BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Jamila taji dad’i sosai dajin Sauban Yana kan gadon asibity inda tashiga d’aki tarufe dinga rawa da murna tana Addu’ar Allah yasa daga can sai kabari,

A lokacin Da Abdullah ya dawo gida domin bincike sai ta marairaice ta zama kalar tausayi kamar zatayi kuka tashiga tambayarsa Yaya jikin d’anta Sauban?”

Kwantar Mata da hankali yashigayi ganin tana Shirin zubar da hawaye domin ya fahimci yanzun Jamila tana matuk’ar son Sauban,
Yashiga fad’in “kiyi hakuri insha Allah Sauban bazai mutuba zai Sami lafiya da Yardar Allah domin a halin yanzun anyi nasarar ceto numfashinsa ya dawo,
Wanda likitoci sunyi iya bincinsu sungano wani abi yaci a cikin abinci Wanda ansara gane ko meye.”

A zubure tace numfashinsa ya dawo kana nufin kace mun Yana motsi kenan?”

Murmushi Abdullah yasaki yace yafara motsi, yanzun binciken da mukeyi waye ya bashi abincin?”
Ta Ina aka zuba Masa abincin?”
Snn menene aka bashi yaci.”

Sarki yayi Alk’awarin muddun aka samo Wanda yayi wnn aikin zai fuskanci hukunci Mai tsanani
Hakan Nima ko waye idan asirin sa ya tonu sai yasha mamaki na,
Snn ki kula da SADEEQ da Sageer domin Suma komai zai iya faruwa dasu tinda akayiwa d’an uwansu hakan.”

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

DIDECTED TO Fateemah M Uthman

Page 11

Shuru tayi domin kwatakwata Bataso aka zo Mata da labarin cewar Sauban ya farkaba,
Ta d’auka ganin Abdullah da tayi a dai dai wannan lokacin mutuwar Sauban ce yazo ya fad’a Mata, Amma sai taji sab’anin hakan.”

Bata ankaraba tana cikin tinani ta Kuma jin muryar Abdullah Yana fad’in “ki daina tinani insha Allah Sauban zai tashi zai rayu zai Sami lafiya da Yardar Allah,
Ya mik’e tsaye tare da sanya talkaminsa yace “Ni natafi zamuje muci gaba da bincike Allah ya tona marar gaskiya”

Girgiza kai kawai tayi da kyar ta bud’e Baki tace “Allah ya bashi lafiya.”

“Ameen yace “yayi ficewarsa.”

Tana ganin fitarsa ta mik’e tsaye tashiga safa da Marwan tana tinanin idan bincike yayi bincike asirinta ya tonu, wani irin hali zata shiga idan asirinta ya tuno aka gano cewar itace tabashi magani yaci domin ya mutu,
Wanda itama kanta batasan ko wanne irin magani bane, ita dai , a wurin bokanya jakadiya ta karb’o Mata shi.”
Shin wanne irin hukunci ne sarki ya tanadarwa Wanda ya aikatawa jikansa hakan.”

Zufa tashiga wanke Mata fuska,
Tana cikin wnn Halin kuyangarta ta shigo ta zube a gabanta tana fad’in “ranki ya dad’e sarkin gida Yana son magana dake.”

Gabanta ya yanke ya fad’i ta kalli kuyangar tace “meyafaru me Yake so yacemun?”

“Ranki ya dad’e Nima bansaniba Amma yace “afad’a maki magana zakuyi Mai mahimmamci .”

“Kije kiyi Masa iso ki ajiyeshi a falon saukar Baki kifad’a Masa Ina zuwa.”

“To ranki ya dad’e Allah ya k’ara maki lafiya, kuyangar ta mik’e tafita domin ai watar da umurnin uwar d’akin nata.”

Sai da aka d’auki kusan minti 15
Bata fitoba sai da ta dai dai ta natsuwarta akan rud’anin da tashiga sannan tafito cikin k’asaita da nuna Isa tanufi inda sarkin gida Yake a zaune a d’akin Baki.”

Tana zuwa cikin Isa da nuna mulki ta nemi kujera ta zauna,
Wanda dama sarkin gida Yana zaune a kan cafet,
Sai da ta zauna ta d’auki k’afa d’aya ta d’ora akan d’aya snn ta juyo ta kalli sarkin gida dake durk’ushe a gabanta Yana fad’in “barka da fitowa gimbiya barka da fitowa sarauniyar gobe Kuma fulanin sarki in Allah ya yarda, Allah ya k’ara maki lafiya,

Tsawa ta daka Masa domin tin farko sarkin gida baya cikin tsarinta asalima haushi yake Bata saboda suffar munafukai garesa, don Yana tsananin shiri da Hajjah sannan ta lura Yana matuk’ar son Sauban da kulawa dashi akan yaranta dako kallon banza basu ishesaba.”

