BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Mutan gari sunajin tafiyar tasu suka firfito suna kuka domin ba k’aramar b’arna akayi masu ba,
Ank’ona masu rumbun abinci ankashe masu shanu wasu sun rasa rayukansu me sukayi masu?
Suwaye suka aikata masu hakan?”
Daren ranar gaba d’aya garin basuyi bacci ba, babban tashin hankalinsu gidajen da aka k’ona daga ciki har da gidansu Safna Wanda a yanzun ya zama fili,
Kuka suka fashe dashi domin sunada ya k’inin har mutanen dake cikin gidan an k’onasu sun mutu.”

Yanda sukaga dare hakan sukaga safiya,
Koda safiya ta waye duka garin ya cika da jama’a ana masu jaje tare da amsar gaisuwa,
Acan bayan gari aka hango inna tafe tana jan k’afa fuskarta duk tab’aci da jini ba hijabi bare d’an gwali akanta,
Ai kuwa da sauri aka nufota aka rik’ata aka zaunar da ita,
Ruwa aka bata tasha jama’ar gari suna fad’in Alhmdulillahi Allah ya kub’utar DA lnno ta tsira, cikin muryar kuka tace “dukanmu mun tsira harda malam da Safna domin kuwa su guduwa sukayi,
Ta kuma fashewa da Kuka tana fad’in Safna Annobace a garin nan ranka ya dad’e duk ita ta Janyo mana wnn bala’in.”

Maigari yace “subahanallahi Allah ya kyauta, ba Wanda ya janyo mana duk abinda yasamemu daga Allah ne bama d’orawa kowa laifi,
Alhmdulillah tinda sun tsiratar da rayuwarsu Allah ya tsaresu a duk inda suke Mun san zasu dawo garemu komai daren dad’ewa.”

Anan sukaci gaba da amsar gaisuwar wad’anda suka mutu tare da jajen shanun da aka kashe.”


Cikin wata bunka ta farka ta tsinci kanta a cikinta, gefenta akushine Wanda yake d’auke da waina da miya da manshanu,
Wata mata tagani ‘yar fillo irinta sanye da kayan fulani irin nata zaune a gefenta Tana kallonta tana murmushi,
a k’allah matar zatayi shekara 40.”

Murmushi safna tasakarwa matar tare da k’ara waigawa domin ganin inda take,
Matar tace “sannu Safna har kin farka.”

Zaro ido safna tayi tana mamakin a Ina take? Wacece wnn?” Ya akayi tasan sunanta?”
Anan take komai yadawo mata sabo cikin razana ta motsa tana neman ta firgita, tare da kallon hannunta tana fad’in macijin ya sareni ko?”

Murmushi matar tasaki tace “bai sarekiba ki kwantar da hankali,
Ta mik’a mata Akushin dake d’auke da waina tace ‘ga abinci kici.”

K’amshin abincin ya daki hancin safna a nan take cikinta ya k’ulle akan yunwa ta tina da rabon ta da abinci har ta manta, ta karbi abincin ta Faraci, citakeyi tana lumshe ido domin ba kad’an takejin dadin abincin ba,
Sai da ta cinye wainar gaba d’aya snn tasha ruwan pure water dake ajiye a gabanta,

Murmushin matar takeyi tana kallon safna cike da tausayi,
Itama safna kallon matar takeyi, tana tinanin a ina tasan wnn fuskar tabbas ko a inane tab’a ganin wnn matar kuma tasanta sosai.”
A mafarki wata zuciyar ta fad’a Mata,
Tabbas a mafarki kika santa anan kike ganinta, da zarar kinshiga damuwa ita ke zuwa tana lallashinki tare da kwantar maki da hankali.”

D’aga kai tayi ta kuma kallon matar wacce take sakar mata murmushi tace “Safna kin tinani?” Kin tina inda Kika sanni?”

hawaye suka soma gangarowa safna ta taso tazo gabanta ta durkusa tace “Inna bazan tab’a mantakiba domin kina taimakona a duk lokacin da nafad’a cikin k’unci da damuwa,
Ke wacece?”

Murmushi matar tayi ta dafa kan Safna tace “zakisan KO ni wacece idan lokacin sanin yayi, kafin nan kitashi kitafi domin akwai sauran k’alubale a rayuwarki,
Ta nuna Mata wata hanya tace “kibi nan kiyitafiyarki domin tsiratar da rayuwarki,
Snn kiya wai ta Addu’a a a duk halin da kika tsinci kanki a cikinsa sai wata Rana.”

Share hawayen fuskarta safna tayi, tayi matar godiya,
Matar ta bata silifas tasaka Wanda tanemi zugin zafin da takeji a k’afarta ta rasa,
Snn ta nufi hanyar da aka nuna Mata tafara tafiya.”

