BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Sai da tacinye tuwon dake cikin plate d’in tas snn Jamila ta zuba Mata ruwa ta wanke hannunta Tana murmushin farin ciki,
Hajjah Kuwa sai Sanya Mata Albarka takeyi tare da yimasu Addu’ar samun zuri’a
Domin a kullum Addu’arta d’aya ce Allah yabawa Abdullah haihuwa Mai Albarka ita dai taga ‘yan jikokinta tun tana raye.”

Tin lokacin da Hajja taci abincin Nan Wasa Wasa yau ciwo gobe lafiya ya zamana komai na gidan sarautar ya Fara ja baya, anan take ta aika
aka Kira Mata Jamila ta dank’a Mata key d’in store tare da duk wata ragamar gidan Domin taci gaba da kula da komai saboda a yanzun ba wata isanshiyar lafiya ne da itaba.”
Murna a wurin Jamila a lokacin abin ba’a magana, ai Kuwa a ranar sai da tayiwa jadiya kyauta ta ban mamaki, tin daga lokacin ragamar komai ta cikin gidan sarautar ya koma A hannun Jamila, tamkar itace matar sarkin.”

Shekarar Abdullah biyar da Jamila ko b’atan wata Bata tab’a yiba,
Inda sarki yashiga damuwa sosai, shi Kuma Abdullah ko a jikinsa domin yasan Allah shike bada haihuwa ga Wanda yaso,
Kuma shike hanawa ga Wanda ya ga dama,
snn Allah baya tambayarka ya akayi baka haihuba, Amma idan ya baka haihuwa zai tambayeka yanda ka rik’e Amanar da ya baka,
Sai dai ita haihuwa tana d’aya daga cikin kaso biyar cikin goma najin dad’in duniya, musamman a gidan sarauta.”

Wasa Wasa sai da Jamila ta shekara bakwai ba haihuwa ba alamarta, hankalin sarki Abdulsalam mahaifin Abdullah ya Kuma tashi
yashiga nema Masa auren ‘yar sarkin zamfara wato bintu,
Abdullah bai san abinda akeyiba.”

Sai da suka kammala shirya komai na dangane da auren Abdullah da Bintu tare dashi da mahaifin bintu,
har ranar d’aurin aure sai da suka tsayar snn sarki Abdulsalam ya Kira Abdullah yake shaida Masa tare da bashi umurnin ya tafi garin zamfara domin ganin matar da zai aura su fahimci juna domin aure ne ba fashi sai an d’aura, Nan da wata biyu masu zuwa.”

Baiyiwa mahaifin nasa musuba ko jayayya domin Abdullah yaro ne Mai biyayya da kawaici musamman a wurin mahaifansa,
Yana komawa yashiga shiri washe gari yashiga jirgi yanufi zamfara,
A ransa Yake sak’awa tare da Bawa zuciyarsa hakurin duk yanda yaga yarinyar a hakan zai aureta tinda mahaifinsa hakan ya ke so, baya fatan ya watsa Masa k’asa a Ido.”

Saukarsa a masarautar zamfara yaga tarbo da kulawa na samman anan take akayi Masa masauki a cikin wani k’ayatattacen d’aki Mai adon gaske, aka cika Masa gabansa da kayan marmari,
Minti goma da zamansa a d’akin, Bintu tashigo cikin shigarta ta Alfarma sanye take da Alk’yabbarta ruwan Madara wacce tak’ara yiwa fuskarta kyau da kwarjini, bayinta suna biye da ita a bayanta tare da yimata kirari ‘yar sarki jikanyar sarki matar d’an sarki Wanda zai gaji sarauta , d’anki ma sarki hak’ik’a kinyi gadon sarauta gaba da baya Allah ya taimakeki ya k’ara mki lfy Fara Mai farar aniya.”

Hannu ta d’aga masu, tare da juyawa ta kallesu, cikin d’aure fuska tace “Ashe banyi maku gargad’i akan kudaina yimun kirariba?” Ashe bance ku daina k’ask’antar da kanku gareniba, Nasha fad’a maku cewa ni mutumci kamar ku, Dani daku duk d’ayane ba wani banbanci a tsakaninmu a wurin mahaliccinmu to kusani wnn shine gargad’i na k’arshe da zan mku a kan hakan, kutafi sai na shigo.”
Snn ta nemi wuri ta zauna tare da sunkuyar da Kai a gaban Abdullah tashiga gaidashi cike da girmamawa.”

