BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Tabd’i jam Ashe tsugunne Bata k’are kenan tinda Abdullah ya auro wad’an Nan tsala tsalan Yan Mata tabbas tasan ko kallon banza a yanzun Bata ishesaba yo Mai zaiyi da ita Yana ganin wad’an Nan Yan Mata wad’anda bata inda Allah ya ragesu,

Ga wani sabon rainin wayo da suka zo Mata dashi cewar Wai Abdullah ne yace suzo su gaida ita, wato da baice suzoba bazasu zoba kenan, tabd’ijam lallai akwai aiki a gabana,
To ko Bintu da take jinin sarauta gaba da baya ta buga tabarni bareku bayin banza da aka ‘yanta,
Ko Bintu da takeji da mulki tayi mun biyayya tabini da dason a zauna lafiya hakan bai sa naraga mataba bareku fitsararri bayin banza.”
Ta d’aga murya tana kiran jakadiya! jakadiya!! jakadiya!!!”

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

DIDECTED TO Fateemah M Uthman

Page 10

Cikin sauri jakadiya taxo ta tsuguna a gabanta tana fad’in “gani uwar d’akina Allah y taimakeki ya k’ara maki lafiya.”

Jamila ta dubi jakadiya cikin b’acin Rai tace “kinada labarin abinda yake faruwa a cikin gidan Nan kuwa?”

Jakadiya ta Kuma rinsinawa tare da sunkuyar dakai tace “ranki ya dad’e uward’akina ban San komai ba, me Yake faruwa a cikin gidan nan?”

Jamila ta kalli jakadiya cikin jin haushi tace “
Ni wad’an Nan bayin banzan wad’anda aka ‘yanta zasu ciwa mutumci a gaban idona.” Ni zasu kalli tsabar idona su cemun Yarima Abdullah ne yaturosu wurina domin su gaida Ni,
wato suna nufin bayin kansu bane kenan tirsasu yayi, a matsayina na gimbiya,
Ta d’aga murya cike da b’acin Rai “k’arya ne wlh duk abinda suke tak’ama dashi nafisu jinsa” dubunsu sun buga sun barni baresu bayin banza da wufi.”
Jakadiya tashi kitafi wurin bokanya ki fad’a Mata duk abinda ya ke faruwa, kada a kuskura a barsu su haihu a gidan Nan snn kifad’a Mata tasakasu a b’angaren masu Zaman banza a wurin mijina,
Sauran bayani idan Kika tafi kibani ita a waya zan iyar Mata dashi.”

Jiki na rawa jakadiya tamik’e tare da k’arb’ar kud’i tafita tanufi k’auyen bokanya k’araba.”


Kwana biyu Kwanciyar hankali tare da natsuwa suka shiga Abdullah inda Yake samun kulawa daga wurin matansa Khadija da Aishat,
Wad’anda kwatakwata basa bin takan Jamila kula da mijinsu kawai sukeyi tare da hidimarsa, hakan itama Hajjah tayi farin cikin ganin yanda hankalin Abdullah ya kwanta sosai.”

Ana hakan suka shiga shirye Shiryen tafiya Bauchi wurin bikin sunan ‘yar da aka haifawa sarkin Bauchi.”
inda Jamila ta shirya tsaf tare da yaranta da Abdullah suka nufi Bauchi biki akabar Khadija da Aishat a gida,
Wad’anda duk a tunaninsu tare dasu za’ayi tafiyar, kamar yanda Abdullah ya fad’a masu akan su shirya dasu za’a tafi, abin mamaki sai dai yakirasu a waya yace suyi hkr ya tafi da Jamila.”
Kasancewar Jamila Abokiyar maijego ce sosai”

Basu nuna damuwarsu akan hakan ba illah sukayi Masa fatan Alheri tare da Addu’a’ar a dawo lafiya.”

A b’angaren Hajjah bataso akayi tafiyar Nan tare da Jamila ba, saboda sanin halinta da tayi komai zai iya faruwa kafin su dawo.”

A garin Bauchi anyi bikin sunan Saudat bikin suna nane na kece raini domin duk Wanda kagani Yana yawo a gidan bikin to jinin sarauta ne ko wanne Yanaji da mulki da Isa,,
Kasan cewar sarautar Bauchi sarauta ce wacce ake nuna tsantsar mulki da Isa tare a cikinta.”

sosai Jamila ta yaba da kyawon Saudat inda anan take ta furtawa Mahaifiyar Saudat cewa,

A gaskiya Saudat yarinyar ta shiga raina sosai domin kyakkyawa ce,
Inama Zaki Bawa d’anki Sadeeq ita, domin nayi Masa sha’awar aurenta idan suka girma,

Murmushi Mahaifiyar Saudat ta sauke ta kalli Jamila tayi Mata kallon bakida hankali,
Tace ” ai mijin Saudat ba’a K’ASAR Nan Yake ba, domin duk Wanda Saudat zata aura sai ya zamana yayi fice a duniya kowa ya sanshi a b’angaren kud’i da mulki to wnn shine mijin Saudat.”

