BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Tafiya sukeyi a jere sai da Sauban ya Kai sarki har cikin d’akinsa ya zaunar dashi a kan kujera snn ya D’uk’a a gabansa cikin girmamawa yana fad’in “ABBA barka da asuba Ina kwana.”

Murmushi sarki yasaki Yana kallon d’an NASA mafi soyuwa a ransa, yace “barka Kade magajin sarki, katashi lafiya ya kwanan iyali?”

Sunkuyar da Kai Sauban yayi cike da jin kunya yace “lafiya k’alau Abba.”

Cikin zolaya Abba Yake kallonsa yace “Alhamdulillah tinda ka kammala karatunka lafiya hankalina ya kwanta muna fatan result Dinka shima zaiyi kyau, kamar ynda muke hasashe
Yanxun Abu D’aya nakeso a wurinka shine kabani jika,
Inaso Naga zuri’arka a doron k’asa tin kafin mutuwa ta daukeni, Wanda nasan burin Hajjah Kenan itama taga d’an jikanta mafi soyuwa a ranta.”

Sunkuyar da Kai Sauban yayi cike da jin kunyar maganar Abba,

Abba yasaki dariya ganin Sauban yanajin kunyar maganarsa yace “Ina ganin wata k’ila d’ana Sauban baya da wani kuzari a wurin iyali,
tabbas sai na gana da jakadiya domin naji tabbas kuwa tana baka dauri kana Sha.”

‘yar dariya sauban yasaki ya sunkuyar da Kai cike da jin kunya,
A zuciyarsa Yana fad’in dama ruwan zafin da Anna take kawo Masa masu kamar wani ganyen magani ta tsareshi a gaban idonta tace Dole sai ya shanyesu a she akwai wata manufa a cikinsu,
Dan hakan yakeji da zarar ya shanye ciwon Mara Yake sanyoshi a gaba har sai ya Kai da Shan ruwan Lipton da lemon tsami snn yakejin saukin jikinsa.”

Sarki ya katseshi da fad’in “Allah yayi maka Albarka Sauban tashi katafi wurin iyalinka.”

Har zai Mike ya kuma komawa ya zauna ya d’an runsuna yace “Abba yau ne nakeso zan tafi gidan gonata tare da Safwan domin mukai ziyara daga can inaso zan wuce masarautar zamfara domin mukai gaisuwa. “

Murmushi sarki yayi “yace Allah ya taimaka tabbas kayi tinani Mai kyau na zuwan naka zamfara ziyara idan katafi kace Ina gaida sarki Abdulmalik.”

Zan fad’a Masa insha Allah inji Sauban snn yayi Abba sallama yafita.”

Kallo sarki yabi bayansa dashi cike da k’aunar sa tare da sauke murmushin farin ciki Yana godiya ga Allah da yabashi d’a nagari Wanda yafito a tsatson tarbiya.”


A d’akinsa shiri yakeyi cikin wata dakakkiyar shadda milk colour Wacce tasha aiki a jikinta ya d’auko hula yasaka itama milk colour agogonsa na gwal wanda sai kyalli yakeyi ya d’auko daga Kan madubi ya d’aura Akan tsintsiyar hannunsa, ya tsun hannunsa guda uku suke sanye da zoben azurfa da zinari Mai shegen kyan gaske sai kyalli sukeyi,
talkaminsa ya saka Suma milk colour ya Kuma feshe jikinsa ta turarensa Mai dad’in k’amshi,
kansa ya kalla a madubi Yana gyara Zaman hular kansa,
tabbas Sauban yayi kyau iya kyau domin kuwa dama kyakkyawa ne.”

K’arar bud’e k’ofa yaji anshigo tare da sallama ko ba’a fad’a ba yasan Saudat ce,
Amsa sallamar yayi yaci gaba da shirinsa,

d’auke take da tiren break fast nashi,
Itama Tasha ado cikin wani leshi Wanda ya amshi jikinta sai kamshi take zubawa dama Saudat gwanace a wurin kamshi.”

A jiye tire tayi a kan d’an matsakaicin dining table dake cikin d’akin, Wanda Yake Zama akai yake cin abinci wani lokacin.”

Tana ajewa taJuyo ta tanufeshi tana kallonsa cike da sha’awa tare da matsananciyar k’aunarsa Mai cike da sonshi da yake fisgarta,
A gabansa taje ta tsaya tare da rik’o hannunsa duka biyun ta d’an sunkuyar da kanta saiti fuskarsa tana kallon cikin idanunsa,
k’amshin turarensa ya daki hancinta tayi saurin lumshe ido, ta furta kayi kyau mijina Ina Alfahari da Kai.”
had’e fuska yayi ba alamar dariya a tare dashi.”

Ganin hakan ta saki hannunsa ta d’an ja baya ta had’e hannuwanta wuri D’aya tana kallonsa???????? tace “Sadaukina Ina kwana?”

Murmushi ya D’an saki Akan lab’b’ansa domin taso tasakashi dariya yace “lafiya k’alau kintashi lafiya?”

