DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
Hmmmmm d’an hakin da karaina……ku iyar Mata friends
Mrs Ana’s Bawa✍
Hmmmmm muje zuwa friends da fatan kuna biye Dani Kuma Kuna fahimtata
Mrs Ana’s Bawa
Mrs Ana’s Bawa gusau????????
Yawan comment yawan typing idan naga ba’a comment to zai koma na kud’i KO a jikina????????♀
One luve my friends
Mrs Anas bawa ce,
Muje zuwa wnn karon naxo mku da wani sabon salon labari a kyauta????????
REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S✍
???? D’AN SARKI SAUBAN????
Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)
DIDECTED TO Fateemah M Uthman
Page 9
Hakan Jamila taci gaba da kula da yaranta Bata yarda kowa ya rab’e inda suke, bare a Kai ga d’aukarsu,
A kullum tunaninta za’a iya zuba masu wani mugun Abu a cikin abinci suci su mutu.”
Kuyanginta ma tare da bayi, kullum cikin sabuwar wahala suke tare da Azabtarwa musamman idan taji kukan d’aya daga cikin ‘ya’yanta to tabbas duk Wanda Yake kusa da d’akin da suke sai ya gane kurensa Dan yinin ranar a tsakar Rana zai k’are yininsa baci basha.”
A kwana a tashi ba wuya Wanda a yanzun Sauban Yana da shekara 12 a duniya Sadeeq Yana da shekara 6 Sageer Yana da shekara hud’u, makaranta d’aya suke karatu tare da Sauban Wanda a yanzun Sauban yake mataki na k’arshe a primary school d’insa jarabawar fita sukeyi.”
Sauban Yana tsananin son Yan uwansa Sadeeq da Sageer domin duk abinda yasamu a makaranta bashida wani buri illah ya Bawa Yan uwansa,
Snn duk Wanda ya Dakar Masa Yan uwa a lokacin za’aga b’acin ran sa, don komai girmansa sai ya Rama masu,
Hakan yasa soyayya tashiga tsakaninsa da Sageer a duk inda kaga sauban a makaranta Yana tare da Sageer, a tare suke cin abinci Wanda Sauban yake zuwa dashi,
Domin shi bayacin abincinsu, wnn umurni ne daga Hajjah tin Yana k’aramunsa take lurar dashi,
wnn dalili yasa ba komai yakeci ba, kwata kwata bayacin wani abin idan ba a hannun Hajjah yafito ba, ko a makaranta baya sayen komai sai dai ya sayawa ‘yan uwansa musamman Sageer da jininsu yafi had’uwa, Wanda shine k’arami a cikinsu,
Sadeeq Kuma sak halin mahaifiyarsa ya d’auko, baya k’aunar Sauban ko kad’an,
Ko a makaranta Yana yawan had’a Masa tarko cikin ikon Allah Sauban Yake k’etarewa kasan cewar yaro ne shi mai tsananin wayo, Yana kallon kowa tsaf yasan Wanda Yake sonshi yasan Wanda baya sonshi.”
A na hakan Sauban suka kammala jarabawarsu ta primary aka had’a masu biki na musamman,
Wanda harda sarki da Abdullah tare da Hajjah suka halarci bikin yayewarsu makarantar primary.”
Hakan Jamila itama tazo domin tana da labarin cewa harda Sauran classic za’a Bawa d’alibai kyauta wad’anda sukayi na d’aya Dan tana da yak’i nin har da yaranta a ciki saboda tana kiran malaman a bayan fage tana basu kud’i Dan su rik’a Bawa yaranta na d’aya ako WANNE k’arshen zango kamar yanda taga Sauban Yana d’aukar na d’aya,
Domin ta fahimci Sageer da SADEEQ ba wani k’ok’ari ne dasuba musamman Sadeeq, Dan har k’ara Sageer Wani lokacin Sauban yakan zaunar dashi ya koya Masa karatu idan suna makaranta.” Sab’anin Sadeeq da ba abinda yasani sai mungunta dason nuna mulki da Isa tin Yana k’aramunsa sak halin uwarsa????????”
Biki akeyi kowa sai murna yakeyi musamman Maimartaba da Abdullah da sukaga Ankira Sauban ya bud’e taro da Addu’a cikin harshen larabci, cikin natsuwarsa da kamalarsa tare da k’asaitarsa Mai fitar da kwarjininsa na jinin sarauta,
Bayan ya gama Addu’ar bud’e taro cikin harshen larabci snn ya koma magana cikin harshen turanci irin turancin Nan Mai kyau irin na mutanan England, tamkar ba’a bakinsa harafin turanci yake fitowaba,
Dad’i tamkar ya kashe duk wani masoynki sauban dake wurin
,
Amma Banda Jamila da takeji Ina wuta ta jefashi Dan bak’in ciki sai fad’i take a ranta tsinanne Mai halin uwarsa kaima ka kusan zuwa Ina tsinanniyar uwarka tatafi”
Bayan ankammala komai aka Fara bada kyaututtuka, inda Sauban ya samu kyauta ta musamman. Domin duk wani Mai fad’a aji Wanda ya halarci taron sai da yabawa Sauban kyautar ban girma tare da burgewa.”
