BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Hannu yasaka ya rungumeta tare da runtse idonsa, sai da suka d’auki minti goma a hakan snn ya Janyeta a jikinsa aka bashi umurnin ya rik’a hannunta ya d’aga sama kowa yagani kamar yanda Al’ada ta tanadar kamar ynda jarmai yayi.”

D’aga Hannunta yayi idonsa a rufe sakamakon biyu biyu da yake ganin mutane, ya kasayin magana,
Maigari yana ganin hakan yaturo dagaci yayi magana a maimakon yarima,
Yagaci ya fara magana kamar hakan “yarima Safna takace ka mallaki safna idan akwai Wanda yakeda ja yafito su Kara da yarima,
shuru kowa yayi, ba mai bakin magana,
Sai da dagaci ya maimaita har sau uku ba Wanda yakeda ja,
Snn wuri ya d’auki kuwa da sowa,
Masu bakin ciki sunayi masu farin ciki sunayi.”

Ganin yarima yana Neman fad’uwa cikin sauri fadawa suka rik’ashi suka nufi gidan gona dashi.”

a nan take taro ya fara watsewa inda aka yayyafawa Jarmai ruwa, anan take ya farfad’o daga suman da yayi yana borin kunya yana fad’in ina yariman yake yafito mukara a karo na biyu waye yafad’a masa anaja da Jarmai.”

Sowa mutan gari suka shiga yimasa cike da murna don kuwa anan take Allah ya cire masu tsoronsa a ransu.”

Duk abin nan da akeyi fadawan da Saudat ta turo suna kaimata rahoton komai har Dukan da akayiwa yarima da cinye shad’in da yayi duk sunfad’a mata
Suka k’ara da cewa ranki ya dad’e yarinyar ta cacci hakan kodan saboda kyawon da Allah ya Mata,
Dan kuwa yarinyar kyakkyawa ce yanda kika san Al’ajana.”

Wani irin ihu Saudat tasaki tayi jifa da wayar hannunta ta cire d’ankwalin kanta tana fad’in k’aryane wlh, na rantse da Allah sainayi Ajalin duka zuri’arsu

Tofa

Mrs Anas NASA
[9/4, 7:56 AM] Hayat: REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 25

“Tamkar mahaukaciya hakan saudat ta koma sai ihu takeyi tana jifa da duk abinda yatari gabanta, tana fad’in k’arya ne wlh ba wata shegiya data isa ta aure mun miji,
in har inada rai ina motsi a doron k’asa.”
Cikin sauri tamik’e tsaye tanufi wurin wayar wacce tayi jifa da ita can gefe d’aya,
Allah yasa bataci screen ba,
Ido rufe Tashiga Neman number mahaifiyarta sarauniya Bilkisu.”

Bugu d’aya zuwa biyu sarauniya Bilkisu,
Tabada umurni a d’auki wayar
Cikin sauri Kuyangi suka d’auki wayar tare da Kara mata a kunneta,

Muryar safna taji tana kuka sosai kamar wacce akayiwa mutuwa.”

Cikin tashin hanki da hanzari ta karb’i wayar daga hannun kuyanga ta juya ta kallesu tayi masu umurnin subar d’akin,

Da hanzari suka fita daga d’akin,
cike da tashin hankali take cewa my daughter meya faru kike kuka?”
A duniya na tsani naji kukanki banason zubar hawayenki meyake damunki?” Meyake faruwa?”
Me kikeso?”

Kuka saudat takeyi sosai, tana fad’in mommy Sauban ne,
Mommy sauban kishiya zaiyi mun, Sauban aure zaiyi mommy”

“Aure sarauniya bilkisu tace cike da firgici,
K’arya ne wlh bai isaba,waye shi da zai yi maki kishiya,
nawa kike yaushe aka haifeki,
da a turai muke ko a cikin lissafin aure ba’a d’orawa akanki bare azo akan maganar kishiya,
Na rantse da Allah ‘yata bazata zauna da kishiya ba
kamar yanda nima bana zama da ita.”

‘yar Gidan Uban waye?” Wani matsayi keda ubanta?”
‘Yar gidan wanne hamshak’in ne a cikin garin Adamawa?”

Saudat na kuka tace “ba ‘yar gidan uban kowa bace,
‘yar k’auye ce ko a k’auyen a can cikin k’auyen Fulani k’azamai marasa wanka masu warin nono da manshanu.”

tasaki kuka tana fad’in Yana tsananin sonta domin har da dukansa akayi akan son da yake Mata wai duk a cikin Al’adar k’auyen ne. Domin kawai yasameta, mommy ya zanyi da rayuwata nashiga ukuna.”

mommy ta fusata tace baki kishiga ukuba, domin “Bai isaba wlh sai dai ya mutu akan son da yake mata amma bazai tab’a aurenta ba, ba zai tab’a kawota cikin gidanki a matsayin kishiya ba.”

har Abada sauban bazai tab’a yimaki kishiyaba in dai inada rai da numfashi a duniya,
Waye sauban waye ubansa ko uwarsa da tana a raye bata isa ta ja daniba bare shi din banza.”