Murmushi tayi na farin ciki, tace lafiya k’alau break fast Yana jiranka komai ya kammala.”

Baiyi magana ba ya dubi agogon hannunsa yaga k’arfe 10am lokacin break d’insa yayi ga lokaci Yana tafiya har yanzun safwan baizoba bai Kuma kirashiba, Kai tsaye wurin dining table din yanufa,
Cikin tafiyarsa ta k’asaita, hakan tabi bayansa kowa Yanaji da mulki Yana yawo a cikin jinin jikinsa,
tana ganin ya zauna akan kujera itama taje ta zauna a kan kujerar dake kallonsa,
tashiga zuba Masa duk abinda tasan Yana buk’ata ruwan te sune farko.”

D’auka yayi ya Sha Yana lumshe ido,
zuba Masa Ido tayi sai kallonsa takeyi kamar ta cinyeshi Akan so,
Dan kuwa kwalliyarsa tayi Mata kyau, don ta amshi jikinsa
a ranta tace “Sadaukina kayi kyau manyan kayana suna maka kyau.”

Ashe maganar tafito fili yanajinta Sarai yayi kamar baiji abinda taceba,
don fahimci Saudat irin matan Nan ne Masu yawan naci Akan abuda suke so,
snn ya lura duk mulkinta duk k’asaitarsa duk wulak’anta mutanen da takeyi tana D’an Jin shakkarsa,
snn macce ce jarabarbiya Mai yawan son a Koda yaushe a kusanceta tafison Koda yaushe namiji Yana kanta,
Wanda shi a wurinsa wahalar da gab’ob’en jikinsa kawai yakeyi dan ba wani abunda Yake amfanuwa da yin hakan,
Illah sai ita da yakejin tana sauke numfashi tare da kuwa kamar alamar tanajin Dadin hakan,
mere Baki yayi ☹ Wanda d’ali’arsa ce,ya ya mai da idonsa Yana kallon agogon hannunsa yaga 10:30am ya ajiye cup d’in hannunsa ya mik’e tsaye tare da d’aukar wayarsa ya shiga Kiran number safwan.”

Ringing biyu safwan ya d’aga a dai dai lokacin da yafito wanka SAFINA tana rungume a jikinsa dukansu ba Kaya a jikinsu sai zuba Masa shagwaba takeyi zaiyi tafiya ya barta. Baisan lokacin da ya d’auki wayarba ya k’ara a kunnensa, a maimakon yayi magana hankalinsa ya tafi wurinta yaci gaba da lallashinta Yana fad’in
“sorry baby bafa tafiyar kwana zamuyi ba, kekoda kwana ya riskemu bazamu wuce kwana biyu mudawoba sorry kinsan Ina tare da ke akoda yaushe zumata.”
saukar dogon tsaki yajiya da k’arfi a kunnensa
Wanda Sauban ya sakar Masa cike da Jin haushin iskancin safwan,

Safwan Kuma Gaba ya Manta da ya d’auki wayar sauban safina duk ta rikitashi.”

Murmushi safwan ya saki Yana fad’in yi hakuri abokina gani Nan zuwa yanzun nan,
Na tsaya aikin lallashi Dan kada naje na dawo a juyamun baya nashiga uku na.”

Kuma Jan wani tsakin Sauban yayi baiyi magana ba ya kashe wayarsa.”
Kan gado yanufa ya zauna, a rayuwarsa ba abinda ya tsana kamar jira Kuma Safwan yafi kowa sanin hakan.”

Saudat ta matsa taje kusa dashi ta zauna har kafafunsu suna gogar na juna idonta a kansa, don idan zata shekara tana kallonsa bazata tab’a gajiyaba,
Cikin muryarta ta Mai cike da k’asaita tace “Sadaukina tafiya zakayi ne?”

Kallonta yayi yaga ta D’an bashi tausayi ya d’an janyota zuwa jikinsa, ai Kuwa ta lafe tana shak’ar k’amshin turarensa, cikin muryarsa Mai tsada yace “gidan gona zan tafi tare da Safwan.”
Iya abinda yace da ita kenan yaja bakinsa yyi shuru.”

Lumshe idonta tayi wata irin wutar kaunarsa takeji tana ruruwa a zuciyarta,
Tashiga tinanin yanzun tafiya zaiyi da wnn kwalliyar Wacce tayi tsananin yimasa kyau jikinsa,
Kafin ya Kai mota Allah kad’ai yasan bayi da kuyangi Mata wad’anda zasuyita kallonsa,
Snn idan yatafi Allah kad’ai yasan adadin maccen da zata kallesa ta yaba kyansa.”
Wasu siraran hawayen kishin mijinta suka zubo Mata Akan fuska tayi saurin Sanya hannu ta daukesu,
Tana kallonsa tana fad’in “Allah ya tsaremun Kai a duk inda ka Sanya k’afa, Allah ya makantar da ‘yan Mata daga kallon kyakkyawar fuskarka, hak’ik’a Ina kishinka mijina.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button