A nan aka zo Sauran classic duk d’alibin da yayi na d’aya, a ka shiga Kiran sunansa d’aya bayan d’aya ana basu kyauta, Jamila sai murmushi takeyi tana gyara hannu tana jiran Akira yaranta taje da kanta ta k’arb’ar masu Dan Bata buk’atar wani yaje ya amso masu.” halinki ba kyau jamila ????
Sai da aka kammala Bawa ko wanne class taga ba’a Kira yarantaba haushi da takaici ya k’umeta,
Wayyo Allah kuxo kuga fuskar Jamila ganin ba’a Kira yarantaba bak’in ciki kamar ya kasheta ganin ko wanne yaro sai d’aga kyautarsa Yakeyi Yana Bawa mahaifiyarsa Amma Banda yaranta,
Lura da hakan da Sauban yayi yasa yasaki murmushi ya tako yazo wurin k’annensa ya janyo hannunsu zuwa jikinsa ya rungumesu Yana lallashinsu tare da cewa kuyi hakurin kunji k’annena,
Wani time d’in kuyi k’ok’ari, ku daina Wasa a karatu ,
Kuma za’a baku kamar hakan kunji.”
Sadeeq ya fisge jikinsa daga jikin Sauban ya nufi wurin mahaifiyarsa Yana sharar hawaye,
Sunan Sauban akaji ana Kira cikin abar magana Wanda tasaka kowa natsuwa,
Cikin takunsa yanufi wurin da ake kiransa a gaban governor yaje ya tsugunna Wanda shine yasaka akirashi,
Governor yana murmushi Yana kallon Sauban ya d’auki wata kyauta Mai girman gaske Wacce aka lullub’eta a cikin wata Leda Mai haske da kyalli,ya mik’awa Sauban.”
Hannu biyu Sauban yasaka ya amsa cike da girmamawa Yana godiya, ai Kuwa aka shiga yi masu hotona,
wayyo mutuwa kozo kuga idon jamila????
Idon kowa Akan Sauban ya mik’e a gaban governor Yana tafiyarsa cikin natsuwa yana d’auke da kyautarsa a hannu kowa sai kallonsa yakeyi Kai tsaye wurin Jamila yanufa ya durk’usa gabanta ya mik’a Mata kyautar
don ta Sanya Masa Albarka,
Ido kansu kowa sai kallonsu yakeyi cike da burgewa
Wad’anda suka San komai sun zuba Ido domin ganin yanda zata karb’eshi,
Ganin Ido kanta snn ga Abdullah da sarki Suma kallonta sukeyi suna murmushi,
yasa tasaki dariya ta k’arb’i kyautar tana murmushin Yak’e Wanda yafi kuka ciwo ta dafa kansa tana fad’in, d’ana kayi k’ok’ari sosai Allah ya taimaka.”
ai Kuwa aka shiga d’aukarsu hotona sai murmushin takeyi tana k’ara rungumo Sauban zuwa jikinta, a can cikin zuciyarta kuma jitakeyi kamar ta kurma ihu akan bak’in ciki,
Ganin idanu sun janye kansu Sauban ya koma wurin maimartaba ana hotona yasa tana ganin hakan tayi saurin mik’ewa tsaye tabar wurin tare da Jan yaranta suka shiga mota tanufi gida.”
Murmushi manyan Hajjah tasaki domin Sauban ya matuk’ar burgeta da yayiwa Jamila hakan,
Don ko yanzun zata gane idan Rana tafito tafin hannu baya rufeta.”
Ana hakan taro ya watse sarki ya dawo gida cike da farin ciki da annashawa, hakan Abdullah sai dai Jin zafinsa d’aya Banda Sadeeq da Sageer Wurin bada kyauta kamar yanda yaga ana Bawa Sauran d’aliban da sukazo na d’aya, yashiga tinanin
Kodai basa karatun ne?”
Hakan yasa suna sauka a mota ya nufi b’angaren Jamila,
Sageer da SADEEQ kwance a kan jikinta tana lallashinsu Sadeeq Yana fad’in Muguntace Sauban ya masu shine ya Hana a basu kyauta a makaranta Wanda Sageer yake cewa ba laifin Yaya Sauban bane laifin uncle ne,
Jamila ta dakawa sageer tsawa tare da zare masa Ido tana fad’in wnn yaron da a asibity na haifeka da nace anyi mun canjenka domin na lura gaba d’aya baka biyo halina ba,
Da zarar anfad’i laifin Sauban yi kakeyi kamar kafashe da kuka, ko ka dakemu,
To bara kaji ka bud’e kunnenka da kyau kaji Sauban ba masoyinku bane Dan ba d’ana bane banice na nahaifeshe ba, kaga ku biyun Nan ku kad’ai na haifa,
Sauban d’an ubane abokin gabarku ne, ko kashesa kukayi ba abinda zai faru, domin idan Baku kashesa ba kunaji Kuna gani zai hau kujerar sarauta,
ku Kuna gefe kuna kallo sai yanda yayi daku kun Zama ‘yan kallon kenan.”