DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
Wani abin d’aure Kai dake faruwa a makarantarsu Sauban shine yanzun shekara biyu kenan duk akayi jarabawa bayaci faduwa yakeyi duk su safwan sun wucesa,
Bayan yasan duk a ciki d’aliban makarantar ba wani Wanda zai d’aga hannu ya ce yafishi k’ok’ari, indai a wurin karatune Sauban shine sahun farko, Amma abin mamaki da zarar an like suna ba wani ci gaba da Yake gani a tare dashi shekara biyu kenan Yana maimaita shekara duk wani mate nashi ya wuce shi a karatu.”
REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S✍
???? D’AN SARKI SAUBAN????
Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)
Page 13
Abin Yana damun sarki Abdullah a kan rashin ci gaban karatun sauban, kullum Yana Nan a yanda yake.”
Hakan yayi tattaki yaje da kansa k’asar batare da kowa yasaniba domin yayi bincike Akan abinda Yake faruwa,
Kai tsaye makarantar ya sauka a ofishin shugaban makaranta.”
Bayan sun gaisa tin kafin sarki Abdullah yayi magana ya fad’i abinda ya kawoshi shugaban makaranta ya Fara da cewa
“ranka ya dad’e dama ko da bakazoba mun yanke shawarar zamu aika maka da sak’o ta hanyar wayarka domin musanar dakai abinda Yake faruwa koda Kai zaka d’auki wani mataki a kan yaronka,sauban
Sabida munfad’awa mahaifiyarsa wacce suke tare a Nan duk abinda Yake faruwa akan karatun nasa ba wani mataki da ta d’auka har yanzun, domin mun yanke hukuncin da zarar mun fad’a maka baka kaima baka d’auki wani matakiba to tabbas kararsa zamuyi a makarantar nan”
Wato yaronka Sauban nasara dalilin da yasa yafi ko wanne d’alibi fad’uwa a makarantar Nan
Na Tara duka malamai nayi bincike akansa domin naji dalilin fad’uwar nasa,
Amsa d’aya ce baya karatu.”
Dan hakan muka yanke hukuncin zamu kiraka mufada maka, idan wata makaranta zaka canxa Masa hanya a bud’e take mu munfi son hakan.”
Shuru sarki Abdullah yayi snn yabude Baki yace “abinda yakawoni k’asar Nan kenan don nayi bincike saboda nima abin Yana damuna matuk’a,
Amma maganar Nan da kayimun na yanke shawarar fitar dashi daga wnn makarantar zan canza Masa wata, ya mik’e tsaye tare da mik’awa shugaban makarantar hannu yace “godiya nakeyi sai anjima yafita.”
Kai tsaye gidan Aminin nasa yanufa inda Sauban Yake da Zama,
Bazata Sarauniya bilkisu taga zuwan sarki Abdullah, inda ta nuna mamakinta a fili.”
Bayan sun gaisa cike da girmamawa snn tasaka bayinta aka kawo Masa abinci tare da kayan motsa baki, sai da ya kammala cin komai snn ta Kuma dawowa cike da izzah da Isa suka Kuma gaisawa.”
Daga Nan Yake fadamata abinda ya kawoshi k’asar Akan karatun Sauban.”
Sosai Sarauniya bilkisu taji kunya domin ansanar da ita hakan a makarantar shap mantawa tayi Bata d’auki wani mataki akai ba.”
Lura da hakan da maimartaba yayi yasa ya kawar da zancen akan cewa ‘ina shi Sauban din Yake Yana son ganin sa, yanaso suyi magana idan da akwai makarantar da yakeso ya fad’a, ayi komai daga you zuwa gobe,
Domin gobe yakeso ya koma.”
Mik’ewa tayi jiki a sanyaye tanufi b’angaren Sauban domin ta kirashi, anan ta gamu da wani bafade Yana shawagi Wanda shi aikinsa kenan a cikin gidan,
Takirashi tace yatafi d’akin Sauban yace yazo mahaifinsa sarkin Adamawa Yazo yana kiransa”
Sauban Yana Yana kwance rigingine akan gadonsa Yana tunanin abubuwan da sukayita faruwa dashi tin Yana yaronsa har zuwa yanzun,
Yanaso yaje k’asarsa ta haihuwa Amma saboda ana farautar rayuwarsa yasa baya sha’awar zuwa,
Snn anan ma ba’a barsaba an hanashi yin karatunsa cikin kwanciya hankali sai shige da fice ake Masa Akan karantunsa Wanda yasan duk abinda Yake faruwa daga masarautar gidansu Yake fitowa Dan kuwa shekaranjiya Yana makaranta a zaune yaga waziri,
yafito daga ofishin shugaban makaranta yayo Masa rakiya suna dariya fuskokinsu cike da farin ciki.” Meya tare masune dabasa son ganin farin cikinsa, shifa haihuwarsu akayi bashine ya haifi kansaba laifin me ya masu, tabbas lokaci Yana zuwa da zai dakatar da duk wani mugun abunda suke nufi akansa.”
K’arar kwankwasar k’ofar d’akinsa ya ankarar dashi daga duniyar tunanin da Yafad’a
Jikin ba kwari ya mik’e yaje ya bud’e k’ofar Yana kallon waye?””
