BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Mutum biyu Yana kashewa Akan sun furta suna Sona,
Hakan ya Hana Audu yin magana Dani,
Shi kad’ai Yake magana Dani duk a cikin garin Nan, Dan hakan idan nafito kowa baya son ya ganni bare yayimun magana Domin gudun wahalar Jarmai,
Idan nafito kiwo zai dinga zagayena duk ranar da Mai rabon wahala yasa yayimun magana a ranar sai dai uwarsa ta haifi wani.”

Wnn dalilin yasa nadinga fad’a maka Kayi nisa da rayuwata gudun kada ya ganmu a tare yayi maka illah sai gashi kasayeshi da kud’i a lokaci d’aya.”

Ta fashe da kuka Mai sauti tace “tayaya zaka taimakeni?”
Kabarni kawai har zuwa lokacin da mutuwata zatazo ta daukeni Dan kuwa bana da gata, iyayena sun zubar Dani a lokacin da nake da buk’atarsu.”

Sosai idon Sauban yacika da hawayen tausayinta,
Ashe a duniya akwai Wanda yafishi shiga cikin matsalar rayuwa?”

Saurin goge hawayen fuskarsa yayi Dan gudun kada tagansa,
Yasanya handkichif yashiga share Mata hawayen dake zuba Akan fuskarta ji Yakeyi kamar ya janyota ya rungumeta, shima ya fad’a Mata damuwarsa,
kukanta ya tsaya cak jin hannun D’an birni a kan fuskarta Yana share Mata hawaye,
Sai da ya goge Mata hawayen tas snn ya juyo da ita suka fuskanci juna yace “daga yau kukanki ya k’are, bana son ganin zubar hawayenki.”

Safna Kin Amince Dani?”

Ta d’aga kai alamar eh.”

Ya Dan saki murmushin gefen Baki, yace “yanzun a wane wuri Audu yake Zama?”

Tace “Audu baya gari yatafi binni sai ana gobe shad’i zai dawo.”

Girgiza Kai yayi alamar gamsuwa zaiyi magana Kenan wayarsa ta dau ringing yacirota yayi a gaban Aljihunsa ya duba safwn yagani yaja dogon tsaki ya d’auki wayar tare da karawa a kunnensa yayi shuru batare da yayi maganaba ,
“Muryar safwan yaji Yana fad’in “aboki kana Ina ne nadubaka banganka ba.”

“Meyafaru?” Sauban yace.”

Tambayar me yafaru tabawa safwan haushi, yace ai Kaine zan cewa meyafaru sabida a yanda naji muryarka baka cikin natsuwarka
Kana ganin la’asar ta gabato kazo muyi Shirin tafiya, kamanta ne har zamfara zamutafi, Wai kana Ina ne hakan?”

“Bansaniba Domin baka aikeniba,
Kajira gani Nan zuwa yanzun.
idan kuma a matse kake kana iya komawa gida,
Dan nasan abinda zaka cemun kenan.”

Dariya safwan yasaki, wacce yasa Sauban yayi saurin kashe wayar tare da Jan dogon tsaki,
Mik’ewa tsaye yayi Yana kallon Safna yace “ki waita Addu’a kisanya Allah a gaba domin shine Mai yin komai,
Ki daina ganin laifin mahaifanki domin bakisan dalilin da yasa suka jefar dakeba.”
Ki daina yawan kuka saboda kuka yakan haifar da matsaloli a lafiyar D’an Adam.”

Snn ki yawaita zagayowa wurin Nan saboda a Ko wanne lokaci zan iya zuwa nemanki a Nan.”

Ya juya yayi tafiyarsa har yayi nisa ya juyo ya kalleta yaga shi take kallo tana murmushi, D’an murmusawa yayi yace “kicire tsoro Jarmai a ranki domin babu wani abu da ya Isa yaimaki Kuma insha Allah bazaki aure Shiba,
Ya juya yayi tafiyar sa.”

Tafiya yakeyi tunaninta yake tare da juya magagganun da ta fad’a Masa dangane da rayuwar ta,
Tabbas tana buk’atar taimako.”

A hakan har ya Isa gidan gonar ba Wanda yaga dawowarsa Kai tsaye d’akinsa yanufa ya fad’a kan gado yayi filo da hannunsa yashiga duniyar tunani,
Ba abinda yake tunani sai ta wacce hanya zaibi domin ya taimaketa,
D’an karamun bakinta yashiga hangowa yanda take juyashi tana Masa magana, tare da manyan idanunta masu zubar da Hawaye,
Tabbas Safna tana da kyau domin ko a turai baitaba wacce tayi kyantaba, wahalace da danti yasaka kyawon nata ya kusan disashewa.”

Dogon tsaki yaja ya Kuma mirginawa, tare da janyo filo,
Sai mutum yaji a kan filon,.
D’aga idonsa yayi domin ganin ko waye,.safwan ya gani kwance Yana kallonsa cike da mmki.”

