BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Kallonsa takeyi cike da tausayi taga har ya d’an rame, tabbas Abdullah ya gad’u da shu’umar macce Azzaluma,
snn tasaki murmushi tana amsa gaisuwarsa ta dubeshi tace tashi mutafi inason magana da Kai, Bata Kuma bin takan jamila ba ta juya ta fita.”

Jiki a sanyaye yabi bayanta suka nufi b’angarenta.”

A gaban Hajjah yake zaune tana Masa fad’a bai tankaba illah ya sunkuyar da Kai k’asa,
” Abdullah meyake damunka ne?”
Ina kashiga kwana biyu mahaifinka yayi ta neman ka?”

Ka kuwa San halin da kajefa mahaifinka kwana biyun na Rashin ganinka bayan kasan baya iya yini d’aya batare da ya sanyaka ido ba,
kasancewar Kai kad’ai yake dashi,
Ina hankalinka da tunaninka suka tafi ne?”

Kana aikin me k’aidin macce da makircinta sukayi tasiri a kanka?”
Shin ko ka Manta cewa wata Rana Kai sarki ne Kai ne zaka gaji sarautar mahaifinka idan kace hakan zakayi wani kallo kake tinanin Al’umma zasu dinga yima ka?”

Meyasa kayi sakaci da Addu’o’e da mahaifinka Yake baka a ko wacce safiya domin kariya daga jikinka da lafiyarka?” nasan kwana biyun Nan ka daina gaba d’aya domin da kanayi da abinda ya Isa yayi tasiri akanka”

Dafe kansa yayi komai yashiga dawo Masa baya, yashiga karanto Addu’oe a cikin ransa tare da runtse idonsa.”

Shuru Hajjah tayi tana kallonsa cike da tausayin sa
Sai da taga ya Fara samun natsuwa snn ta dubeshi tanuna Masa d’akinsa dake cikin babban falonta Wanda tin kafin yayi aure wani lokacin anan Yake kwana , tace tashi kashiga ciki kayi wanka ka canza Kaya, sann kayi Arwala kayi nafila raka’a biyu tare da karatun Alk’ur’ani,.idan ka gama ka karanta Addu’ar da mahaifinka Ya baka snn kafito katafi fada Yana nemanka.”

Jiki ba kwari ya mik’e yanufi d’akin nasa domin ya ai watar da umurnin Mahaifiyar sa”

Ai Kuwa Yana kammala yin sallar had’eda karatun Qur’ani yaji duk wata natsuwa tashigesa anan take komai nasa ya dawo Wanda ya gushe Masa,
Karon farko matansa yashiga tunani ko lafiya sukeyi,
Meyasa meshi hakan Wanda kamar an mantar dashi komai, a kansa,
Bai gama samun natsuwa ba sai da yashiga karanta Addu’oen da mahaifinsa ya bashi na neman tsari daga sihiri,
Tare da warware sihiri a jikin mutum Koda anyi masa,

Sosai yasamu natsuwa BaYan ya kammala yinsu a Nan take ya dawo cikin hayyacinsa,
snn yafito Yana murmushi ya durk’usa gaban Hajjah yace “umma nagode hak”ika kin kubutar Dani daga duhu, insha Allah hakan bazata Kuma faruwa ba.”

Murmushi tasaki tace “sakacinka ne Abdullah, ka daina sakaci da Addu’a domin kasan kana zagaye da makiya da ma hassada tashi katafi fada Idan kafito katafi wurin matanka domin kaji buk’atarsu ka lallashesu ka Kuma kwantar masu da hankali domin Suma sunshiga damuwa Allah yayi maka Albarka ya tsareka da sharrin masu sharri.”

Ameen yace “had’ida sunkuyar da Kai ya tashi ya fita yanufi fada,
A fada ma hakan ta kasance nasiha sosai sarki yayita Masa, tare da bashi wani rubutu dake cikin gora ya shanye snn yak’ara Masa wasu Addu’oe
a Nan ya Kuma jinsa ya k’ara samun natsuwa snn yayi Masa sallama yafito,

Da kwarin gwaiwarsa had’ida natsuwa ya nufi sashen matansa wad’an kansu Yake a had’e suna zaune a wuri d’aya a cikin falonsa kasancewar anan suke Zama suna tattauna matsalarsu da yanda zasu b’ullowa Jamila.”

Jin sallamarsa yasa suka saki murmushi suka mik’e gaba d’ayansu suka tarbeshi tare da yimasa sannu da zuwa”

Rungumesu yayi ya sunbaci ko waccen su a goshi snn ya Rik’a hannunsu suka zauna a tare a wurin d’aya suka sakashi a tsakiya,
Karon farko hakuri ya Fara basu,
Tin kafin ya iyar suka tareshi cikin kissa suna lallashinsa tare da kwantar Masa da hankali.”
Snn daga k’arshe suka gabatar Masa da abincin tare da kayan ciye ciye.”

