DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
Dariya Jamila tasaki Mai sauti tace “Ashe dama kana da wnn tinanin da hikima tin tini ka gujeni ka nuna k’iyayyata a fili?”
Kiyi hakuri ranki ya dad’e kece tin farko Kika nuna tsana ga gareni, wnn dalilin yasa bana wata alak’a dake sai dasu Hajjah wad’anda babu abinda suka tsinanamun tin iya zamana dasu sai dai nayita masu bauta Ashe ke Alheri ce.”
“Ya Isa tace.”
“Ta Yaya zanga likitan domin muyi maganar?”
Ranki ya dad’e indai Zaki saki kud’i ganin likita baya da wani wahala Ni da kaina zan d’auko maki shi na kawo makishi har cikin falonki.
Sabida kinsan Hajjah da sarki sun yarda Dani d’ari bisa d’ari.”
Murmushin farin ciki Jamila tasaki tace “ka burgeni ban tab’ajin farin ciki irin na yau ba,
Kaje ka d’auko mun likita ko nawane zan bashi in har burina zai cika ganin Sauban ya daina motsi a doron k’asa,
kaima zakayi murmushi domin idan burina ya cika za kayi mamakin abinda zanyi maka.”
“Godiya nake ranki ya dad’e bara natafi kada a ga mundade a wuri d’aya a zargi wani abin, ki Sanya idon ganinmu xuwa anjima tare da likitan.”
Bincike akeyi sosai a cikin gidan sarautar domin ganin an kamo masu hannu a cikin wad’anda sukayi yunkurin kashe Sauban,
Ba wani abu da aka gano ko wata alama,
Wanda har da Jamila ake binciken wnn yasa ta b’atarwa mutane da hankali akan ayi bincike a kanta.”
Saboda tana matuk’ar nuna bakin cikinta Akan abinda ya faru,
Inda Abdullah yake Mata kallon tafi kowa shiga cikin damuwa na faruwan lamarin wani lokacin har lallashinta yakeyi.”
Sarkin gida sai zirga zirga yakeyi tsakanin gida da asibity domin Hajjah tayi matuk’ar yarda dashi duk abinda za’a sawo Dan gane da magani ko wani abun to shi ake Bawa kud’i Ya sawo,
Wnn dalilin yasa yasamu damar keb’ewa wuri d’aya dashi da likita ya fad’a Masa cewar gimbiya tana buk’atar ganinsa yau da misalin k’arfe 8 na dare.”
Likita bai kawo komai a ransa ba,
domin yaga yanda sarkin gida yake zirga zirga a asibityn sannan ya lura da yanda aka yarda dashi
Ganin anyarda dashi d’ari bisa d’ari yasa baiyi tinanin komaiba ya amsa Masa da to idan yatashi daga asibity idan zai koma gida Yana Nan tafe,
Yashiga tinanin wata k’ila akan maganar ciwon Sauban ne take nemansa.”
Misalin k’arfe 8 sarkin gida ya tsaya a can bayan asibity inda ba Wanda zai iya ganinsa yakira likita a waya, cikin minti 5 likita yafito daga asibity dama lokacin tashinsa yayi, ya tarar da sarkin gida ya d’aukeshi a mota ya nufi wurin gimbiya Jamila dashi.”
Hak’ik’a Jamila tayi farin cikin ganin likita a gabanta zaune sai murmushi take saki a fuskarta,
Ta kalli likita da kyau tace “barka da zuwa doctor.”
“Yawwa hajiya barka da gida Yaya iyali?” inji likita.”
Bata amsa Masa ba tace “Yaya jikin Sauban d’in ?”
ta kuma jeho Masa wata tambyar.”
“Alhamdulillah sauki yanata shigosa sai dai har yanzun lakkan jikinsa Bata Fara aiki ba domin. Abinda akayi amfani dashi, Yana da k’arfi sosai domin yafi guba masifa a jikin d’an adam Wanda har yanzun mun rasa Gane ko meye.”
Murmushi ta saki ta girgiza Kai, tace “likita katab’a rik’a miliyan 20 a matsayin naka na kanka?”
Wata irin zabura tare da Zaro ido sarkin gida yayi Jin Ankira miliyan 20 to Ashe shi da yace abashi miliyan 2 kad’an ya d’iba kenan tab da yasani da yace sai anbashi miliyan goma.”
Girgiza Kai likita yayi yace “ranki ya dad’e a Ina zanga miliyan 20 bare har na rik’eta, kinsan aikin namu a k’ark’ashin wani mukeci, sai dai idan wata ya k’are muke k’arb’ar Albashi Wanda bazai wuce dubu 80 ba dashi muke rufawa iyalinmu asiri tare da ‘yan uwanmu.”
Wani shu’umin murmushi Jamila tasaki tace “kana son ka mallaki miliyan 20 naka nakanka?”
“Kwarai Kuwa likita yace tare da Kuma gyara Zama.”