“Me Yake tafe dakai ta fad’a a tsawace.”

Murmushi yasaki domin yasan Bata son ganinsa, yace “ranki ya dad’e zuwa nayi domin na jinjina maki akan namijin k’ok’arin da kikayi hak’ik’a kinyi matuk’ar k’ok’ari wurin samun nasarar Sauban yaci abincin dakika dafa a jiya, saboda Sauban yarone Mai tsananin wayau Kuma bayacin abincin kowa sai na Hajjah.”

Zaro Ido tayi cike da firgici,
Ko me tatina a Nan take ta Kuma saita kanta tare da daka Masa tsawa “rufemun Baki mekakeso kace ne?”
Kana nufin nice nazubawa Sauban wani abin a cikin abinci domin yaci ya mutu?”
Ko kana nufin nice nayi yunkurin kashesa?” Lallai kanaso kayi Wasa da rayuwarka,
Binciken da aka turoka kayi mun kenan?”
to bara kaji kada ka manta Kai sarkin gida ne, Ni Kuma gimbiya ce ko yanzun idan naso zan iya cireka daga matsayin da kake nabawa wani snn daga k’arshe idan naso zanyi sanadin barinka gidan gaba d’aya, Dan hakan. Ka tsaya iya matsayinka kada kayi yunkurin shiga hurumin da banaka ba.”

Sarkin gida yace “hakan ne gimbiya matar yarima, gskya kina namijin k’ok’ari a cikin gidan Nan.”
to Amma Ni abinda bansaniba shine komeye ribarki ta son kikashe Sauban?”
Kina tinanin idan binciken da sarki yakeyi idan ya gano kece sila komeye makomarki?”

Waifa Ina ganin Dubara ta b’ace maki idon ki a rufe Yake shiyasa Kika aikata abinda Kika aikatawa Sauban,
diba kigani.”

Ya Ciro wayarsa a Aljihunsa ya kunna video tin lokacin da Sauban yashiga b’angarenta har zuwa lokacin da yafito har fad’uwar da yayi da lokacin da ya fad’i ta lek’a ta gansa yashe a k’asa tasaki dariya ta koma ta rufe k’ofarta.”

Murmushin mugunta sarkin gida yasaki yace “mezakice Dan ganne da wnn video snn bashi kad’ai bane na ajiye wani a wuri Mai mahimmaci,
Ya mik’e tsaye yace idan kinshirya magana Dani Zaki iya nemana tin kafin lokaci ya k’ure maki.”

Jikin Jamila duk yayi sanyi hankalinta ya tashi zufa sai tsiyaya take Mata a jiki kamar wacce tafito daga wanka takasa bud’e Baki tayi magana
Har sarkin gida ya Kai bak’in k’ofar fita, sannan tamik’e tsaye tace “dakata sarkin gida.”

Cak ya tsaya batare da yajuyo ya kalletaba,
Tafiya ta farayi sai da tazo daf dashi ta tsaya tace ” nawa kake buk’ata domin ka rufe wnn maganar?”
zan baka duk abinda kake so in har zaka rufe wnn maganar a cikin gidan Nan.”

Murmushi sarkin gida yasaki domin anzo wujen dama abinda Yake buk’ata yaji daga bakinta kenan saboda yasan watan arzikinsa ya kama.”

Juyowa yayi ya kalleta yasaki murmushi yace “miliyan biyu kawai nakeso daga gareki ba yawa.”

“Bani account no naka tace a tak’aice,
Cikin sauri yashiga karanto mata,
Yana Nan a tsaye cikin minti talatin yaji alert din miliyan uku.”

Ta dubeshi tace harda k’ari naiyimaka domin bana buk’atar naji makamanciyar wannan maganar
Kafi kowa sani komai zan iya aikatawa Wanda ya zalinceni,
Kasani muddun maganar Nan tafita bayan nabaka kud’ina kasani da Kai da zuri’arka Kuna cikin tsaka Mai wuya mutuwa ko rayuwa.”

“Bakida matsala indai wnn ne ai tinda kin biya shikenan,
Ya Kuma zuwa gabanta ya durk’usa yace “kina burgeni ranki ya dad’e kud’i ba matsalarki bane shin me zai Hana kisaki kud’i domin a aika da Sauban lahira.”

Murmushi tasaki ta taka zuwa kan kujerarta ta zauna,
shima sarkin gida ya dawo ya zauna a gabanta domin yaga maganarsa tasamu karb’uwa a wurinta.”

“Mekake gani za’ayi domin biyan buk’ata ta na ganin sauban ya bar duniya?”

“Ranki ya dad’e ai wnn aikin Mai sauk’i ne abinda za’ayi shine, kisaye likitan dake kula dashi a asibity da kud’i, ya masa allurar guba a Nan take zai mutu wnn shine mafita.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button