BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

hmmmm Saudat kenan????

Wani murmushin gefen Baki yasaki Dan yasan kishin saudat Sarai tun a turai,
mik’ewa tsaye yayi yafita sakamakon Kiran wayar safwan da yashigo wayarsa alamar ya iso.”

Bayansa tafi suka jera suna tafiya a tare , tin daga harabar b’angarensa bayi Mata da kuyangi suke zubewa k’asa tare da sunkuyar da Kai suna Kai gaisuwa ga yarima,
daga masu hannu kawai yakeyi alamar ya amsa.”

Sai da ta kaishi bakin get din fita daga part dinsu snn ta d’aga Masa hannu ta juyo cike da k’aunar mijinta tare da kishinsa.”

A bakin motar da zasuyi tafiyar ya tarar da safwan Yana jiransa sai waya yakeyi yana dariya da alama da safina yakeyi domin ita kad’aice matsalar safwan inji sauban????”

Tsaki Sauban ya Kuma ja, yabawa fadawa umurni tare da jami’an tsaro wad’anda zasuyi tafiyar a tare umurnin da sushiga mota sutafi, a bar safwan wurin tinda bai tashi lafiyarba????

Kasancewar duk inda zaitafi indai tafiya Mai nisace sarki yaba umunin yadinga tafiya tare da fadawa da matakan tsaro saboda tsaro da Kuma kula da lafiyarsa.”

Cikin sauri fadawa suka bud’e masa mota ya shiga safwan shima ya shiga aka rufe k’ofar, motoci suka Fara fita daga gidan D’aya Bayan D’aya Wacce mota zata Kai kusan guda goma a Nan take aka Fara sakin jiniya Wacce ta Karad’e gaba D’aya gidan sarautar alamar d’an sarki zai fita kenan.”

Safwan wayarsa kawai yakeyi da matarsa yana dariya harda su d’aga k’afa yanayi Yana kallon sauban cike da tsokana,
Yana fad’in “haba Zumata nafad’a maki ki kwanatar da hankalinki, Ni dai tafiyar Nan idan bakyaso Allah yazun zan iya dawowa gida”

Wani kallo Sauban ya wurga Masa Mai cike da harara Mai dauke da ma’anar baka da hankali.”

Can yaga safwan ya tintsire da dariya Yana fad’in ok to shikenan ki gyaramun komai naki, ki kula da kanki domin idan Kika Bari wani abin yasameki bazan tab’a yafe makiba, yasakar Mata kiss a waya tare da kashe wayar “

“Mere baki sauban yayi yace” dama d’an iska a duk inda Yake zai iya nuna halinsa.”

Kallonsa safwan yayi Yana dariya yace “ranka ya dad’e ko gaisawa bamuyiba sai zagi ya biyo baya.”
Da matata fa nake waya zaka Kira da Dan iska, to idan hakan ne Kai wayasan iskancin da kayi kafin kafi cikin gidanka.”

Gyaleshi Sauban yayi ya janyo laptop d’insa yashiga dannawa.”


K’arar jiniyar da ta karad’e gaba D’aya gidan sarautar alamar ” D’AN SARKI SAUBAN zai fita kenan
Hankalin Sadeeq ya tashi matuk’a domin idan shi zai fita mota D’aya ake bashi ta fadawa wad’anda bazasu wuce guda biyar ba, wad’anda zasuyi Masa rakiya Amma Sauban harda wasu jami’an tsaro suke dafe Masa baya ana Masa jiniya”

Kai tsaye wurin mahaifiyarsa yanufa fulani, Yana huci,
Fulani dake kishingid’e ana Mata tausa,
Tana ganin shigowar Sadeeq Ransa a b’ace tabawa baiwar umurnin tafita zata gana da yarima cikin saurin baiwar tafita.”

Ta kalli Sadeeq tace “yarima lafiya meya faru?”

Cikin maganarsa ta rashin tarbiya yace “meyasa ake nuna Mana fifiko a cikin gidan Nan,
Sauban yafimu ne ko yafi kowa ne a cikinmu idan zaifita tamkar sarki zaifita yanda akeyiwa sarki jiniya hakan ake Masa sab’anin mu da ake sakinmu a sake, ba matakan tsaro wato Ana nufin mu ba Yaya bane shine d’a.”

Na rantse da Allah sai Naga Bayan Sauban sai Naga Sauban baya motsi a doron k’asa, bana sonshi yanda na tsini mutuwata hakan na tsaneshi.”

