DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Abdullah yashiga cikin tashin hankalin mutuwar mahaifinsa hakan Hajjah wacce takasayin magana sai girgiza Kai kawai takeyi,
hakan akayi Masa wanka akayi Masa sitira aka kaishi gidansa na gaskiya.”
Mutune k’asa k’asa jahohi sarakuna da shuwa gabannin k’asa duk sun zo wurin ta aziyar mutuwar sarki Abdulsalam,
BaYan wata biyu da mutuwar sarki aka yanke hukuncin nad’a magajin sarki wato Abdullah.”
Murna a wurin Jamila abun ba’a magana domin idan kowa Yana bakin cikin mutuwar sarki ita farin ciki takeyi sabida mijinta zai maye gurbinsa ya Zama sarki Dole a kirata da Sarauniya Kuma fulanin sarki,
Dole Hajjah taja baya tayi kallo don Dole sarautar gida ta dawo a hannunta don itace matar sarki a yanzun.”
D’aya ga watan match aka nad’aga sarki Abdullah a kan kujerar mulkin Adamawa hakan itama Jamila aka d’agata a matsayin Sarauniya Kuma fulanin sarki domin ta Hana a Bawa kowa sarautar fulani, tin daga lokacin sunanta ya tashi daga gimbiya Jamila ya koma Fulani ko Kuma kuce Sarauniya.
Duk wani ragamar cikin gidan sarautar itace take gudanar da komai, batare da tayi shawara da kowa ba,
Hakan sauran matan sarki Abdullah basa da abin cewa saboda dukansu ta kaisu wurin boka an d’aure Mata bakinsu sai yanda tayi dasu a cikin gidan.”
Duk abinda takeyi Hajjah tana sane da ita sai dai takawo nagani ta zuba Mata domin tasan komai lokaci ne garesa wata Rana sai labari,
Hakan zata Kira sauran matan Abdullah ta dinga yimasu nasiha tare da basu hakurin akan abinda suke gani Jamila tana aiwatarwa a gidan komai Yana da lokacin sa.”
Basa nuna damuwarsu Akan ta saboda mijinsu bai wulakantasu bai bai nuna kyamata a garesu ba hasalima yafi samun natsuwa a tare dasu to meye abin daga hankali a ciki?”
Sunsani Sarai harda shima Abdullah Bata barshi a banza ba Dan hkn yke biye Mata ga duk abinda takeso amma ai komai Yana da lokacin sa Mai hakuri bazai tab’a tab’ewaba.”
A kwana a tashi ba wuya har Sauban ya kammala karatun sa na secondary ya Fara zuwa jami’a mataki na farko
a lokacin yana da shekara goma Sha tara
Ya girma duk wani kyau nasa ya bayyana, dama Sauban kyakkyawa ne, snn mutum ne ba mai yawan son magana ba tin Yana k’aramunsa bare yanzun,
snn baya son a damesa da yawan magana,
Dan hakan baya da wani aboki sai safwan Wanda d’an abokin Abbansa ne da aka turosa karatu a Nan England
Sosai tasu tazo d’aya da Safwan saboda safwan Yana da son karatu sosai kusan duk ra’ayinsu yaxo d’aya, sai dai shi safwan da zarar anyi hutu yake komawa gida Nigeria sab’anin Sauban da yake Zaune a k’asar gaba d’aya,
Waje d’aya ra’ayinsu ya banbanta da sauban,
Shine safwan akwai shi da son hirar ‘yan Mata abinda Sauban ya tsana kenan , snn safwan Yana da yawan surutu da barkwanci da son ya shiga abinda da bai shafesaba abinda Sauban ya tsafi tsana kenan a rayuwarsa, dan hakan wani lokacin yakeji haushin safwan idan suka hadu a makaranta.”
A lokacin da Sauban Yake da shekara goma Sha Tara a lokacin Saudat take da shekara Tara a duniya,
Saudat yarinya ce Yar gata sangartaccciya wacce uwarta da ubanta suke sonta, tare da sakanta ta,
Basa son ganin kukanta bare b’acin ranta,
A duniya duk abinda Saudat take buk’ata batare da b’ata lokaci ba ake Mata shi. Wnn dalilin yasa Bata ganin girman kowa musamman bayinta masu kula da ita maza da mata duk Wanda ya Mata ba dai dai zata d’aga hannu ta wanke sa da mari ko a gaban mahaifiyarta Bata ce Mata komai sai majinjina da zata kumayi Mata na burgewa “
Wnn halayan nata na sangarta da rashin ganin darajar mutum tin tana karamarta,
yasaka gaba d’aya yarinyar Bata burge Sauban,
Kwata kwata Bata bashi sha’awa,
Ita kuma Saudat tana tsananin son Sauban domin ko abinci aka kammala Bata ci sai har lokacin da Sauban yadawo a duk inda ya tafi snn zataje ta d’auko takawo Masa a d’akinsa su zauna suci a tare, ba Dan ransa Yana soba sai Dan gudun kada iyayenta suga kamar Yana tsanar yarsu”, Bayan sunyi Masa halacci a rayuwa
Amma shi a zuciyarsa har ga Allah ya tsane yarinyar ba Kuma yarinyar ya tsanaba sangartar ta da halayenta ya tsana,
Bayaso kwata kwata tana shigo Masa d’aki tana fad’awa a kan jikinsa,
Wanda ya lura ko a gaban idon mahaifiyarta ta fad’a a kan jikinsa Bata yimata magana illah ta dinga murmushi tana d’aukar hakan ba komai bane.”