Kallonta yakeyi Yana murmushi Yana Hamdala wurin ubangijinsa domin Bintu ta dace da rayuwarsa kyawawan halayanta sunyi matuk’ar burgeshi, uwa uba bintu kyakkyawa ce ajin farko domin tafi Jamila komai ta kereta ta ko Ina, yashiga godewa Mahaifinsa domin ya zab’a Masa abinda ya dad’e Yana nema a rayuwarsa.”
Ai kuwa cikin a waya uku da sukayi a tare suka fahimci junansu soyayya Mai k’arfe tashiga zukatansu kowa ya fahimci d’an uwansa tare da yiwa junansu fatan Alheri snn Abdullah yayi Mata kyauta Mai girman yayi Mata sallama ya dawo gida cike da farin ciki.”

Yana sauka Kai tsaye fada yanufa wurin maimartaba cike da farinciki gabansa ya Kai durk’ushe Yana zuba Masa godiya tare da fatan Alheri,
Murmushi sarki yayi irin nasu na manya snn ya dubeshi yace “Magaji da alama zab’ina yayi maka naji dad’i da ganin hakan sai kafara Shirin auren ku Nan da wata biyu, godiya Abdullah ya shiga yiwa sarki snn ya Masa sallah yatashi yafita cike da farin ciki.”

Rasa yanda zai fad’awa Jamila yayi, Wanda yaga yanzun kwata kwata Bata da lokacinsa Bata bashi kulawa kamar da, mulki kawai ta sanyawa gaba,
Dan hakan shima ya kyaleta ya zura mata Ido,
Wasa Wasa duk safiyar Allah ta waye Abdullah da Bintu sai sunyi waya tafi a k’irga a tsakaninsu wata irin shakuwa da soyayya ta Kuma shiga Wanda sukeji idan d’aya bai auri d’aya ba bazai iya rayuwa ba.”

Biki sai k’aratowa yakeyi Wanda ya rage saura sati d’aya d’aurin aure, duk masarauta ta d’auka yarima Abdullah aure zaiyi kowa sai murna yakeyi sunajin dad’i wata k’ila canji zai shigo a cikin gidan sarautar, duk abin Nan da akeyi gimbiya Jamila Bata da labarin komai harkokinta kawai takeyi,
Snn kowa tsoron tunkararta yakeyi ya fad’a Mata.
A nan take aka shiga gyaran d’aya b’angaren dake kallon sashin Jamila,
Inda Jamila tacika da mamakin ganin ana gyaran wurin to kyaran me akeyi a d’aya b’angare irin nata Wanda babu abinda ya banbantashi da b’angarenta
Bata kammala tunaniba jakadiya tashigo Mata a firgice ta zube gabanta tana fad’in ranki ya dad’e najiyo wani labari a majiyar da Bata k’arya cewa yarima Abdullah mijinki aure zaiyi Nan da sati d’aya za’a d’aura auren.”

Wata irin zabura tayi ta mik’e tsaye daga kujerarta ta mulki tana fad’in k’aryane wlh babu wata Wanda da Isa ta jadani a gidan Nan ta zauna lafiya.”

Kirawomun bokanya k’araba yanzun Nan a waya tayi mun bugun k’asa taganemun tabbas da gaske Yarima Abdullah auren zaiyi ko maganar mahassadane da ‘yan bak’in ciki.”

Cikin minti biyu jakadiya tashiga Kiran bokanya, ai Kuwa Kira biyu bokanya ta d’auki waya tana dariya Mai cike da Ban tsoro tace
“anayimun waya daga masarautar Abdulsalam Akan maganar d’an sarki yarima Abdullah tabbas yarima Abdullah aure zaiyi Nan da sati d’aya Kuma aurensa dole ne za’ayi shi ba fashi babu ja da baya domin tauraruwar yarinyar da zai aura tana da haske sosai, snn akwai wani haske a tare da yarinya bugu da k’ari zatakawo farin ciki a cikin gidan sarautar,
Saboda ‘yar sarki ce, ubanta tsaye Yake akanta,
idan kika matsa dole sai anfasa auren Zaki iya rasa rayuwarki koki haukace.”
Bokanya tana gama fad’in hakan ta yanke wayar.”

Wani irin gumine yashiga tsattsafowa Jamila a jiki tashin hankali Wanda ba’a Sanya Masa Rana,
Ba babban tashin hankalinta jin cewa zatazo da farin ciki a cikin masarauta meye wnn farin cikin?”

Jakadiya tayi karaf tace haihuwa ya uwar gijiyata,

Hannu ta d’aga ta wanke fuskar jakadiya da Mari tana “fad’in k’aryane wlh babu wata wacce ta Isa ta haihu da Yarima a gidan Nan bayan ni.”

Hmmmmm fitinar mulki kenan????????

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

DIDECTED TO Fateemah M Uthman

Page 6

Sunkuyar da Kai jakadiya tayi hannunta dafe da kuncinta tana fad’in “Allah ya huci zuciyarki ya uwargijiyata, abinda kike nufi bashine manufata ba,
Tare da mik’ewa tsaye ta d’an runsuna tace “ki huta lafiya gimbiya snn tafita.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button