DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

A d’an Zaman da Hajjah tayi tare da gimbiya bilkisu ta Gane bilkisu macce ce Mai tsananin nuna mulki da Isa tare da izzah, sannan tana tsananin nuna soyayyarta ga tilon ‘yarta wato Saudat,
Tana son Saudat sosai Wanda sabida son da take Mata Bata bawa kowa rainonta kamar yanda aka San matar sarki Bata rainon d’a da kanta, tsakanin ta da yaro sai dai idan ankawo shi yasha nono, Amma bnda gimbiya bilkisu wacce
a kullum tana tare da ‘yarta hakan shima sarki Abdulrahaman da zarar ya bugo waya baya da wata magana sai ta Saudat,
Hajjah ta jinjinawa wnn soyayya da sukayiwa Yar su kwaya d’aya tilo”
BaYan wata d’aya Alhamdulillah jikin Sauban yayi kyau yasamu lafiya Wanda har magana yakeyi Kuma Yana cin abinci sosai.”
A ranar sarki da Abdullah tare da sarki Abdulrahaman sukazo k’asar, tabbas sunji Dadi sosai ganin Sauban yasami lafiya Wanda yake zaune Akan kujera ana fira dashi.”
Anan sarki Abdulrahaman Ya kalli maimartaba tare da Abdullah da Hajjah ya Fara da cewa “ku ga farce ranka ya dad’e Ina neman wata Alfarma a wurinka Allah yasa zaka Amince da hakan, ranka ya dad’e Ina neman Alfarmar a bar Sauban k’asar Nan wurin gimbiya bilkisu domin taci gaba da kula dashi har lokacin da zai kuma samin lafiya,
Snn idan ya warke Ina neman Alfarma akan a barshi a hannunta yayi karatunsa anan har zuwa lokacin da ya mallaki hankalin kansa yasan abinda Yake Masa ciwo lokacin da zai fahimci makiyi da masoyi snn sai yakoma gida Nigeria,
diba da yanda ake farautar rayuwarsa makiyansa k’ok’ari sukeyi ta ko wacce hanya so sukeyi sai sunga bayansa.”
Shuru kowa yayi yarasa amsar da zaibawa sarki Abdulrahaman domin shawarar da yanke tayiwa kowa dad’i a wurin sai murmushi ko wannesu yake saukewa.”
Snn Sarkin yayi gyaran murya Fara magana kamar hakan “hak’ik’a Abdulrahaman kayi matuk’ar tunani tare da hangen nesa muna godiya da wnn karamci naka Allah yabar tare ya raya maka zuri’a.”
Hakan Hajjah itama tayi Masa Addu’oe godiya tare da sanya Albarka,
Murmushin kawai Abdullah yakeyi cike da farin ciki domin yarasa abinda zaiwa Aminin nasa, iya k’auna sarkin Abdulrahaman ya nuna Masa ita da karamci, mik’ewa yayi tsaye fuskarsa tana saukar da murmushi yanufi inda Abdulrahaman yake zaune Abdullah ya rungume shi Yana Masa godiya, Yana fad’in ” nagode Aminina yanda kayi mun Allah yabani abinda zanyi maka fiye da hakan hak’ik’a Kai abokine Kuma Aminine na kwarai.”
Yinin ranar kowa cike yake da farin ciki,
Sai da sukayi sati d’aya a lokacin sauban ya Kuma Samun lafiya sosai har an sallamoshi daga asibity sundawo gida,
snn suka tattara kayansu har da hajjah suka dawo gida Nigeria suka bar Sauban a England wnn shine dalilin Zaman Sauban a k’asar England karatu.”
muje zuwa my friend’s⛹????♀
Bakaramin bak’in ciki da damuwa Jamila tashiga cikinsaba jin Sauban yasamu lafiya sosai k’arin Jin dad’i har da barinsa akayi a can domin yayi karatu,
Wato ana nufin bama a kasar Nan zaiyi karatuba kenan,
So akeyi yafi kowa karatu a gidan kenan?”
Tacije Baki taji wani irin tsanar Sauban tare da Hajjah ya dirar mata a zuciya domin tasan wnn duk shirrin Hajjah ne,
Domin ba Wanda Hajjah takeso takeso ganin ci gabansa kamar Sauban, ta rasa dalilin da yasa ta tsani nata yaran Sadeeq da Sageer,
wadan da ta fahimci ba Hajjah kawai ta tsanesu duk mutanen gidan basa sonsu ganin ido NE kawai da Kuma tana tsaye a kan yaranta.”
ta d’auki d’amarar indai tana da Rai da lafiya ko a can Sauban bazai tab’a samun abinda yakeso ba,
Indai kud’i suna aiki sauban bazai tab’a fitowa da sakamako Mai kyauba Sauban bazai tab’a Jin dad’in rayuwarsa ko bai mutuba sai Nigeria tayi Masa wahalar Shigowa sai ta Sanya anyi tir da alawaddan karatunsa.”
