DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
Sallamar Abdullah yasa taja bakinta tayi shuru illah ta had’e fuska domin Bata ga alamar Wasa a tare dashi ba.”
Wuri ya samu ya zauna cikin d’aure fuska tace “barka da shigowa,
“Yawwa yace snn kuyangi suka zagayeshi da kayan motsa baki.”
Kallonsa Sadeeq da Sageer sukeyi domin ba’a koya masu gaisuwa ba, shima bai damuba domin yasan irin tasu tarbiyar kenan,
Wanda yayi fad’a har ya gaji ba wani sauyi a tare dasu,
Kallonsu yayi snn ya d’aga masu hannu alamar su zo wurinsa, cikin sauri Sageer ya riga Sadeeq zuwa suka zauna a gefensa.”
Kallonsa Jamila tayi ta d’anyi murmushin tace yarona Sauban yayi k’ok’ari sosai.”
Shima murmushi yayi ya Kuma had’e fuska ya kalli sadig da sagir yace “meyasa bakuzo na d’aya aka Baku kyauta ba Kuma makaranta kamar yanda aka Bawa kowa?”
Ashe dama ba karatu kukeyi ba?”
Baza kuyi koyi da yayanku Sauban ba?”
Sageer yace munaso Abba,
Sadeeq yace “Ni nafison nafishi ta ko Ina.”
Murmushin Abdullah yasaki domin ya dad’e da fahimtar duk halin mahaifiyarsa sadeeq ya d’auko,
Yace “tayaya zakafishi bayan baka mayar da hankali a karatu ba,
Gargad’i na k’arshe da zan Kuma yimaku shine duk kuka kuskura hakan ta Kuma kasancewa sai na d’aukar maku mataki.”
Jamila tayi karaf tace “tayaya?”
A’a nifa bana son hakan, duk abinda ya faru da akwai wata a k’asa,
Kai kutashi kushiga daga ciki Allah ya rayamunku domin Ni ka d’ai ke sonku a cikin gidan Nan.”
Suka tashi cikin sauri suka nufi d’akinsu,
Ido kawai Abdullah ya zuba Mata baice da ita komai ba ya tashi ya fita Yana tir da Hali irin nata.”
Fitarsa b’angaren Hajjah yanufa ya d’auki Sauban ya fita dashi yanufi Gidan gonar mahaifiyarsa, Wanda ya lura da Sauban Yana matuk’ar son zuwa wurin Yana Jin dad’in KASANCEWARsa a cikin gidan gonar Koda yaushe tamkar mahaifiyarsa bintu
Sai kusan k’arfe bakwai suka dawo gida,
BaYan ya Kai Sauban b’angaren Hajjah snn yawuce masallaci sukayi sallar magariba tare da maimartaba suna cikin masallacin akayi Isha’i kamar yanda suka Saba a kullum,
bayan sun kammala yin sallar ne suka fito a tare suna tafiya dogarai na biye dasu a baya
Sarki yake cewa “Abdullah ya kamata kayi aure ka maye gurbin Bintu Wacce ta mutu,
Murmushi kawai Abdullah yayi bai tankawa mahaifin nasaba,
Sarki yaci gaba da cewa idan ka shirya ko a gobe zan d’aura maka aure, sai dai wnn karon mata biyu zaka aura a lokaci d’aya domin inason lokacin da zan sauka a kan kujerar mulki idan za’a d’oraka akai ya zamana kana da Mata hud’u kamar yanda aka San ko wanne sarki,
idan ka cireni daga ciki koni akwai dalilina nayin Mata d’aya.”
Murmushi Abdullah yasaki baiyi magana ba domin koshi Yana da buk’atar k’arin auren koba komai ya dinga samun kulawa ya Kuma dinga samun natsuwa idan buk’atarsa ta motsa domin Jamila yanzun Bata da lokacin komai sai mulki dasaka a gaba da hidimar yaranta.”
Sarki yace Kai nake saurare meye ra’ayinka ko baka buk’ata ne?”
Girgiza Kai Abdullah yayi cike da girmamawa yace “duk abinda kace shine dai dai,
Bana da zab’i sai naka a kullum burina nayi maka biyayya na faranta maka nasaka ka farin ciki, ko yanzun ka shirya Nima a shirye nake za’a iya d’auramun auren da ko wacce macce kake so zan karb’eta hannu biyu.”
Sarki yaji dad’in furucin Abdullah Wanda sai murmushi yakeyi Yana girgiza kai,
Ba Wanda ya sake yin magana a cikinsu har Abdullah ya Kai maimartaba d’akinsa kamar yanda yasaba idan suka dawo sallar, sai ya kaisa har d’akinsa snn yayi Masa sallama yafito yanufi d’akin Hajjah itama yayi Mata sallama snn yanufi nashi d’akin domin ya kwanta,
Wnn karon bayan ya Kai maimartaba d’akin nasa wuri yasamu a gefensa ya zauna tare da sunkuyar da Kai Yana jiran ya Sanya Masa Albarka kamar yanda yasaba snn yatashi yafita.”
