DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
Washe gari Saudat ta shirya tare da bayinta suka rakata domin ta gaida mutanen gidan daga Nan ta zagaya gida wurin Hajjah ta Fara zuwa,
Hajjah tana ganinta tayi murmshi tare da yi Mata sannu da zuwa anan Hajjah tasamu damar k’arewa Saudat kallon sama da k’asa, anan taga tsantsan mulki a tare da ita tare da tsantsar soyayyyar mijinta a cikin idanunta,
Anan Hajjah taji dad’in ganin hakan ko ba komai jamila tasamu wacce zasu Kara da ita a cikin gidan nan,
Hajjah ta gyara Zama tashiga karantowa Saudat duk halinda mijinta Yake ciki Akan makiya domin zagaye Yake da makiya rayuwarsa tana cikin hatsari don ana amfani da abin Sha ko abinci ana cutar dashi Dan hakan in har tana buk’atar rayuwar mijinta sai ta tashi tsaye Akan mijinta.
Anan Hajjah tayi ta karantar da ita yanda zatayi tattalin mijinta Wanda tuni Saudat tasan da hakan domin yanda takejin Sauban ko baiwa ta Kama tana kallonsa sai ta fille Mata Kai Ko tayi mata hukunci mafi tsanani to bare har tabasu abinci sudafa su bashi yaci, to ita meye amfaninta.”
Godiya tayiwa Hajjah snn ta tashi ta shiga b’angaren duka matan sarki suka gaisa,
Har b’angare fulani jamila inda tabi Saudat da kallo cike da kyashi da hassada Dan ko kayan jikin Saudat abin kallo ne bare gwala gwalan dake sanye a jikinta,
A ya tsine take kallon Saudat wacce itama Saudat take Mata kallon Mai bisa ruwa.”
Kalmar da tafito a bakin fulani Jamila itace “ba girin girin ba tayi Mai Allah yasa ankawo budurci a gidan mijin Domin Banga farin gyalle Yana yawo a cikin gida ba kamar yanda Al’ada take.”
Kallon shekeke Saudat tayi Mata tace “ai Koda farin gyalle zaiyi yawo bazai tab’a Shigowa wnn bangarenba domin an kusan walkiya komai zai bayya Dan Ina sa ran shigowata cikin gidan sai na bayyak’o asirin kowa daga ciki harda masu yunkurin kashe farin cikin rayuwata,
Tana kaiwa Nan tayi ficewarta.”
Zufa tashiga karyewa Jamila me wnn yarinyar take nufi ne?”
Tana nufin tasan komai a kanta ne?”
Tana cikin tunanin hakan hankalinta a tashe taji wayarta ta d’auki ringing debawar da zatayi taga sunan Sarauniya Bilkisu wato Mahaifiyar Saudat kenan,
Cikin ran Jamila tashiga fadin Kiran me bilkisu takeyimun BaYan ta hanawa d’ana auren marar kunyar yarta, kafin wayar ta tsinke tayi saurin d’auka tare da karawa a kunnenta.”
Sautin muryar Sarauniya Bilkisu taji tana fad’in “Sarauniya Jamila matar sarki Abdullah Kuma fulanin sarki Abdullah maccen da take mulkin cikin gidan masarautar Adamawa,
Kira nayi domin na fad’a maki ‘yata tashigo cikin masarautarku,
Kada wani abun yasami ‘yata,
Tsakanina dake kin sanni na sanki Kar Tasan Kar ne,
Na rantse da Allah inda nashiga a cikin duniyar Nan Koda mafarki bazakiyi tinanin Zaki shiga wurin ba, nasan bakya buk’atar k’arin bayani Dan gane da koni wacce ce,
Dan hakan a kiyaye aso abinda ‘yata takeso koda mafarki kada ayi yunkurin cutar mun da ita Dan bazan tab’a yafewa Wanda yayi yunkurin yin hakan ba.”
D’if taji ankashe wayar.”
Mik’ewa tsaye tayi tana safa da Marwan me Sarauniya Bilkisu take nufi ne?”
Tabbas tasan bilkisu hatsa bibiyace, da duk wani abinda take tak’ama bilkisu ta shafeta, idan tana karama da mulkin miji bilkisu har gobe ita kadai ce a wurin mijinta. Bata da kishiya idan tana tak’ama da mulkin cikin gidan kujerar Saudat ta mulki ta cunawa kujerar ta,
Idan tana tak’ama da bokaye bilkisu tsafi takeyi tabawa bunki jini ya Sha.”
Tayi saurin kaiwa zaune ta d’ora hannu a hab’a???? tana tunanin Allah yasa ba’ajalinta bace Saudat aka kawo a cikin gidan nan”
Tin daga lokacin Jamila Koda Wasa Bata kallon Saudat da sunan jefa Mata habaici ko wata magana, inda Saudat take batabi ta wurin ta wuce snn mulki a cikin gida tanayi Saudat nayi ba Wanda ya Isa ya takura wani,
Dan mulkin Saudat yafi karkata Akan mijinta saboda tana son mijinta tana Kare Masa lafiyar sa, duk abinda tasan Sauban Yana buk’ata da kanta take Masa hatta abincinsa da kanta take girka Masa kofin ruwansa ba wata kuyanga ko baiwar da ta Isa ta Sanya hannu ta tabashi idan Bata hukuntataba,
Hakan da zarar Sauban yafito daga b’angarensa bayi da kuyangi suke sunkuyar da Kai k’asa suna Mai gaisuwa a garesa har sai lokacin da yawuce snn suke daga kansu,
Domin duk wacce tasake ta kallesa bare ta kalle kayan da yasaka hukuncinta na daban ne.”