Dariya Jamila kawai tasaki domin idan wani mulki takeji Mahaifiyar Saudat ta shafeta domin ita matar sarki ce ita Kuma matar d’an sarki ce,
Snn idan kyau take ji dashi Mahaifiyar Saudat ta shafeta,
Hakan idan boka take tak’ama dashi Mahaifiyar Saudat tsafi takeyi, tsakaninsu Kar Tasan Karne,
Dan hakan komai rashin mutumcin Jamila tana shafawa Mahaifiyar Saudat lafiya.”
Hakan dai suka kammala hidimar bikin suka dawo gida, inda tun a can ta dinga zubawa Abdullah surkullenta a cikin abinci da ruwan Sha Yana shanyewa batare da yasani ba.”

Tin kafin su dawo jakadiya ta karb’o sauran ragowar maganin a wurin bokanya tashiga ai watar dashi a cikin gidan sak’o da lungu har part din su Khadija da Aishat.”

Sun sauka lafiya Shigowar su cikin gidan sarautar a Nan take Abdullah komai nasa ya canza,
Baya son ganin kowa a duniya sai Jamila, a maimakon ya nufi d’akinsa domin ya huta Kai tsaye d’akin Jamila yanufa suka shiga a tare tana ganin hakan tasan aikinta ya faraci tashiga murmushi murna da farin ciki domin aikinta ya Fara tafiya a yanda takeso saura wad’an can bayin banzan tare da Sauban.”

Tin shigar Abdullah d’akin Jamila kwana biyu kenan bai fitoba, hakan yasa sarki yashiga nemansa idan ya aiko kiransa sai Jamila tace “bacci yakeyi idan ya tashi za’a fad’a Masa, hakan Hajjah itama kwana biyu ta daina ganin Abdullah tashiga tambayar ko lafiya?”,
Tana zaune labari ya risketa cewa ai Abdullah Yana Nan lafiyarsa k’alau Yana b’angaren Jamila kwanansa biyu bai fitoba ko lek’e, anan Yake Zaune Yana aiwatar da komai nasa”

Murmushi Hajjah tayi tace Akira Mata matan Abdullah Khadija da Aishat,
Bayan minti talatin suka shigo suka durk’usa a gabanta tare da gaida ita cike da biyayya da girmamawa.”
BaYan ta amsa gaisuwarsu ne take tambayarsu Ina mijinsu yashiga kwana biyu?”

Shuru sukayi domin basa da amsar da zasu Bata,
Hakan ya tabbatar wa da Hajjah labarin da aka fad’a Mata gaskiya ne kenan,
Murmushi tayi tace kutashi kutafi kuci gaba da hakuri tare da Addu’a komai zaizo cikin sauki.”

Cikin ladabi suka mik’e suka fita,
Hajjah na ganin fitarsu itama tamik’e tsaye tare da gyara Alk’yabbarta kuyanginta suka Mara Mata baya tanufi b’angaren Jamila, karo na biyu kenan da hajjah ta tab’a sanya k’afarta ta shiga b’angaren Jamila saboda Hajjah macce ce Mai k’awaici da Alkunya ga duk abinda ya shafi Abdullah.”

Kai tsaye part d’in Jamila tanufa tare da sallama d’auke a bakinta,
Jamila tana kishin gid’e a kan kilishinta kuyanginta duk suna zagaye da ita ko wacce tana Mata hidima.”

Mamaki Hajjah tacika dashi ganin yanda Jamila take shinfid’a mulki tamkar itace Sarauniya matar sarki,
Ko ita Bata abinda takeyi.”

Ganin Hajjah yasaka Jamila mik’ewa zaune tana fad’in “sannu da zuwa umma.”

Yawwa Hajjah tace cikin had’e fuska tare da nuna mulki da Isa,
Ta kalli Jamila tace “kirawomun Abdullah “

Jikin Jamila duk ya mutu saitaga Hajjah tayi mata wani irin kwarjini Wanda yasa takasa yimata musu ko jayayya illah ta mik’e tanufi d’akin da Abdullah yake cikinsa ,
A kwance ta tarar dashi Wanda aikin nasa kenan kwanciya yanaso yafita yarasa dalilin nasa na Rashin fitar
, Yana kewar mahaifansa da matansa Amma ya rasa dalilin da yasa baya da k’arfin gwarwar yunkurin fita,
Kallonsa tayi takashe Masa Ido d’aya cike da kissa tace “umma tana falo tanason ganinka tashi mutafi.”

Jikinsa na rawa ya mik’e tare da sanya talkaminsa yafito falon,
Kallon juna sukayi da Hajjah yayi saurin zubewa k’asa kamar yanda yasaba ya gaida ita Yana murmushi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button