Murmushin farin ciki fulani Jamila tayi, tajanyo hannun Sadeeq tace “zauna d’ana yanzun na tabbatar da kasha nono na,
Kabar komai a hannuna Ni nasan abunda nake shiryawa,
Abunda nakeso da Kai ka rage nuna tsanarsa a gaban mutane kabar abin a ranka
Indai Ina motsi a doron k’asa Sauban bazai tab’a Kai labari ba.”

kuyi hkr nasan kun Matsu labari Sauban ya Kare mukoma Kan labarinmu to Amma idan Kuna biye Dani sai kun fahimci tushen labari snn zaku fahimci duk abinda zaici gaba da faruwa a Nan gaba idan muka Koma Kan labarinmu,

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 16

Jiniya kakeji tana tashi sannu a hankali manyan motoci kirar jeb bak’ak’e suke ta gangarawa a cikin k’aramun k’auyen Lassa dake k’aramar hukumar mulkin Adamawa.”

gaba D’aya jiniyar ta k’arad’e dukan k’aramun k’auyen Wanda maza da Mata tare da dattijai da samari kowa sai Kama ‘ya’yansa yakeyi yana shigarsu cikin gida wasu Kuma sai gudu sukeyi suma fad’in sarki ne yazo tare da ‘yan sanda.

kusan fulani da tsoron Yan sanda lol????

Babu abinda yafi daga masu hankali irin jami’an tsaro Yan sanda da sukaga gani tsaitsaye a Bayan mota ko wanne ya hak’a bindigarsa kamar wad’anda ke fagen yak’i
fuskokinsu ba wani alamar sauki ko dariya a tare dasu.”

Kai tsaye babban gidan gonar suka nufa, Wanda Yake zagaye da fadawa da masu gadin wurin, cikin zafin nama aka hangame masu k’atun get din gidan gonar suka dinga shigar da motocinsu d’aya Bayan Daya.”

Murmushi kawai sauban yake saukewa domin tinda aka shigo k’auyen na Lassa ya tsinci kansa cikin wani farin ciki tare da Annashawa duk ya Manta wata damuwarsa domin Yana tsananin son k’auyen nan tare da gidan gonarsa”

Parking motocin suka shigayi a cikin parking space, sai da suka tsaitsaya,
Snn cikin sauri fadawa suka nufo motar da Sauban Yake a cikinta suka bud’e Masa, tare da zagaye motar har da jami’an tsaro suna jiran fitowarsa.”

Sai da ya d’auki minti biyar kafin yafito, Wanda Al’adarsa ce baya saurin fitowa a mota lokaci daya sai ya d’auki minti biyar zuwa goma saboda tsaro????.”

Safwan ne yafara fitowa snn Sauban yabiyo bayansa, cike da mulki da k’asaita, Yana fito yashaki k’amshin garin yayi saurin lumshe idonsa tare da d’aga kansa sama cike da farin ciki Yaci gaba da shak’ar iskan garin Wanda Yake yawan sanyashi farin ciki da Annashawa.”

Gidan gonar yashiga k’arewa kallo Yana Mai murmushin Jin dad’i da farin ciki a fuskarsa.”

Sai da ya d’auki minti goma a hakan fadawa duka sun zagayeshi snn ya juya yafara tafiya suka rufa Masa baya zuwa cikin gidan gonar a wurin da suke sauka idan sukazo.”

Fad’in fad’i da girman wurin tare da tsaruwar wurin Bata lokaci ne Amma iya tsaruwa wurin ya tsaru babu abunda babu a cikinsa Dan gane da kayan fruit da duk wani Abinda ya danganci shuke shuke,
A can d’aya b’angaren Kuma wani wurin hutawane Wanda aka zagayeshi da manyan kujerun k’arfe domin zama,
Sai Kuma gefe D’aya da na hango wani babban dining table ne da alama shima an ajiyeshi ne domin zama asha fruit,
sai Kuma wasu manyan d’akuna guda uku da na hango a jere da juna wad’anda anyisu ne domin hutawa musamman idan tafiyar kwana tasameka, babu abunda babu a cikin d’akunan na dangane da kayan buk’atar rayuwa, d’aya daga cikin d’akunan wanda Naga Anfi k’awatashi da komai a cikinsa Bintu take sauka wani lokacin suke kwana a duk lokacin da sukazo tare da maimartaba Suna hutawa.”

A can d’aya b’angaren dake kallon Bayan gari,
wani Babban wurin wanka ne anzagayeshi da furanni Wad’anda suka k’awata wurin,
cike wurin Yake da ruwa gwanin ban sha’awa.”

Idan Kika matsa gaba kad’an fanfuna ne tare da rijiyoyi wad’anda sarki yasaka aka Gina domin jama’ar k’auyen su dinga Shigowa ta k’ofar baya suna dibar ruwa kasancewar k’auyen suna fama da k’arancin ruwa amfani.”

K’auyen Lassa k’auyen ne na fulani, ko fulanin ma irin fulanin dajin Nan masu masifar kyawo wad’an suke rayuwa a cikin daji tare da shanunsu da ‘yayansu da matansu.”
Domin duk inda ka wurga idanunka tungayen fulanine tare da bukkokinsu dake k’ank’afe a tsakiyar k’auyen sai tarin shanu da suke shawagi suna kiwo a cikin k’auyen.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button