BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Satin daddy Daya a England bai Sanya sauban a idonsa ba, Wanda Sauban ya d’auki Alkawarin yabar gidansu Saudat kenan har Abada bazai Kuma Zama a cikinsaba,
Hotel ya kama sannu a hankali duk ya kwashe kayansa a gidan ya mayar hotel a kusa da d’akin safwan yaci gaba da karatunsa”

Da zarar daddy yakira wayarsa a kullum cemasa yakeyi Yana makaranta jarabawa sukeyi shiyasa har yanzun basu samu ganin junaba.”

Hakan sarki Abdulrahaman da sarki Abdullah suka yanke ranar auren Sauban da Saudat wata shidda masu zuwa,
Murna da farin ciki kamar ya kashe Saudat inda bilkisu takejin wani bakin ciki a cikin ranta Akan auren.”

Duk abin Nan da akeyi Sauban bai San abinda yake faruwa ba,
Hankalin sa a kwance, domin barin gidan yayi yafi samun Kwanciyar hankali Akan Yana cikinsa,

A d’akin Safwan Yake akwance safwan Yana shirya kayansa a kwati domin gobe zai koma gida Nigeria gaba Daya sakamakon ya kammala karatunsa,
Inda Sauban yake kwance rufe da Ido domin yasan sai yayi kewar abokin nasa,
Yana hakan wayarsa ta d’auki ringing dibawar da zaiyi yaga Abbansa NE.”

Dagawa yayi cike da biyayya,.ya gaida Abba ya amsa Masa,
Anan yake bashi umurni akan ya had’o kayansa Yabiyo safwan yadawo gida tinda sun Sami hutu idan hutu ya K’are sai ya koma makaranta akwai maganar da yakeso yayi dashi wacce batayi a waya sai gashi gashi, snn ko banza k’asarsa Nigeria tana kewarsa tare da a halinsa.”

Sosai sauban yaji dadin umurnin da Abba ya bashi Wanda dama irin wnn lokacin yake jira Wanda za’a bashi umurnin yadawo k’asarsa ta haihu.”

Tare da Safwan suka shiga had’a kayansa, washe gari sukabi jirgin karfe goma suka nufi Nigeria.”

Dan Zaman da daddy yayi na sati daya a England abinda bai tab’a yiba iyakacinsa yayi kwana Daya zuwa biyu ya kwana,
A Nan yaga yanda Saudat take gudanarwa da rayuwarta wurin yanayin shigarta da yanda gaba Daya rayuwarta ta turai ce take gudanar wa,

Anan take hankalinsa ya tashi yayi tir da irin wnn rayuwar,.
Kamarsa sarki, Mai mulkin kasar hausa k’asar Addinin musulci k’asar da musulmai sunfi kafirai yawa ace yarsa ta cikinsa wacce yafiso Akan komai take wnn shigar wacce da ita da tsirara batada wani maraba,
Wacce ya kamata a ce tana sanye da sitirarta da Alk’yabbarta ta lullub’e jikinta tana zuba mulki Amma ace itace take bayyanar da suffarta a gaban kafurai makiya ma’aiki ransa ya baci matuk’a,
Anan take yabada umurni su shirya gobe gobe zasu sabar k’asar Nan gaba dayansu Kuma su sani daga har Abada bazasu Kara zuwa turai su zauna ba sai dai su shigota su fita.”

Murna Saudat tayita domin itama tana son taje NIGERIA Wanda Sarauniya Bilkisu ta k’ara cika tare da Jin haushi”

Washe gari suka had a kayansu gaba daya tare da fadawa sukabar k’asar zuwa Nigeria.”


Biki aka shirya na musamman Dan tarbar Sauban, Wanda ya shekararsa goma Sha biyar kenan rabonsa da k’asarsa,
Sosai Hajjah take murna da jin dadi, hakan fulani Jamila itama ba laifi tanuna farin cikinta tare da matan sarki.”

Shigowar Sauban a cikin gidan komai dawo Masa sabo tin daga lokacin da yafito sashen Jamila a lokacin da tabashi abin Wanda sanadin cin abinci bai Kuma sanin inda kansa yakeba sai dai ya farka ya gansa a turai har zuwa gwagwarmayar rayuwar da yasha a cikin gidan, Yar kwallah ta ziraro Masa Ido yayi saurin Sanya hannu ya dauketa a lokaci da yayi Ido da Hajjah tana sakar Masa murmushi farin cikin ganinsa, da sauri yaje ya rungumeta Yana Mai cike da farin ciki hakan ya itama Anna tana farin cikin ganinsa.”

Anan aka gabatar da komai,
Masu farin cikin nayi masu bakin ciki Suma sunayi na ganin ci gaban da Sauban ya samu ya girma huta ya zauna a jikinsa kamaninsa da mahaifinsa da mahaifiyarsa sun bayyana a tare dashi, Ina Sadeeq yakejin want sabon bakin cikinsa Sageer Kuma sai murna yakeyi da dawowar Dan uwansa,
Hakan hajaru da Bintu kannensa wad’anda bai tab’a ganiba sai a waya suma suna farin cikin ganinsa.”

