BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Zagaye wurin yayitayi yakai yadawo Yana dube dube ko Allah zaisa zai yahangota, shuru ba Alamarta, sai da yaji anfara Kiran sallar Isha’i snn ya hakura ya Koma inda yafito zuciyarsa ba dad’i ya rasa dalilin b’acin ran nasa,
Kai tsaye massalaci yanufa bai ko jira safwan ba,
Sai dai safwan ya tarar dashi zaune a sahun gaba, mamaki ya cika safwan yashiga tambayar kansa meyake damun Sauban ne munzo lafiya Amma lokaci Daya duk ya birgice.”

Hakan sukayi sallah suka Koma cikin gidan gonar, har a lokacin Kan sauban sama yake Yana tunanin tare da Jan dogon tsaki, zuciyarsa tana tsananin tausayin Safna jiyakeyi tamkar ya dauketa suyi tafiyarsu ya kaita cikin masarautarsu domin tasamu yanci kamar ko wanne yaro Mai gata.”

Dogon tsaki yaja ya juya da karfi Cikin d’aga murya mai sauti Wanda bai San yana da itaba yake fadin natsani zubar hawayenki insha Allah Nine gatanki zanyi maki gata tamkar iyayenki.”
Maganar zuci yakeyi bai San tafito fili ba.”

Wata irin dariya Mai sauti safwan yasaki Yana kallon sauban Yana fad’in “haba sai yanzun na Gane wnn sauyin naka Ashe kogin soyayya kafad’a, ni ko wacce yarinyace wnn Mai sa’a a duniya,?”
sunkuyawa safwan yayi gefen sauban cike da tsokana yace “ranka ya dad’e, kogin soyayyah ne kafada ba KO tantama sonta kakeyi.”

DA sauri sauban ya kallesa ya kuma Jan tsaki yana fad’in ” ita wa?”
Wacece kake magana a kanta?”
ya dafe kansa yace “banga dalilin DA yasa nataho DA Kaiba wlh.”

Dariya safwan yasaki yana fadin “kafini Sanin KO wacece,
Kada kadamu ko yanzun muna iya bin hanya mukoma gida idan baka iya kwana Kai kad’ai sai da macce, don kuwa nima kaina a takure Zan kwanta.”

Juyawa yayi ya wurgawa Safwan harara yace “kadauka kowa irin ka ne.”

Dariya safwan ya saki yace “har gwarani Ina a mayar da abinda ke raina bana barinshi a rai har yafara sanyani sabbatu maganar zuci tafito fili.”

Gyaleshi Sauban yayi ya rufe Idonsa tamkar Wanda Yake bacci shi kad’ai yasan yanda yakejin a ransa akan tausayin Safna.”

Hakan suka kwana Sauban bai samu wani baccin kirkiba da zarar ya motsa safna yake gani a idonsa tana kukan nan nata,
tunani kawai yakeyi hanyoyin da zaibi domin ganin ya taimaketa.”

dakyar yasamu safiya tawaye masa,Bayan sunyi sallah suka shiga Shirin barin garin zuwa masarautar zamfara,
Sosai yayiwa masu kula da gidan gonar Alheri, hakan suka tafi wurin Mai gari sukayi masa sallama shima Sauban yayi Masa Alheri Mai gari sai godiya yakeyi Yana Jin dad’i snn suka fito.”

Tunani yake a Ina zai ganta gashi bai San gidan su ba,
Waigawa yayi ya Kalli safwan dake gefensa yana waya, ya wurga masa harara cike DA jin haushi tare da jan dogon tsaki, Wanda sai da safwan ya Dan juyo ya kallesa yayi masa alama DA hannu meya faru?”
Kauda idonsa gefe sauban yayi yaci gaba da kallon gefensa da bayansa yana tinanin ta Ina zata fito.”

Karo sukaci DA wani d’an fillo yana kiwon shanu, sauban ya nufi wurinsa yana fadin “Assalamu Alaikum malam Dan. Allah tambaya nakeyi.