Tsaki ya Kuma ja Yana fad’in “meye hakan safwan?”

Safwan yace “meye hakan Sauban da ka kusan Hawa kaina.”
Me Yake damunka ne Naga duk ka birgice kashiga duniyar tunani kamar Wanda ya fad’a soyayya a lokaci Daya Ina kafito?.”

Jan tsaki Sauban yayi ya Kai Masa harara.”

Dariya safwan yasaki tare da sauka daga Kan gadon yace “ko tsaka da tayi tsaki Allah sai da ya tsine mata,
Malam katashi tinda kadawo mu fara Shirin tafiya kasan inada iyali.”

Kallonsa Sauban yayi yace “sai gobe zamu bar nan, ba yau ba.”
Daga hakan ya mik’e ya bar Masa d’akin, domin Yana da buk’atar Zama yayi dogon tunani Wanda yasan indai safwan Yana a wuri surutunsa bazai barka kayi wani nazariba,

kai Safwan a rage surutu kayi hakuri Sauban Nima hakan nake fama da nawa safwan din har ciwon Kai Yake sakani????????‍♀

Bin bayansa safwan yayi Yana fad’in “dakata malam Wai meyake damunka ne munzo lafiya k’alau lokaci d’aya duk ka wani birkice.”

Kyalesa sauban yayi yaci gaba da tafiyar sa yanufi wurin lambu domin shak’ata, daga yayi tinanin da ya damesa.”

comment dinku Yanayin k’asa sosai idan Naga ba’a comment zan ajiye rubutun na Bari sai Bayan sallah wata k’ila naci gaba?

Mrs Ana’s Bawa

Not edited

Mrs Ana’s Bawa

comment dinku Yanayin k’asa sosai bakwa comment shiyasa banajin k’arfin gwaiwar yi maku typing kullum, gaskiya idan Baku gyaraba ‘DAN SARKI SAUBAN zai koma na kud’i yasin ko a jikina????????‍♀

Mrs Ana’s Bawa

kome ke faruwa Kuma Sauban?????????

Mrs Ana’s Bawa

Mrs Ana’s Bawa

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 19

Kwance yake akan doguwar kujerar dake zagaye da lambun yana kallon sama, ya d’ora hannunsa Akan goshinsa ya lumshe idonsa da alama,
Tunani yakeyi,
babu abinda Yake Masa gizo a idonsa sai kyakkyawar fuskarta tare da D’an k’aramun bakinta a lokacin da take bud’eshi tare da juyashi tana fad’a Masa damuwarta.”

Dogon tsaki yaja ya Kuma juya kwanciya daya tina da yanda idonta yake zubar da hawaye alamar tasaba da kukan,
Kuma Jan wani tsakin yayi ya mik’e zaune tare da dafe Kai.”

Kallonsa safwan yayi dake gefensa a zaune akan d’aya kujerar dake kusa dashi Yana latsar laptop d’insa,
Ya d’an dakata da dannar laptop din yana kallon sauban tabbas akwai abinda yake damunsa a rai, shi dai iya saninsa lafiya kalau sukaxo k’auyen nan,
Murmushi yasaki yace “ya dai abokina?”
Tsakin da kakeyi akai akai nameye Allah yasa ba gamo Kayiba?”

Kuma Jan wani tsakin sauban yayi yamike tsaye tare da wurgawa Safwan harara Yace “idan kaga dama katashi mutafi muyi sallah magariba idan kuma sai ka tsaya yimun tambayoyin abinda yake damuna sai kayita zama, yayi gaba abinsa ya bar safwan yana kallonsa.”

Mere Baki safwan yayi ya rufe laptop d’insa ya mik’e yabi bayansa Yana fad’in idan tayi wari ai maji.”

Banza dashi Sauban yayi yaci gaba da tafiyarsa,
Bayan sun kammala yin sallar magariba dukansu suka fito fadawa sai gaisuwa suke kaiwa a gaban Sauban, d’aga masu hannu kawai yakeyi alamar ya amsa, ya wuce yayi gaba.”

D’ak’i yashiga ya fad’a toilet ya yyi wanka yafito ya canza Kaya izuwa jallabiya ruwan k’asa mai d’an gajeren hannu ya Sanya silifas yafito,
A tunaninsa zai ga safwan yabiyo bayansa cikin d’akin,
sai yaga ashe bai biyoshiba, yaji dad’in hakan,
sannu a hankali ya sulale ya fita ta k’ofar baya yanda ba wanda zai ganinsa,
cikin gari ya nufa Kai tsaye batare da kowa ya gansa ba.
Kasancewar duhu ya Fara mamaye garin gashi ba wutar nepa, hakan yasa yayi amfanin da fitilar wayarsa ya kunna yashiga haska gabanshi.”

Wurin da suka zauna dazun yanufa, baiyi dibon dare neba, gudun kada wani abin ya cutar dashi kasancewar wurin dajine ba mutane a wurin sai yawan itatuwa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button