Saudat kina wuta????
Sosai hankalin hajjah ya kwanta tare da maimartaba domin Sauban Yana samun kulawa a wurin matarsa.”
Wanda sauban duk abinda takeyi baya gaban sa domin kallon marar tarbiya Yake Mata wacce take azabtar da bayinta hakan Yana tsananin K’ona Masa Rai
Wanda shi mutum ne Wanda yasan darajar Dan Adam.”
Aurensu da wata uku ya shirya ya koma England domin ci gaba da karatunsa,
Yabar Saudat a Nan wacce Bata damu da tafiyar tasa ba saboda akwai Mata a kusa da ita wad’an sai ta darje domin biyan buk’atar ta.”
Komawarsa makaranta asirin wasu daga cikin fadawan masatautarsu ya Toni inda sukaje makaratar su Sauban suka kaiwa shugaban makarantar kud’i har miliyan goma Akan duk Sauban yayi jarabawa ya dinga zubar dashi.”
Shugaban makarantar baiyi k’asa da gwaiba wurin Kiran jami’an tsaro aka catke Masa su, dama sunyi magana da sarki Abdullah da zarar irin hakan ta faru ya d’aga waya yakirashi zaizo yaga wad’anda sukeyiwa Sauban wnn zalincin, na mayar dashi baya a karantunsa.”
Washe gari sarki Abdullah ya duro k’asar inda aka kaishi wurin mutanen abin mamaki fadawansa yagani wad’anda yayi matuk’ar yarda dasu,
Abin ya d’aure Masa Kai tare da Sanya shi cikin rud’ari, hakan ya bada umurni ayi ta dukansu har sai sunfadi Wanda yasakasu,
Duka akayi masu sosai Amma basu fad’aba daga k’arshe da kansu suka Sha guba suka mutu domin dama aikin sai da rai suka fito mutuwa ko rayuwa.”
Sarki yayi bakin cikin mutuwar tasu hakan yasaka aka rufeso yabaro k’asar tare da yiwa shugaban makaranta godiya,
Tin daga lokacin sauban yasamu dama da Kwanciyar hankalin yin karatunsa har yasamu nasarar kammalawa shekara D’aya da ta rage Masa yadawo gida Nigeria Cike da murna da farin ciki.”
kamar yanda kuka gani a cikin page 1 yanda ake murnar dawowar tasa.”
Mu Koma Kan labarinmu na baya muka had’e a page 15
idan ba comment yasin sai kunyi sati daya ba posting????
Mrs Ana’s Bawa✍
[8/2, 7:31 AM] Hayat: REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S✍
???? D’AN SARKI SAUBAN????
Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)
Page 15
hmmmm mutum mutum sai Allah???? Ina kallonku masu Kan kwakwa aci gaba da zuwa Rafi wata Rana tulu zai fashe ‘yan bu………????
Cigaban labari
Da kyar ya samu asuba tayi sai sak’awa yakeyi Yana kwancewa Akan Saudat,
Gaba D’aya zuciyarsa a dagule take, Wanda yarasa dalilin hakan,
Hakan jiki ba kwari ya fad’a toilet yayi wanka tare da d’auro Alwala yafito yanufi masallaci domin gudanar da sallar asuba.”
Sahu D’aya suka jera da maimartaba mahaifinsa, Bayan sun kammala yin sallar ne suka fito a tare suka jera suna ,
Tafiya suna Hira cike da burgewa suka nufi b’angaren sarki,
sarki Yana tsananin son d’ansa Sauban saboda hankalinsa da tunaninsa ga ibada Wanda duk iya Zaman da yayi a turai bai Sanya ya zubar da Addininsa da Al’adarsa ba,
Yana jijjina tarbiyar Sauban tare da yaba Masa duk da baiyi rayuwa a cikin masarauta ba Amma yafi sauran yaransa Sadeeq da Sageer tarbiya da son Addini, wad’anda kafin ka gansu sunfito sallar asuba a masallaci ma wuyacin Abu ne,
Wani lokacin har sai ya shiga da kansa b’angaren nasu ya tayar dasu Daga bacci suna kunkuni suna komai snn suke fitowa massalaci ayi sallar dasu,
Sab’anin Sauban Wanda in har Yana garin Nan sahu. Daya suke Zama dashi ko wacce sallah wani lokacin har shi yake tayar dashi idan yarigashi fitowa, hakan ba k’aramun Burgesa yakeyi ba tare da sanyashi farin ciki,
yasan ko yanzun ya fad’i ya mutu ya bar magajinsa Wanda zai rik’e Al’umma da gaskiya da Amana ga Kuma Addinin.”