Murmushi yakeyi Yana godewa Allah Akan ni’imar da yamasa na iyaye na gari da Mata na gari,
BaYan yaci abincin ne ya janyo su zuwa jikinsa yashiga kwantar masu da hankali cikin hikima Yashiga basu hakuri.”

Kwana biyu komai Yana tafiya dai dai inda Abdullah baya Wasa da ibadarsa tare da Addu’o’e hakan yasa komai ya kwancewa Jamila sai kisan kud’i takeyi ba biyan buk’ata,

Anan ta yanke shawarar janyo kowa a jikinta cikin siyasance har ta cin ma biyan buk’atarta,
Babu abinda yafi d’aga Mata hankali irin yanda taga Abdullah yadawo kamar Abdullah sa na da Wanda tasani, baya shakkarta snn duk abinda zaiyi Mata Kai tsaye Yake Mata , batare da wani dibanya ba ko shakka
Snn ta lura da yanda Yake matuk’ar ji da matansa fiye da ita, domin idan Yana tare dasu baya buk’atar kowa ya rabesa, ba kamar ita da yake Allah Allah safiya ta waye yabar d’akinta snn ko a wurin kwanciya sai dai idan itace ta nemesa.”

Snn ga SAUBAN yaron shima komai nasa sai dad’a ci gaba yakeyi, a yanzun Yana aji d’aya a secondry school komai nasa sai dad’a ci gaba yakeyi,
Ita Kuma nata yaran suna Nan a yanda suke komai nasu sai dad’a yin baya yakeyi Wanda har taji haushin hakan ta ciresu a makarantar gaba d’aya tafi buk’atar a Kira malamai a gida a karantar Mata dasu tana kallo.”

Dan hakan kowa ya zira Mata Ido akan yaranta daga ciki kowa har da Abdullah Wanda take nuna Masa tamkar bashi ne mahaifinsu ba.”
To bare Hajjah wacce da yaran da rashinsu duk d’aya ne a wurinta,
Shi Kuma sarki Yana fada ba komai yake sani Yana faruwa a cikin gidaba saboda a kwai Sarauniya ita ke gudanar da harkokin gida.”

Sauban yarone Wanda Yake matuk’ar son zumunci da Yan uwansa, hakan yasa da zarar ya dawo daga makaranta Yake fita Hajjah Bata saniba Yake zuwa part din Jamila wurin Yan uwansa,
Hakan zaije ya zauna Sadeeq yazo wurinsa ya zauna sauban yayi ta koya Masa karatu,
Tin Jamila tana kyamatarsa har ya Kai ta farajansa a jiki domin cikar burinta.”

Wata Rana yazo wurin Yan uwansa bayan sun kammala karatu, Jamila ta zubamasa abinci tace gashi yarona zauna kaci yau kahuta da cin abincin hajjah,
Girgiza kai yayi yace “nagode mommy.”

Sai a lokacin Sadeeq ya Masa magana duk da ba wata magana yake masaba ko zuwa yayi Sageer kawai Yake kulashi,
Yace haba Yaya Sauba kaci abincin mana, na lura bakacin abincin mommy idan ta baka.”

Sauban yayi murmushi yace “ba hakan bane Sageer na koshi ne shiyasa Amma zanci ko kad’an ne.”
Ya k’arb’i abincin ya faraci cokali biyu yayi ya ajiye yace “Alhamdulillah had’ida mik’ewa tsaye yace “natafi Y’an’uwa na sai da safenku.”

Tafiya yakeyi ya farajin cikinsa Yana hautsinawa Yana daf dashiga b’angaren Hajjah ya yanke jiki ya fad’i, sai kunfa yake fita a bakinsa.”

Da gudu bayi suka nufi wurin Hajjah suka fad’a Mata cikin Azama tafito ta tarar da Sauban gaba d’aya ba rai a jikinsa, cikin sauri takira sarkin mota aka nufi asibity dashi “

Da Gaggawa likitoci suka amshesa suka shiga bashi taimako cikin gaggawa,
Sai da aka d’auki lokaci Mai tsayi snn aka samu nasarar ceto rayuwarsa,
Inda duk aune aunen da likitoci sukayi sun rasa gane abinda yaci, Kuma ga duk kan alamu bincike ya nuna akwai abinda yaci Wanda ya haifar Masa da wnn matsalar wacce da ba’ayi saurin kawo shi asibity ba da sai dai ya rasa rayuwarsa .”

Hankalin kowa ya tashi da Jin hakan inda Hajjah ta tabbatar da Sauban bayacin abincin kowa a gidan sai nata
Ko natan sai Wanda ta dafa da hannunta,
To a Ina yasami abinci yacin da yaci?”

Hakan sarki shima hankalinsa ya tashi matuk’a tare da Abdullah, Wanda sai bincike sukeyi a inda Sauban yaci abinci snn menene aka zuba Masa a cikin abincin.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button