Bafade yagani yayi saurin durkushewa gabansa Yana fad’in ranka ya dad’e maimartaba sarkin Adamawa yanason magana dakai.”
Murmushi yasaki na farin cikin jin mahaifinsa yazo, ya d’agawa bafaden hannu had’ida d’aga Kai alamar gashi Nan zuwa.”
Komawa yayi yasaka manyan kayansa harda hula sab’anin k’ananun Kaya dake jikinsa gudun kada sarki yayi Masa fad’a akan saka k’ananun Kaya kamar yanda yake Masa a duk lokacin da ya gansa da su.”
A gaban mahaifinsa yake Durkushe Bayan ya gaidashi cike da girmamawa,
Murmushi kawai sarki yakeyi Yana kallon d’ansa mafi soyuwa a ransa tare da tausayinsa.”
Anan sarki yashiga fad’a masa abinda ya kawo shi, tare da yi Masa fad’a Akan ya dinga tsayawa Yana karatu ya daina Sanya Wasa a karatunsa ya d’iba yagani duk wad’anda suke karatu a tare duk sun wuce sa suna gabansa.”
Sunkuyar da Kai Sauban yayi sai da Abban nasa ya gama yimasa fad’a yayi shuru.”
snn sauban ya d’aga Kai ya kallesa cike da girmamawa ya d’an sunkuya yace Abba kayi hakuri insha Allah bazan sake ba.”
Washe gari sarki Abdullah bebar k’asarba sai da ya kammala yiwa sauban komai na dangane da karatunsa ya canza Masa wata makarantar da duk wani abin da yasan Yana buk’ata snn ya yaje yayiwa sarauniya bilkisu sallama tare da godiya yashiga jirgi yanufi k’asar sa NIGERIA”
Sosai safwan yayi bakin cikin canjin makaranta da akayiwa Aminin nasa wani b’angare , idan ya Tina da dalilin yin hakan yakanji Dadi a ransa, domin yawan fad’uwar Sauban a makaranta shima abin Yana damunsa Wanda iya bincike sunyi bincike sun rasa sanin dalili,
Sai dai duk da hakan amintansu tana Nan domin da zarar antashi daga makaranta safwan Yana wurin sauban duk dai da dai shi ke biyarsa Sauban ko ajikinsa domin wani irin miskiline Wanda baka Gane gabansa bare bayansa snn mutum ne ba Mai son yawan magana ba, snn duk abinda Yake damunsa bazaka tab’a ganewaba bare ganin b’acin rai a fuskarsa. sai dai ya bar komai a ransa.”
Hirar safwan da Sauban itace a kullum safwan baya da wata Hira idan suka hadu sai ta Aure a rayuwar safwan shi dai ya Matsu lokaci yazo yayi aure,
domin shi kad’ai yasan yanayin da Yake shiga a duk lokacin da yayi Ido biyu da Jajayen fata masu yawo tsirara.”
Harara kawai Sauban Yake watsa Masa tare da jamasa dogon tsaki batare da ya tanka Masaba.”
safwan zai waiga ya kallesa ya mere Baki yaci gaba da maganarsa domin ba zai fasa gayamasa abinda ke ransa ba akan aure.”
Wani lokacin Kuma idan yanason tsokanar Sauban Dan yayi magana ya biye Masa, sai dinga cemasa dama irinku marasa maganar Nan idan Kika Sami macce sai kunyi kamar bazaku barta da Raina Akan jaraba, har gwara mu muna fitar da abinda ke cikin ranmu.”
To a lokaci Sauban sai Kuma Jan dogon tsaki tare da wurga Masa da kallon baka da hankali.”
Hakan rayuwa taci gaba da tafiya,
Wanda canjin makarantar da akayiwa sauban ya Fara ganin haske a karatun nasa,
Shima safwan ya kammala karatun NCE nasa
Ya dawo a makarantar su Sauban ya jona dgree d’insa, suka Kuma had’ewa wuri d’aya.”
Akwana a tashi ba wuya Saudat ta kusan kammala secondary school yanzun tana aji shidda a secondry
duk wata cika da halittar jikinta na matsayinta na cikakakkiyar macce duk ta bayyana,
Ba laifi Saudat kyakkyawa ce Dan duk inda ‘ya macce zata d’aga hannun ta nuna ita kyakkyawace Saudat zata d’aga nata,
Sai dai rayuwar turai da ta ratsata zuciyarta,
Gaba d’aya ta zubar da Al’adarta ta jinin saurata ta d’auko rayuwar turawa ta d’orawa kanta, Wanda da zarar kikaga Saudat idan bakin santaba bakya tab’a cewa ta had’a wata alak’a da musulmi, musamman yanayin shigarta da yanda take ma’amala da maza,
Hakan bai saka Sarauniya bilkisu taga kuskurentaba bare ta tsawata Mata,
Bare Sauban Wanda da abinda ya damesa yanuna zai dinga tsawata Mata bilkisu ta dakatar dashi tana fad’in ya barta tayi abinda ranta yakeso kada ya takurata tinda shi ba Wanda ya saka Masa Ido bare ya takurashi a kan duk abinda zaiyi.”