BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Turo k’ofa akayi cikin isa da k’asaita ba tare da anyi sallama ba aka shigo,

K’amshin turarenta ya tabbatar masa da wacce tashigo, masa d’aki a dai dai wnn lokacin,
Ransa yab’aci matuk’a da rashin yin sallamarta, wato har yanzun saudat tana nan da halinta bata sauyawa ba,
shi har ga Allah ya manta da yana da wata mata a rayuwarsa.” Saboda Sam ya tsani halin saudat da duk wani mai hali irin nata,
Ci gaba yayi da abinda yakeyi yayi kamar bai san tashigo d’akinba. “

Tsaye tayi wuri d’aya ta hard’e hannayenta a k’irji tana k’are masa kallo sama da k’asa cike da burgewa tare da sha’awa mai cike da so da k’aunar gwarzon mijin nata, amma isa da mulki tare da girman kai da takeji yana mata yawo ya hanata zuwa ta tunkareshi domin tayi masa sannu da zuwa tanajiran sai ya farayimata magana snn.”

Jallabiyarsa ya d’auka ruwan madara yasaka tare da fesawa jikinsa turarensa mai dad’in k’amshi ya d’auki wata kyakkyawar leda wacce ya ajiye wuri d’aya da alama wani muhimmin abune ke cikinta ya zura talkaminsa ya rab’a ta gefenta zai fita. “

Gabansa ta sha tana kallonsa tana murmushi cikin k’asaita take fad’in haba sadaukina sai kace baka ganniba, bayan kasan wurinka nazo, kaddai ace har yanxun halinka yana nan baka canzaba,
Ko ka manta da cewa ni matarkace ta sunnah wacce katafi kabarni shekara d’aya KO waya baka mun bayan kasan Ina sonka Ina cike da kewarka.”

Kallo d’aya ya mata ya kuma tanke fuska ba alamar wasa a tare dashi ya sanya kai yayi ficewarsa ya nufi fada wurin maimartaba. “

Sarkin gida a gaban fulani a durk’ushe yana kwasar gaisuwa, “Ranki ya dade Allah ya k’ara maki lafiya da nisan kwana, sarauniya a wurin sarki gimbiya a wurin sarki kece mai mulkin masarauta daga sarki saike wani Albishir naxo maki dashi “d’anki yarima Sauban ya sauka lafiya yanzun hakan yana cikin masarauta yana hutawa. “

Gaban fulani ya fad’i tayi saurin mik’ewa daga kishin kid’en da take zuwa zaune, a nan take ta had’e fuska,
Ta juya ta kalli sarki gida cikin k’asaita tace “bani labarin yanda ka gansa “

Sarkin gida ya saki murmushi ya kuma gyara zama yace “ranki ya dade yarima ya k’ara fari ya k’ara k’iba da cikar kamala dakin gansa kinsan yana cikin kwanciyar hankali da walwala. “

Tsawa ta daka masa tace “yimun shuru bashi na tambayeka ba,
Tanuna masa hanyar waje tace tashi kafita. “

Jiki na rawa sarkin gida yafita yana mamakin fulani KO dai akwai wani abin da yake faruwa ne da ita? . “

Cikin fushi da bak’in cikin abinda yarima ya Mata tashiga b’angarenta, ta zauna akan kujerarta ta mulki,
A nan take bayinta suka zagayeta KO wacce tashiga yimata hidima, a can mai kula da kayan marmarinta tashigo d’auke da tire na kankana tare da Apple ta durk’usa k’asa ta ajiye a gabanta ta yanko kankana tare da sunkuyawa tabata tace “ranki ya dade gata kisha idan kina da buk’ata. “

Wani irin wawan kallo ta wurga mata ai bata bari ta sauke hannunta ba ta d’auke mata fuska da Mari tare da kifa Mata tiren kankanar a jikinta, tana fad’in tashi kifita Dan ubanki na fad’amki Ina bukata ne?”

Mik’ewa tayi jiki ba kwari tashiga tsince duk kankanar da ta zube, tafita tana sharar hawaye tare da tsinewa hali irin na gimbiya saudat matar d’an sarki Sauban ‘ya ga sarki Abdul’rahaman sarkin Bauchi
Amini ga sarki Abdullah mahaifin sauban sarkin da ke mulkin Adamawa. “

labarina k’irkirana nayi mallakina ne idan kikaji yayi dai dai danaki to akasi aka samu

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? **????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer

Page 3

Wai meyasa kukeyimun hakan ne, wasu da yawa suna Bina prv akan sunaso suyi rigester wnn littafin, bayan nariga da tun farko nafad’a maku cewa wnn book din bana sayarwa bane kyauta ne barka da sallah ne ga duk wasu masoyana masu bibiyar labaraina, pls Dan Allah ku daina Bina prv kunacemun kunaso kuyi rigester, ku kwantar da hankalinku tunda na lura da kud’in hannunku k’aik’ayi suke maku zanyi maku littafi na kud’i Amma ba wnn ba, wnn kyauta ne fatana kubani had’in Kai wurin yimun comment domin na fahimci sak’ona Yana zuwa yanda nakeso ngd????????????????????????