BaYan kwana biyu matan Abdullah suka haihuwa dukansu suka Sami ‘Ya’ya Mata,
Khadija ta haihu ranar Monday Aisha ta haihu ranar Friday.”
Murna a cikin masarautar abin ba’a magana,
Wanda Ina wuta Jamila tafad’a domin kwatakwata batasan ma suna d’auke da cikiba sai dai kwatsam taji haihuwarsu daga sama abinda yafi Kona Mata Rai Kenan.”
Jakadiya ta shiga dokawa Kira cikin sauri jakadiya tazo ta zube a gabanta,
Cikin d’aga murya tace “ya akayi wad’an can bayin banzan suka haihu a cikin gidan Nan?”
Dama suna dauke da ciki Baki fadamun ba?”
Ta d’aga murya cikin b’acin Rai ta Zaro Ido alamar komai tana iya aikatawa jakadiya tace fad’amun nawa suka Baki domin kib’oyemun cewa suna dauke da cikin Abdullah a cikin gidan Nan ban saniba.”
Sunkuyar da Kai jakadiya tayi cike da tsoro jikinta Yana rawa cikin girmamawa tace “ranki ya dad’e har Abada kud’i bazasu tab’a tasiri a gareniba har na Kai ga cin amanarki,
Yanda Kika San Baki San komai Dan gane da cikin jikinsuba sai dai kikaji haihuwa daga sama, Nima hakan ne a gareni ban San komai ba akai kiyi hakuri ranki ya dad’e Allah ya huci zuciyarki,
Amma Kuma ranki ya dad’e meye abin daga hankali da haihuwarsu Bayan dukansu Mata suka haifa ba maxa ba,
Koda maza ne suka haifa Sadeeq da Sageer sune a gaban ‘ya’yansu nesa ba kusaba nayi imani d’aya daga cikinsu shi zaiyi mulkin masarautar Adamawa.”
Wani murmushi Jamila tasaki najin dad’in ance d’anta zaiyi mulki,
Ta dubi jakadiya tace “tashi kitafi naji kin wanke mun DUK wata damuwata,
Kece da shegen kwadayin tsiya nasan za’a iya sayenki da kud’i Wanda idan na fahimci hakan sanyawa zanyi a saremun kanki kinsan ba tausayi ne daniba komai zan iya aikatawa, don hakan Dole ne na zargekeki kibi a sannu domin na tsane cin Amana”
Tuba nakeyi ranki ya dad’e nafi kowa sanin halinki insha Allah hakan bazai tab’a faruwa ba,
ki huta lafiya jakadiya tamik’e ta fita a ranta tana tsinewa Jamila akan tuhumar da tayi Mata bada laifintaba”
Anyi shagalin suna a gidan sarautar Wanda Jamila ta bada tata gudunmawa sosai komai da ita akayi sosai take nuna k’auna ga matan Abdullah tare da jaririansu,
Sai dai ta ciki na ciki bak’in ciki ne fal a ranta musamman yanda taga Hajjah tana farin ciki da haihuwar Wanda Sam bataga irin wnn farin cikin a fuskarka taba a lokacin da ta haifi su Sadeeq,
Hakan shima Abdullah sai murmushi yakeyi Yana farin ciki daga ganinsa kasan Yana tare farin ciki, hakan dai akayi taron suna aka watse yara suka ci sunan fateema Bintu wato sunan mahaifiyar Sauban kenan wacce Abdullah bazai tab’a mantawa da ita ba,
d’ayan Kuma taci sunan Hajaru wato sunan Hajjah Kenan, sarki yace Kuma Sam bai yarda da a canza basu suna ba a hakan za’adin kiran sunansu.”
Hakan yayiwa duk wani mutum dake cikin masarautar Dadi Amma Banda Jamila da mak’arabanta.”
Sauban ya Fara zuwa makaranta secondry school inda ya Fara daga jss1 kasancewar karatun can ba d’aya bane da karatun Nigeria,
Sosai Yake hazaka da k’ok’ari har malaman makarantar sun Fara Alfahari dashi Akan karatunsa,
Hakan gimbiya bilkisu tana kula da karatunsa tare da addininsa sosai da Kuma tarbiyansa.”
BaYan wata uku da bikin ‘ya’yan Abdullah,
Sarki ya kwanta ciwo Wanda har asibity ya kwanta yasamu lafiya ya dawo gida,
Tin daga lokacin lafiya ta Kiya Masa yau ciwo gobe lafiya,
Wata safiyar juma’a aka waye gari sarki yace ga garinku Nan.”
Mutuwar sarki ta girgiza Al’ummar garinsa dama wajen garin Baki d’aya domin duk Wanda yasan sarki Abdulsalam sarkin dake mulkin masarautar Adamawa yasan sarki ne Mai Adalci da sanin ya kamata sai dai duk da hakan mutuwa Bata barin wani Dan wani.”