DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL
“Jakadiya tace “ranki ya dad’e ki kwantar da hankalinki, idan yasan wata ai baisan wata ba, na rantse maki da Allah ba wani Wanda zai hau kujerar sarki sai Sageer ko Sadeeq.”
Fulani tasaki murmushi ta kalli jakadiya tace “Dan hakan nake sonki domin ko shaid’an Yana tsoron sharrinki tare da muguntarki,
yanzun meye mafita kinsan na kashe kud’i da yawa wurin karb’o maganin nan Amma shegen yaron Nan Mai Kama da Aljanu yasaka nayi asara.”
Jakadiya tace “ranki ya dad’e kibani Nan da zuwa gobe komai zai Kai k’arshe,
Fulani ta Kuma sakin murmushi tace “tashi kitafi Nima akwai abinda nake sak’awa Nan da zuwa goben.”
Wani irin mulki takeji Yana mata yawo a cikin jinin jikinta sai juya bayi da kuyangi takeyi yanda ranta yakeso,
duka k’afafunta biyu suna kan d’aya baiwarta wacce tafi tsana duk a cikin bayinta saboda bak’in da take dashi gata gajeruwa gata da k’aton Baki,
A rayuwar Saudat ta tsani tayi Ido biyu da bak’in mutum ko marar kyan mutum tafison duk abinda zatayi Ido biyu dashi ya zamana Mai kyaune, Dan hakan ta tsani wnn baiwar tata.”
Baiwar sai zufa take had’awa tagaji iya gajiya sabida gaba d’aya ta sakar mata nauyin jikinta,
Sauran bayin Kuma sai hidima suke mata cike da taka tsantsan gudun kada suyi laifi.”
Cike take da Jin haushin Sauban, hak’urinta ya kusa ya k’are a kan me Dan yaga tana sonshi, shine yake mata duk abinda yaga dama, itama fa jinin sarautace ‘yar sarkice ‘ya d’aya tilo a wurin mahaifinta,
Yanda mahaifinsa yakeji dashi itama hakan mahaifinta yake ji da ita, duk wani abinda yakeji game da sarauta tamafishi jinsa domin sarautar masarautarsu tafi sarautar masarautarsu nuna mulki da Isa,
yau kam ta shirya Masa duk abinda za’ayi sai dai ayi Amma tagaji da neman mata ‘yan uwanta namiji takeso Kuma mijinta.”
Kuyangarta tashigo da gudu ta durk’usa a gabanta tace “ranki ya dad’e ankawo sabbin bayi ‘yan mata ne wad’anda komai yaji a tare dasu nasan zakiji dad’in ma’a mala dasu sosai.”
Mari ta kwad’a mata a fuska har sau biyu tare da sanya k’afa tayi shuri da ita, sai da kanta ya daki wani tebur Wanda kayan fruit suke a jiye a kansa, cikin d’aga murya Mai cike da Jin haushi tace “bana buk’ata tashi kifita,
Ta sauke k’afarta daga kan jikin baiwar tata, ta mik’e tsaye a fusace tanufi b’angaren Sauban.”
Zaune yake akan lafiyayyen gadonsa da waya a kunnensa Yana magana da Safwan yana fad’in “inajinka kasan fa banason surutu kafa kiyaye,
Safwan yace “eh zakace hakan tinda kana kusa da gimbiya Saudat ni wlh Sauban kabani mamaki ace kadawo ko waya bazaka iya yimun ba ka shaidamun kadawo da Ban kirakaba da shikenan,
Allah wnn halin naka ya kamata ka canza shi,
Murmushi Sauban yayi tare da dafe Kai domin kansa ya Fara Sara Masa akan surutun Safwan yace “kaga yanzun dare ne inada buk’atar hutu gobe kazo zamuyi magana.”
Safwan yace “kace hakan jarababbe asha soyayya lafiya,
Mere Baki Sauban yayi yace “Kai kasan abinda ake nufi da hakan, ni bansan hakan ba,
Safwan yasaki dariya yace zaka sani ne ai,
Da sauri Sauban ya kashe wayarsa domin kada ya Kuma damunsa a surutu.”
Wnn karon da sallama ta shigo d’akin,
Wanda Sauban da yake zaune a kan gado sauke wayarsa kenan akan kunnensa ya d’aga Kai ya dubeta tare da amsa mata sallamarta.”
Ido ya zuba mata Yana kallonta, itama shi d’in take kallo anan take taji duk wata tsewa da rashin mutumci da tazo dashi ta nemesa ta rasa, domin ba k’aramun gwarjini ya mata ba.”
Kusa dashi ta nufa ta zauna a gefen gado a inda yake zaune k’afafunsu suna gogar na juna tace “Sadaukina lokacin cin abincinka fa yayi,
Ya kamata a gabatar maka da komai.”