Sarki ya juyo ya dafa kansa kamar yanda yasaba yashiga “fad’in Abdullah Allah yayi maka Albarka Allah ya sanyawa rayuwarka hak”ika wnn biyayya da kakeyimun Allah yabaka d’anda zai lunka maka fiye da hakan , snn kazama cikin shiri gobe za’a d’aura maka aure da wasu tsala tsalan bayi wad’an da Aka ‘yanta Naga sun dace da Kai Allah yabaku zuri’a Mai Albarka.”
‘Ameen Abdullah yace Yana murmushi Mai cike da jin dad’i.”
Wayarsa tayi ringing yayi kamar bazai d’aukaba sarki yayi murmushi yace ka d’auki wayar Mana.”
Cikin sauri ya Sanya hannu a Aljihu ya d’auko wayar,
Ganin sunan Abokinsa ne Wanda suka tashi a tare wato sarkin Bauchi Wanda mahaifinsa ya rasu aka d’orashi a kan kujerar mulkin,
Yana murmushin ya d’aga wayar tare da karawa a kunnensa da sallama a bakinsa, cike da tsokana Yake fad’in ranka ya dad’e sarki Allah ya k’ara maka lafiya ya kake?”
Murmushi Abdulrahaman yayi yace “yau Kuma ‘yar zolayace “to kiranka nayi domin nayi maka Albishir Sarauniya ta haihu ansami ‘ya macce.”
Masha Allah Abdullah yashiga fad’i tare da cewa Ina kusa da Abba gashi ku gaisa sai ka fad’a Masa.”
Jin hakan sarki yasan Abdulrahaman ne sarkin Bauchi yakira Abdullah domin shi kad’ai ne Yake kiransa Abdullah idan suna tare wani lokacin ya kan k’arb’i wayar su gaisa tare da lurar dashi akan abinda ya shege Masa duhu akan lamarin sarauta, kasan cewar mahaifin Abdulrahaman Amine ne a wurin sarki mahaifin Abdullah.”
Sarki ya amshi wayar ya kara a kunnensa Yana murmushi bayan sun gaisa,
Abdulrahaman Yake fad’awa sarki anyi Masa haihuwa ansami ‘ya macce,
Kasancewar matansa hud’u ba Wacce ta tab’a haihuwa sai yanzun.”
Masha Allah sarki yace tare da fad’ad’a fara’arsa yashiga fad’in “Allah ya raya SAUDAT yasanya Mata Albarka.”
Murmushi sarki Abdulrahaman yasaki domin yaji dad’in sunan da sarki yasaka ma ‘yarsa, yashiga fad’in Masha Allah sunan yayi dad’i Abba Allah yak’ara girma da d’aukaka, tabbas ada nayi rashin mahaifi Amma a yanzun samunka duk ya kawar mun da Kashi hamsin a cikin d’ari na Rashin mahaifi da nayi, nagode Abba,
yashiga godiya sarki Yana amsawa Yana murmushi snn ya mik’awa Abdullah wayar.”
Abdullah ya k’arb’a Yana fad’in sunan ‘yarmu Saudat lallai Abba ya it’s zab’en suna Mai dad’i, Allah ya raya Mana ita sai munshigo bikin suna gaba d’ayanmu.”
Hakan sukayi sallama ya kashe wayar,
Snn yayiwa maimartaba sallama ya tashi ya fita cike da farin cikin gobe ne d’aurin Aurensa snn Babban Amininsa ya samu k’aruwar ‘ya macce wacce sarki ya SAKAWA suna “SAUDAT.”
Washe gari ya Kama ranar juma’a kenan a babban masallacin k’ofar gidan sarki bayan an kammala sallar juma’a aka d’aurawa Abdullah Aure da bayinsa Khadija da Aishat, d’aurin auren da kowa ya shaida.”
Wanda Jamila sai dai ta tsinci maganar daga sama bayan anyi komai angama,
Anan take sarki yasaka aka gyarawa kowa part d’inta kasancewar part 4 a b’angaren Abdullah,
Wnn aure ya ba k’anwata Jamila rai musamman da taji duk bayine aka ‘yanta Kuma aka aurawa mijinta.”
Jikinta baiyi sanyiba sai da safiya ta waye suka shigo gaida ita, anan taga zallar kyau da kwarji, batasan lokacin da idonta ya rufeba tashiga surfa masu ashar tare da korarsu daga b’angarenta.”
Kasan cewar sun san halinta Sarai yasa ko wacce daga cikinsu hankalinta bai tashiba illah ma suka sakar mata murmushi suna fad’in Allah ya hushi zuciyarki, dama Yarima ne yace muzo mugasheki ba Wai yin kanmu bane,
suna fad’in hakan suka tashi suka bar Mata sashen nata.”