Jamila tace “so nakeyi a matsayinka na likita Wanda kasan sirrin jikin d’an Adam so nake kasan yanda zakayi cikin hikima da dabara irin taku ta likitoci ka kawar mun da Sauban yaron gidan Nan Wanda kake kula dashi, ya bar duniya.”
Idan ka kawar dashi to kasani zaka mallaki miliyan 20 Kai har da ma k’ari domin zan K’ara yi maka wata kyautar ta ban mamaki.”
Zaro Ido likita yayi gumi ya shiga wanke Masa jiki, ga k’oshi ga kwanan yunwa,
Yana son kud’i sosai Yana son ya mallaki miliyan 20 din Nan, to Amma idan asirinsa ya tonu Yaya zaiyi da sarki maimartaba Yaya zaiyi da aikinsa Wanda ya dad’e Yana nema da kyar yasameshi.”
REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S✍
???? D’AN SARKI SAUBAN????
Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)
Page 12
Taimakon Gaggawa aka shiga Bawa Sauban inda aka sakashi a cikin wata na’ura domin ceto rayuwarsa.”
tayi yunkurin shiga inda yake likitoci suka dakatar da ita tare da Bata hakuri da lallashin akan bazata Sami ganinsa ba,
Sai Nan da wata d’aya domin Yana cikin wani yanayi Wanda Addu’arsu kawai ake buk’ata”
Shuru Hajjah tayi taja da baya, hankalinta a tashe Dan ganin takeyi Sauban bazai tashiba mutuwa kawai zaiyi, dibo da yanda taga wani irin kunfa Yana zuba a bakinsa,
Wuri ta nema ta zauna fadawa suka zagayeta babu abinda takeyi sai Addu’ar Allah yabawa Sauban lafiya tare da rayuwa Mai d’orewa.”
Gimbiya bilkisu ta matso kusa da Hajjah tace “umma kiyi hakuri da izinin Allah Sauban zai tashi, zai Sami lafiya, har Abada makiya baxasu tab’a samun galaba akansa ba,
Kizo mutafi masaukina ki ki huta har zuwa gobe idan Abdullah yaxo sai a San mafita.”
Hakan Hajjah ta amince tabi Gimbiya bilkisu tare da fadawan,
Ko can d’in hakan bilkisu da Anna sukayi ta kwantarwa Hajjah da hankali snn ta Fara sakin jikinta a gidan, sai dai duk wani motsi nata da t Sauban a bakinta tana jera Masa Addu’o,e.”
Duk iya bincike anyi ba wata alama da tanuni akwai sa hannun wani daga cikin gidan sarautar wurin yunkurin kisan Sauban, domin duk abinda za’ayi Jamila tana tare da Abdullah ana binciken da ita ba abinda takeyi sai aikin kuka a cewarta tana tsananin tausayin Sauban Halin da makiya suka sakashi me ya tare masu a duniya.”
Ba abinda Abdullah yakeyi sai Bata hakuri,
hakan yasa ba Wanda yataba kawo bincike a kanta
, hakan shima sarkin gida, Wanda duk abinda za’ayi a gidan shine a gaba Yana bada tashi gudun mawar, sabida Yar jajen sarki ne da Anna sunyi imani bazai tab’a cutar dasu ba, Dan hakan Koda Wasa ba’a tab’a kawo komai a kansuba.”
Hakan aka kammala bincike ba wani haske da aka samu, hankalin kowa ya koma England wurin Sauban washe gari Abdullah ya shiga jirgi ya sauka k’asar England domin dibo jikin sauban.”
BaYan tafiyarsa da sati biyu komai yayita faruwa daga ciki har da samun nasarar samun lafiyar sauban, domin numfashinsa ya dawo har ya Fara motsi, anyi nasarar gubar Bata iyar da gauraye jikinsaba batayi tasiri a jikinsaba “
Satin Abdullah biyu a can ya dawo gida Nigeria tare da sauran bayi hud’u aka barwa Hajjah d’aya da kuyanga d’aya tare da Anna, domin ganin lafiya ta fara samuwa ga sauban duk da dai har yanzun ba Bari akeyi ana ganinsaba Yana cikin na’ura.”
Gimbiya bilkisu itake hidima dasu Hajjah wacce ba yanda Abdullah baiyiba Akan zai kamawa su Hajjah wurin zama Amma saita nuna b’acin ranta, tana fad’in wato zai nuna cewa Hajjah shi kad’ai ta haifa, Banda su kenan,
Har sarki Abdulrahaman ta bugawa waya ta fad’a Masa Wanda shima yanuna b’acin ransa sosai dajin abinda Abdullah yace, hakan dai Abdullah ya basu hakuri yabar Hajjah a Nan snn yadawo gida Nigeria a cewarsa idan Sauban ya cika wata daya kamar yanda likitoci sukace zai Kuma dawowa tare da maimartaba domin su dubashi.”