Shuru yayi bai amsa mata ba,
Yin Shurunsa hakan Yana nufin Yana buk’ata kenan,
ta mik’e cikin tafiyarta Mai cike da k’asaita da yanga tafita,
da kanta ta had’o Masa duk wani abinda tasan yana buk’ata domin Bata barin bayi ko kuyangi su tab’a abincin mijinta domin tana tsananin kishin mijinta Bata son kowa ya rab’eshi sai ita kad’ai
Gabansa ta dire Masa komai tare da zuba Masa farfesun kifi da fresh milk Mai sanyin gaske, sai da ya d’auki minti uku snn ya mik’a hannunsa da niyar zai d’auki kofin ya Kai bakinsa, tayi saurin sanya hannunta ta d’auka ta mik’a masa kallo Ido cikin Ido sukayiwa juna Sauban yayi saurin kauda idonsa daga kallonta snn ya amshi kofin ya Kai bakinsa Yana kurb’ar milk d’in,
Sai da ta tabbatar da yaci komai ya k’oshi snn ta had’a kayan da kanta, tafita dasu waje,
Ido yabita dashi Yana kallonta har zuwa lokacin da tafita daga d’akin ,
Yashiga tunani a ransa, indai kyaune Saudat kyakkyawace ajin farko domin babu inda Allah ya rageta, sai wuri d’aya zuwa biyu.” Na farko shine Sam Bata da hallaya na gari akwaita da wulak’anta d’an Adam, d’ayan Kuma sirrinsa ne shi kad’ai yasan komeye,
shi dai har yanzun yakasa jin wani abin Dan gane da ita yasan tana sonshi tana kishinsa Amma shi Sam bayajin hakan akanta, asalima wani lokacin jiyakeyi ya tsaneta musamman idan yaga yanda take wulak’anta bayinta da kuyanginta, tana son kasancewa tare dashi shi Kuma bayajin hakan a tare dashi,
Hasalima idan ya tilastawa kansa dole sai ya kasance da ita Domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansa jinsa yakeyi baya samun wani gamsuwa bare biyan buk’ata a tare dashi illah ma ya Kuma janyowa kansa wani sabon ciwon Mara Wanda yake fama dashi a koda yaushe Dan hakan. Yake yawaita yin azumi tare da Shan lemun tsami a cikin ruwan Lipton d’insa”
Dogon tsaki yaja ya mik’e tsaye tare da cire kayan jikinsa ya d’aura towel yashiga toilet Domin ya watsa ruwa yayi Shirin kwanciya bacci.”
wasu fitananun kayan bacci tasaka a jikinta wad’anda suka fitar mata da sigar jikinta tasan komai jarumtar Sauban sai ya firgita yafita hayyacinsa idan ya ganta a cikin kayan baccin Nan,
Ko wanne lungu da sak’o na jikinta sai da tabishi da turare domin Saudat akwai son k’amshi ga tsafta,
Doguwar Alkibba tasaka ta rufe jikinta snn ta juya wurin ‘yan matan dake kwance a d’akinta su biyar, d’aya daga cikinsu har ta Fara yimata kallon K’ululla tana had’iyar miyau
dukansu kyawawane Yan mata ne masu cikar halitta bayine take zab’owa take sanyawa a gyara mata su Tana ajiyesu a d’akinta domin biyan buk’atarta.
Wnn d’alibi’ar ta dad’e tana aikatata tin a England a inda tayi karatu,
Ta dubesu da kyau tare da nuna masu wani d’akin tace “kutashi kushiga d’akin can domin yau bana da buk’atarku.”
Jiki na rawa suka bi umurninta sukayi shigewarsu d’akin snn taja dogon tsaki tafita tanufi d’akin yarima Sauban.”
Mrs Ana’s Bawa????
REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S✍
???? D’AN SARKI SAUBAN????
Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)
Page 4
Tsaye yake akan madubi cikin shirinsa na kwaciya bacci Yana feshe jikinsa da tsadadden turarensa Mai k’amshin dad’i.”
turo k’ofa tayi tashigo tare da sallama d’auke a bakinta,
Idan zata shigo d’akin Sauban kawai take sallama,
ko shi Dan tasan idan batayi sallama ba idan zata shekara goma a wurin bazai d’aga Kai ya dubeta ba, bare ya tanka mata.” sab’anin duk inda zata sanya k’afarta a cikin gidan Bata sallama saboda nuna Isa da mulkinta gani takeyi idan tayi sallama kamar ta zubar da ajinta ne gani take ta kaskantar da kanta ne idan tayi sallama.”
K’amshin turarenta ya daki hancinsa Wanda yasa yayi saurin lumshe idonsa tsikar jikinsa tashiga tashi,
Bai San lokacin da ya juyo ya kalletaba tare da amsa mata sallamar da tayi,
Ido biyu sukayi a lokacin da ta cire Alkibbar da tarufe jikinta da ita,
gaba d’aya duk ilahirin suffar jikinta ta bayya a cikin rigar baccin Wanda yasa Sauban yayi saurin cije leb’onsa na k’asa tare da kawar da kansa daga kallonta ya sauke ajiyar zuciya snn yanufi gadonsa ya kwanta tare da janyo pillow ya rungume a k’irjinsa.”