* Runsunawa yayi cike da girmamawa da biyayya yace “nagode Ranka ya dad’e insha Allah zan kiyaye duk abinda ka umurceni dashi.”

Murmushi sarki yasaki Yana kallon d’an nasa Wanda yafi soyuwa a cikin ransa, ya girgiza kai, tare da furta Allah yayiwa rayuwarka Albarka Sauban.”

“Ameen Sauban yace snn yafita daga fadar ya nufi b’angaren Fulani.”

A kishingid’e ya tarar da ita akan kilishinta tayi matashin Kai da titimi Mai adon gaske, tana ganin shigowar Sauban tasaki wani irin murmushi sai da ta d’auki minti biyar snn ta tashi zaune cike da yanga da k’asaita ta dubi sauban tana jiran ya Kai durk’ushe a gabanta ya kwashi gaisuwa kamar yanda ake mata,
sai ganinsa tayi yaja wuri d’aya ya zauna tare da tsureta da Ido kamar Wanda yake karantar wani abin a tare da ita.

Bak’in ciki da takaici suka rufeta, wato Yana nufin ita zata Fara yimasa magana kenan a matsayinta na sarauniya, to Yake ta gaidashi ko meye Yake nufi, ta lura da yanda Yake wani ji da kansa da nuna Isa da mulki kamar shine sarki gaba d’aya,
ta K’ara kallonsa a karo na biyu wnn karon Ido cikin Ido sukayi dashi suna kallon juna ko wannensu da irin kallon da Yake jifar d’an uwansa,
a Nan take taga y Kara yimata wani kwarjini,
Cikin ranta tace tsinanne kawai Mai halin uwarsa, saurin kawar da bintu nayi Amma bintu Bata mutuba domin tabarmun dafinta Wanda yafita fitina,
Ta Kuma kallonsa na karo na uku tace a ranta ai nasan idan zamu kwana a Nan bazaiyi mun maganaba idan bani nayi Masa ba,
Cikin dakiya da k’arfin Hali tace “barka da zuwa yarima, da fatan ka sauka lfy.”

“Lafiya k’alau yace a tak’aice, snn yace “Banga sadeeg da Sageer ba.
Yi tayi kamar bataji abinda yace ba, a ranta tana fad’in d’an rainin wayo ko kagansu me zakayi masu bayan ka k’ara Tula masu haushi a ransu,
Yasan taji abinda yace yasa bai Kuma yin maganaba illah yaciro wayarsa domin ya diba Miss call din da akayi Masa a lokacin da Yake fada a gaban mahaifinsa,
Ganin sunan babban Amininsa Kuma abokinsa Wanda suyi fad’a suyi dad’i wato SAFWAN, murmushi yasaki domin yasan bai fad’a Masa cewar ya dawo Nigeria ba, Kuma tinda ya kwada Kiran numbersa ta Nigeria yaga yasamu yau zai Sha mita da surutu kenan Wata k’ila har kansa sai yasaka yayi Masa ciwo.”

Wayarsa ya mayar a Aljihu Yana k’ok’arin tashi tsaye sai gani yayi an zagaye shi da kayan abinci iri iri, kallo yabi abincin dashi, bai fasa yunkurin mikewa tsayenba,
Ya kalli fulani yace “gimbiya ki huta lafiya yanufi hanyar waje.”

Cikin d’aga murya Mai sauti Wanda batasan tana da itaba, takira sunansa tace “Sauban baka ganin an ajiye maka abinci ne?
ai yakamata ko lemu ne ka tsaya kasha idan baka buk’atar komai.”

Shuru yyi na d’an minti biyu yana nazarinta snn ya bud’a Baki yace “bana buk’atar cin komai a halin yanzun domin lokacin cin abincina baiyi ba,
Snn Koda lokaci yayi nasan Saudat ta tanadar mun duk wani abinda nake buk’ata ki huta lafiya tare da ficewarsa ya nufi b’angaren sa Yana murmushinsa na gefen baki”

Cije Baki tayi ta mik’e tsaye cike da takaicin asarar da ya janyo mata cikin d’aga murya tashiga Kiran jakadiya cikin sauri jakadiya tafito daga cikin wani d’akin takai durk’ushe a gabanta tana fad’in “gani ya uwargijyata,
Fulani tace “jakadiya ya b’arar Mana da komai ya ruguzamana duk wani shiri namu, baici abincin ba yanzun meye mafita?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button