macce ce Mai son nuna Isa da gadara Akan abu, to bare gata cikin gidan sarauta,
Anan take ta farajin kanta tamkar itace a matsayin matar sarki,
Cikin k’ank’anin lokaci ta Fara shinfid’a sarauta da mulki a gidan tamkar itace sarauniya.”

Ganin hakan da Mahaifiyar Abdullah tayi wato Sarauniya hajara wacce ake Kira da Hajja macce Mai dantako da sanin ya kamata duk Wanda ke cikin gidan Yana matuk’ar sonta bayi da kuyangi musamman mijinta wato sarki Abdulsalam Yana matuk’ar sonta wann dalilin yasa bai tab’a tunanin yi Mata kishiyaba domin duk wani farin ciki na rayuwa tana bashi a zamansu,
Duk a cikin tarihin masarautar babu sarkin da yayi mulki Yana da Mata d’aya sai sarki Abdulsalam.”

Sarauniya Hajja macce ce marar son hayaniya ko Kuma damuwa, wnn dalilin yasa dataga take taken Jamila matar Abdullah Akan son mulki yasa ta Ta had’a bikin nad’a Jamila a matsayin gimbiya.”

Hakan kuwa akayi anyi bikin nad’in sarautar gimbiya Jamila, bayan kwana biyu
duk wasu daga cikin ragamar gidan Sarauniya Hajja ta sakarwa jamila tashiga juya komai a yanda takeso, bayi da kuyangi kuwa sai yanda tayi dasu a gidan, domin gani takeyi tamkar itake mulkin sarautar,
bak’in cikinta d’aya ne shine har yanzun Bata samu haihuwaba domin tasan da zarar Allah ya Bata haihuwa babu abinda zai Hana d’anta ya hau kujerar mulki.”

Ganin yanda take juya mutanen gidan da yanda take tafiyar da mulkin cikin gidan cike da Isa da gadara yasa Hajja tafara taka mata burki akan wasu abubuwa daga ciki
Wnn dalilin yasa ta d’auko tsanar duniya ta d’orata a kan Hajja, inda takeji Ina wuta ta jefa Hajjah a ciki, koda zata huta.”

Akwai wani lokacin tafito daga b’angaren Hajjah tashigo d’akinta a fusace sakamakon kiranta da Hajja tayi tana fad’a Mata adaina Banzartar da abinci hakan, abincin da Yake wata d’aya a gidan sarautar yanzun sati biyu yakeyi drink’s d’in da Yake sati biyu yanzun sati d’aya yakeyi ta tsawatar Mata tare da k’arb’e key d’in store d’in a hannunta gaba d’aya.”
Karb’e key d’in da Hajja tayi a hannunta ya Kuma sanyawa Jamila tsanarta sosai a ranta,
Anan take tashiga safa da Marwan a cikin d’akinta ta Hana kowa shigo Mata d’aki,
Sai tunanin abinda zata aikata domin kawar da Hajja a doron k’asa domin ganin ita kad’aice a gidan ta ke son hanata taci karanta babu babbaka a yanda take so a cikin gidan.”

Tana hakan Jadiyarta ta turo k’ofa tashigo cikin hanzari,
Ta xube gabanta tace “ranki ya dad’e naji wani labari marar dad’in ji da sauraro Yana yawo a cikin gidan Nan cewa wai sarauniya Hajjah ta karb’e key d’in store a hannnki.”

Kallon jakadiya jamila tayi ta furzar da iska Mai zafi snn tace “hakan ne Sarauniya ta karb’e key a hannuna,
ta nunamun ban isa akan komai na gidan Nan ba, ta nunawa jama’ar gidan ni ba abakin komai nake ba
Wlh tallahi jakadiya na tsani matar nan, na rantse da Allah Da ba itace Mahaifiyar mijina Abdullah ba da tuni an Manta da tarihinta a cikin masarautar Nan.”

Jakadiya tace “wnn hakan Yake Amma duk da hakan ba a hakan za’a bartaba domin idan kika zuba Ido ko Mai sai dai kiga ana gudanar dashi a gidan nan, ke Kuma kina gefe kina kallo a matsayinki na gimbiya matar d’an sarki Mai jiran gado.”

Kallon jadiya tayi tace “meye mafita?”
Dariya jadiya tasaki tace “mafita d’ayace akwai wata bokanya a can wani k’auye Wanda ake kira da k’auyen bokanya k’araba, ita wnn bokanyar babu abinda Bata iya aikatawa idan kaje Mata da buk’atarka anan take zata share maka hawayenka,
Shawarar da zan Baki ya uwargijiyata itace kikawo kud’i masu yawa natafi wurin bokanyar nan nasaka tayi maki aikin da Zaki mallake komai na gidan Nan , ya zamana komai ya dawo a hannunki sai yanda kikayi dashi”
Snn na Nemo mki maganin haihuwa da zarar kin haihu kin haifi d’a namiji,
Kinga daga Nan sai musan yanda zamuyi mu kawar da sarki Akan kujerarsa sai mijinki Abdullah ya hau karagar mulki, Kinga sarautar duka ta dawo hannunki sai yanda kikayi da kowa dake cikin gidan nan domin kin Zama matar sarki kuma sarauniya ga Kuma d’anki yarima Mai jiran gado a hannunki.”

Wata irin dariyar farin ciki jamila tasaki Domin har tafara hango mijinta a kan kujerar mulki ita Kuma tazama Sarauniya,
Tace “wnn shawara taki tayi jakadiya.
Dan hakan nake sonki duk a cikin ma’aikatan gidan Nan,

Tashiga bedroom dinta taciro kud’i masu yawa tafito ta mik’awa jakadiya tace tashi kitafi yanzun Nan kisani na mallaka komai a hannunki, idan kika zalinceni Zaki had’u da fushina domin kinsan ba kyau ne daniba, ban sassauci.”

Jiki na rawa jakadiya ta k’arb’i kud’in tana fad’in “Har Abada bazan tab’a zalintarkiba ya uwargijiyata ki daina ko kwanta a kaina, ta mik’e tsaye tace natafi sai nadawo.”

Hakan jadiya ta tafi k’auyen bokanya k’araba ta k’arb’o magani Wanda za’a sanyawa Hajjah a cikin abinci ko lemun Sha da zarar Tasha to duk abinda Jamila tace shi za’a aikata a gidan.”

Abinci suka shiryawa Hajja na musamman wanda yasha magani har ya gaji,
Hakan Jamila ta sanya bayi suka d’auko abincin tana gaba suna bayanta a biye suka nufi b’angaren Hajjah dashi,
Wanda suka sameta kishin gid’e tana cin Ayaba fuskarta cike da murmushi da Annuri kamar ko da yaushe,
Tana ganinsu murmushin fuskarta ya kuma k’aruwa ta tashi zaune tana murmushi takai dibanta a wurin kuyanginta tace “kutafi ku huta saina nemeku.”

Cike da ladabin munafurci Jamila ta Kai zaune a gefen Hajjah tana Kai gaisuwa gareta snn ta gabatar Mata da abincin da tadaho Mata.”

Murmushi Mai cike da murna da Jin dad’i Hajja tayi,
Tana kallon Jamila tana fad’in godiya nakeyi gimbiya Allah ya biyaki yabaku zuri’a Mai Albarka.”

“Ameen Jamila tace tare da janyo abincin ta Fara xubawa Hajjah a cikin plate tuwo ne miyar taushe Wanda tasan Hajja tana tsananin so.”

Murmushi kawai Hajjah take saukewa a fuskarta snn ta sanya hannu ta k’arb’i abincin tafaraci,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button