Saudat tana aji hud’u a primary,
Abinda Sauban ya lura dashi shine ko a makarantar tasu Wasa da maza ba komai bane a gareta, gaba d’aya Bata mu’amala da Mata ‘Yan uwanta Abokananta sune maza.”
Akwai wani lokaci da yaje d’auko ta a makaranta kasancewar shi yake Kai ta idan zaitafi makaranta Yake ajiyeta idan Kuma ya dawo yakan tsaya ya daukota su dawo a tare, lokacin da yaje daukota ya tarar da ita zaune Akan k’afar wani malaminsu bature jar fata sai shafata yakeyi tana dariya.”
Cikin b’acin Rai ya fincikota daga jikinsa ya kifa Mata Mari sosai yayiwa baturen rashin mutumci snn yasakata a mota suka nufo gida.”
Duk a tunaninsa zata fadawa mahaifiyarta
Domin ya shirya abinda zai fadawa gimbiya bilkisu Wanda sanadin hakan yafison ya bar gidan gaba d’aya dama Zaman gida yafice Masa a Rai sam.”
Amma Sam Saudat Bata fad’a mataba,
Illah tin daga lokacin tashiga Jin tsoron Sauban duk wani abin idan tanayinsa Bata barin sauban yagani, saboda a duniya ba Wanda ya tab’a dukanta sai Sauban Dan hakan take tsananin jin tsoronsa.”
Wasa Wasa Saudat sai girma take k’arawa Wanda har ta kammala primary school tashiga jss1,
A lokacin tafara sanin ko ita wacece ko ita ‘yar wacece,
Tafarajin kanta Yana Mata girma, dan ta Kira bayinta ta wulakantasu ba wani abin bane gareta, domin mahaifiyarta tana nuna Mata k’askantune a wurinta ta wulakantasu yanda ranta yakeso snn tayi mulkinta yanda takeso ita kad’ai CE wurin mahaifinta Kuma sabida da ita suke zaune a k’asar England.”
Wnn dalilin yasa Saudat ta tashi da girman Kai da nuna Isa da mulki Wanda a duniya ba Wanda take tsoro sai Sauban.”
Lura da tana D’an Jin tsoron Sauban yasa wata Rana Mahaifiyarta takirata tashiga fad’a Mata cewa ta dainajin tsoron Sauban idan ta ganshi ta daina firgita tana fasa abinda tayi niya, tasani ba wani dangata dake tsananinsu asalima taimakonsa sukayi suka tsiratar da rayuwarsa daga mutuwa.”
Shuru Saudat tayi batayiwa Mahaifiyar tata maganaba sai da d’auki Yan mintina snn ta dubi mahaifiyar tata tace “mommy Ina son Sauban shine mijina Zaki aura mun shi?” Ina sonshi a duk yanda Yake
Tas taji Mari a kuncinta gimbiya bilkisu tana Mata wani kallo, cikin daga murya tace “nawa kike mekikasani a duniya dangane da aure shekararki nawa 13 kike zan cen aure,
To bara kiji Koda kin Isa aure bazan tab’a aura maki Sauban ba saboda Baku daceba gaba d’aya baya cikin tsarin maxan da nakeso ki aura,
Kisani ke kad’ai muka haifa a duniya mahaifinki sarki ne, Dan hakan Ina da burin ki auri namiji Wanda yayi fice a duniya Wanda sunan sa yayi fice kowa yasanshi a duniya ba kamar Sauban ba, kada na Kuma jin wnn maganar a bakinki, ta janyota tana lallashinta sakamakon Marin da tayi Mata.”
Duk abinda gimbiya bilkisu take fad’a a kunnen Sauban a lokacin ya tinkaro d’akin nata domin ya gaida ita, karaf a kunnensa yaji tana fad’in hakan ya girgiza Kai yafita shima a zuciyarsa Yana fad’in mezaiyi da ita Koda Mata sun Kare a duniya bazai tab’a auren Saudat ba.”