BaYan komai ya lafa, sarki yakirashi ya zaunar dashi Yafad’a Masa dalilin Kiran nasa da yayi So yakeyi yayi aure snn ya zab’ar Masa matar auren wacce yasan zai farin ciki da sanin ko wacece wato saudat.”

Gaban Sauban ya fad’i cike da firgici ya kalli mahaifin nasa,
Amma Dan gudun kada ya fahimci wani abin yayi saurin dakewa tare da sunkuyar da Kai baiyi maganaba, domin baya fatan Allah ya kawo lokacin da zaiyi musu da mahaifin nasa.”

Sosai ya amshi auren Saudat hannu biyu batare da yanuna alamar baya sontaba yasan hakan rayuwarsa zataci gaba da tafiya ba wani farin ciki a cikinta.”

Anan take maganar auren Sauban ta karad’e gidan sarautar cewar yarima Sauban zaiyi aure zai auri Saudat Yar sarkin Bauchi Amini ga sarki Abdullah.”

Ina wuta Jamila ta fad’a wato yarinya da ta kwallafawa Rai Akan Sadeeq ko Sageer dayansu ya aura sabida sarautar masarautarsu gata ita kad’aice a wurin mahaifinta shine aka Bawa Sauban ita,
Ta dafe Kai Wai meyasa duk abinda ta Sanya a gaba sai Sauban yayi Mata katanga dashi, wato ta kashe Bintu Ashe Bintu Bata mutuba kenan tabar baya da k’ura.”
Gata Bata isa ta tunkari gimbiya bilkisu akan maganar afasa auren ba domin tsakaninsu Kar ta San Karne domin duk abinda take tak’ama dashi gimbiya bilkisu ta shafeta.”

Hajjah tayi farin cikin wnn had’in auren domin tasan sarki Abdulrahaman Aminin Abdullah sannan Yana da karamci a idonta kodan taimakon da yayi masu a lokacin da lular ciwo tasame Sauban,

Zaman Saudat a cikin masarauta Tasha wahala sosai kafin tasaba da saka manyan Kaya tare da Alk’yabba, sai da tasaba snn aka shiga koya Mata yanda zata gudanar da mulkinta a matsayin da Gimbiya Yar sarki,
Anan take Saudat Taji girman Kai ya shigeta tare da jinin mulki dake yawo a jikinta, cikin wata biyu ta Fara taka duk Wanda takeso ta Kuma wulak’anta duk Wanda taga dama dama hakan sarautar masatautarsu take,
A b’angarenta har kujera gareta wacce take Zama ta sarauta wacce take zuba sarautarta Akai tare da mulkinta a yanda take so sai yanzun takejin kanta duk a can baya ba rayuwa takeyiba sai yanzun take rayuwa, b’angaren Mata Kuma ba Wai dainawa tayiba, sai ta kalli cikakkiyae kuyanga wacce taji komai da komai tasaka a gyara Mata su akai Mata d’akinta domin biyan buk’atarta.”

Komawar safwan gida ya shima ya tarar da mahaifinsa yasaka Ranar Aurensa wata uku masu zuwa,
Inda ya had’ashi da Yar k’anwar mahaifin nasa Mai suna SAFINA, wacce dama itace zabin safwan,
Wato Sai anyi bikin safwan kenan snn ayi na Sauban.”

Bayan bikin safwan inda an Sha shagalin biki na Dan gata komai anyi na k’awatar,
Tare da Sauban aka raki safwan gidan sa wurin Amaryarsa Wanda Sauban baiso zuwa sai da yaga b’acin ran safwan snn ya yarda akatafi kaishi dashi.”

Washe gari tin da safe sauban yakira safwan a waya lokacin Yana tare da Amaryarsa rungume a jikinsa Yana shaye Mata Albarkatun kirjinta, Kiran Sauban ya shigo wayar sa da kyar ya Mika hannu ya d’auka, a kasalance yak’ara wayar a kunnensa.”

Mere baki sauban yayi daji yanda safwan yake amsa Masa maganarsa,
Karon farko safwan yace “lafiya kuwa Sauban Kira hakan tin da safe ko kamanta ba’a England mukeba snn yanzun fa ni inada iyali ya Ina cikin wata duniya zaka dawo Dani cikin duniyarku fadamun me’akayi.”

Dogon tsaki yaja Sauban baiyi maganaba illah ya kashe wayar gaba d’aya Yana tinanin dama akwai duniyar da mutum zai shiga BaYan wacce yake cikinta.”
D’an iska kawai ai kasamu abinda kakeso saikafi Mai kura shafawa yacewa safwan sai kace Yana jikinsa????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button