Tafiya takeyi sosai tanayi tana hutawa saboda gajiya har yamma ta Mata a kan hanya,
Hakan take tafiya cikin daji, batare da wani tsoro ko fargaba a tare da itaba,
Kwatsam ta ganta a tsakiyar hanya akan wani babban titi wanda motoci suke wucewa da k’arfi ba batare da sun tsayaba,
Wani Mai sayar da abinci ta hanga a can tsallaken titi taji cikinta yayi kuka alamar yunwa takeji ga kuma kishirwa,
Hawaye ta share a idonta tana “fad’in Allah Sarki Baba Allah ya jik’anka ya gafarta maka.

Ta mik’e tsaye tanufi wurin Mai sayar da abincin,
Tanaso ta k’etara titi tsoro takeji saboda yanda taga motoci suna wucewa da gudu, sai tazo ketarawa sai kuma ta dawo baya tana sharar hawaye,

A can tajiyo jiniya tajuya ta hango motocine tafe wad’an da basa da iyaka, cikin zafin nama ta nufi kan titin da gudu tana fad’in kafin ku k’araso na k’etara,
Ai kuwa sai dai taji a d’auketa da mota ta fad’i a tsakiyar titi jini yana fita a hancinta da bakinta.”

Da sauri motocin suka taka burki suka tsaya,

Wata kyakkyawar macce wacce hutu ya zauna a jikinta ‘yar birni ‘yar gayu tana sanye da glass a fuskarta sai k’amshi take zubawa wacce shekarunta bazasu wuce 37 ba, tabud’e mota tafito ranta a b’ace take kallon direbanta tana “fad’in yahuza baka ganine ko idonka a makance yake kadiba kagani aikin da akayi d’an Adam ba dabba bane.”

A nan take Tabawa escort d’inta masu take mata,baya umurni tace “ku dauketa kusakata a mota mutafi asibity da ita.”

Cikin sauri aka tallabi safna aka sakata a mota suka d’auki hanyar babbar asibity dake zaman kanta a cikin garin Adamawa.”

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 29

* A lokacin da aka nufi asibity da Safna ba rai bare numfashi a tare da ita,
Kai tsaye Emergency aka nufa da ita cikin gaggawa likitoci suka k’arb’eta suka duk’ufa a kanta domin ceto rayuwarta da tsayar da jinin dake fita a hanci da bakinta.”

Sosai hajiya LAILA ta girgiza da ganin yanayin da yarinyar tashiga, danko fuskarta bata tsaya ganiba hankalinta a tashe yake matuk’a.”

Hajiya laila mace ce mai mai tausayi mai son ‘ya’ya,
haihuwarta d’aya a duniya ‘yarta d’aya macce mai suna SUHAILAT wacce ta b’ata tin lokacin da ta haifeta bikin sunanta kawai akayi washe gari aka wayi gari babu ta ba alamarta tab’ata.”

B’acewar da har yanzun ba labarinta bare a san dalilin b’atan nata,
wacce a kullum hajiya laila take kukan rashin ‘yarta kwaya d’aya tilo wacce take tunanin itace kwanta a duniya, tun daga gareta KO b’atan wata bata kumayi ba, amma sai dai tanaji a jikinta Suhailat d’inta bata mutuba, tana raye domin tana yawan mafarkin ‘yarta ta girma tana cikin mawuyacin hali.”
A kullum Addu’a takeyi Allah ya bayyanar mata da tilon yarta cikin k’oshin lafiya”
Cire glass din idonta tayi ta share hawayen dake zuba a idonta,
snn ta mayar da glass din a fuskarta,
takoma cikin mota ta zauna tare da jinginawa akan kujera,
Wayarta ta d’auka kira mijinta Alhaji HABIB SANI NAIRA,

RINGING d’aya zuwa biyu Alhaji Habib ya d’auka, a lokacin yana office suna mitting tare da yaransa akan cigaban da aka samu a kanfaninsa,
Yana ganin kiran nata Saida yasaki murmushi ya kalli wayar,
Snn ya tsayar da maganar da yakeyi,
Snn Ya d’auki wayar , Cikin so da k’aunar matarsa, kuma Amaryarsa yake fad’in “Amarya bakya laifi koda kin kashe d’an masu gida, da fatan kin isa lafiya.”

Murmushi tasaki tana fad’in “Alhajina akwaika da tsokana shekara goma shatakwas kake kirana da Amarya,
Da ace Suhailat tana raye aida munfara shiga sahun iyaye dan kuwa kasan kamar yanzun mun sami suriki.”
Murmushi yasaki domin shi kansa ta tayar masa da dafin b’atan ‘yarsa wacce tafi soyuwa a ransa,
Itama yanzon yasan tashiga cikin damuwar domin yasan da zarar akayi zancen suhailat sai ta zubar da hawayenta,
Gyaran murya yayi yace “Amarya kamar yanda yake kiranta meyafaru dake ne?” domin najiya a jikina kina tare da matsala.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button