Mataki na farko da zamuyi amfani dashi shine,
duk wata zuri’ar da ita yarinyar suke Alfahari da ita sai mun hallakasu.”

Gobe zanturo dakaru tare da kayan aiki gaba d’aya su ruguza k’auyen da duk a halin dake cikin k’auyen ke harda ma mutanen dake rayuwa a cikin k’auyen,
A cinnawa gidansu wuta duk su k’une, bana buk’atar koda ganin gawarsu ayi.”

A tashi k’auyen gaba d’aya kowa ya huta, kinga idan mukaYi hakan Ankare da matsalarta ki sanyawa rayuwarki bake ba kishiya har Abada indai inada rai da lafiya ynda ban zauna da kishiyaba hkn kema har abada bazaki zauna da itaba.”

Dariya Saudat tasaki cike da farinciki tana fad’in “nagode mommy na Dan hakan nake tsananin k’aunarki fiye da daddy domin kece Mai sharemun hawayena bakyason ganin kuka na,

Kuyi hkr d wnn yau banajin yin typing din

mrs Anas Bawa

[9/8, 12:57 AM] Hayat: REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 26

“A kan gado fadawa suka ajiye Sauban inda yake rufe da ido shi kad’ai yasan zugin zafin da yakeji a bayansa,

Safwan ya taimaka masa yacire masa rigar jikinsa yana masa fifita, ganin shatin bulala ya kwanta a bayansa yayi masa jajir akan lallausar fatar jikinsa Abu ga farin mutum gwanin ban tausayi.”

Cike da jin haushi safwan yace “meye hakan ka janyowa kan ka kaga kuwa yanda jikinka da bayan ka, da duk ilahirin jikinka yayi?
Wani irin so kakeyiwa safna Wanda har kake neman hallaka kanka da rayuwarka,
a kan macce, na rantse da Allah ko ni kaina da nafika damuwa da macce bazan iya wnn wahalar ba,
nafison na barta ko wacce ce har Abada in dai har sai anyimun irin wnn dukan za’a bani ita, haba ga mata nan ‘yan birni birjek sai ka darje saika zab’a.”

Ni yan zun ban san yanda zanyi da kaiba gashi wnn zuwan bamuzo da doctor ba kamar yanda muka saba zuwa dashi a duk lokacin da zamuyi tafiya mai nisa.”

Wani bafade yashigo da sallama ya tsuguna a gaban safwan yana fad’in ranka ya dad’e mahaifin yarinyar akayi shad’inta ne,
tare da yarinyar suke neman iso.”

Mere baki Safwan yayi domin cike yake dajin haushin halin da sauban ya jefe kansa a kan macce,
A bazata yaji muryar sauban yana fad’in “kace masa ya shigo.”

Sauri Safwan yayi ya juya ya Kalli sauban, yace “Ashe dama kana iya magana kabarni inata surutu ni kadai kamar mahaukaci.”

Harara sauban ya jefa masa tare da jan tsaki.”

Sallama Baba ta katse Safwan daga maganar da yakeyi, son ya mayarwa sauban.”

Baba ya shigo Safna tana biye dashi a baya wurin zama Safwan ya nuna masa akan kujera tare da gaidashi.”

Amsa gaisuwar yayi tare da girgiza Kai,
ya zauna k’asa yana fad’in Barni na zauna anan ya isa,

Tsaye safna tayi idonta a kan yarima tana kallonsa cike da tausayi ganin duk jikinsa yayi ja akan kwancin bulala,
Shima idonsa a kanta yana kallon fuskarta anan take yaji wani irin farin ciki da kuzari sunzo masa a lokaci d’aya, ya dafa gado ya Tashi zaune tare da yanyo rigarsa ya rufe jikinsa ya Kalli baba yace “Baba ina wuni.”

Lafiya k’alau Baba yace yaya k’arfin jikinka?”.

“Alhmdulillah sauban yace idonsa nakan safna dake sharar hawayen tausayinsa.”

Baba ya Ciro wani magani a Aljihunsa ya tashi daga inda yake yanufi wurin yarima yana fad’in “ranka ya dade magani nakawo maka Wanda zai taimakeka wurin kariyar dafin bulala.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button