K’asa d’an fillo ya zube yana kallon yarima yana fadin ranka ya Dad’e da kanka Allah yasa nasani.”

Hannu sauban ya mik’a masa alamar yatashi tsaye,
AI kowa cikin sauri d’an fillo ya mik’e tsaye.”

Hannu yarima a cikin Aljihun wandonsa , yake kallon d’an fillo cikin maganarsa daki daki yace “kasan gidansu Safna?”

Safna ranka ya dad’e?” D’an fillo ya jeho masa wnn tambayar.”

D’aga Kai sauban yayi alamar eh ita nake nufi.”

Kallo safwan yake binshi cike DA mamaki DA Al’ahabi tare da ayar tambaya a bakinsa.”

D’an fillo yace “duk garin nan safna d’ayace budurwa, wata fara marar jiki kyakkyawa, hannu sauban ya daga masa ya furta ita nake nufi Ina ne gidansu.”

Cike DA mamaki d’an fillo ya shiga kwatanta masa gidan,
Girgiza Kai sauban yayi alamar ya gane, ya Ciro kudi a Cikin Aljihu ya mikawa d’an fillo, hannu na rawa ya amsa yana zuba godiya”

Sauban bai tanka masaba yajuya yanufi inda yayi masa kwatancen,
Safwan yana biye dashi cike DA mamaki ba damar yayi magana yasan halin sauban sarai DA zarar yayi magana bazai tafi dashiba, idan kuma ya dage akan sai yatafi dashi yafison yafasa ai watar da abinda yake da Niya, Wanda bazai so hakan ba yafiso yabishi a hakan har yaga yarinyar da tafara yasaka sauban sabbatu.”

Sauban a gaba safwan yana biye dashi a baya, sai shanye kwana sukeyi suna bullewa wata, suna karya wata kwana kenan wanda zata sadasu da da gidansu safna kamar yanda d’an fillo yayi masu kwatance,
sai ganin mutum sukayi anjefo daga cikin gida Wanda sauban yake tunanin nan ne gidansu safna
Safna ce kwance a k’asa tana rungume da fantekar d’ibar ruwa, matar DA tajehota waje sai kunfar baki takeyi tana d’aga murya daga cikin zauren gidan tana fad’in “munafuka mai bak’in jini duk sa’arki sunyi aure sunbarki, to kisani bazakici abinci a gidan nan ba, har sai kin d’ebo mun ruwa, tinda ba ubanki yake kawo abincin ba tsinanniya wacce aka tsinta a cikin bola.” Wayasani ba ko cikin shege uwarki tayi ta zubar dake a bola, Aljana Kawai.”

Durkusawa sauban yayi ya rok’ota ya mikar DA ita tsaye cike da tausayi, safna tana ganin sauban ta kara fashewa da kuka, yayi saurin runtse idonsa zuciyarsa tana k’una a rayuwarsa ya tsani zubar hawayenta.”

Ya juya ya kalli inno dake tsaye a cikin zaure sai zarar ido takeyi ganin yarima,
Murmushi ya Dan Saki ya tako zuwa k’ofar zauren gidan ya d’an sinkuya yace ‘ Ina kwana Inna.”

Zubewa k’asa inno tayi tana fadin ranka ya dade DA kanka a kofar gidan nan barka da zuwa bara nakira maka jauro, ta zuba cikin gida DA gudu.”

Yacika DA mamaki dama jauro yana cikin gidan akeyiwa safna wnn cin mutumcin to meye amfaninsa tinda matarsa tafi karfinsa,
Dogon tsaki yaja ya juya ya kalli safna wacce take goge jikinta tana sharar hawayen fuskarta safwan yana,mik’a Mata fantekar d’ibar ruwanta.”

Dogon tsaki yaja ya kuma juyar da fuskarsa kofar gidan, Wanda yayi dai dai da fitowar jauro”

ABIN MAMAKI BAYA K’AREWA SAI DA NA TSAYAR DA RUBUTA WNN LITTAFIN AKAN RASHIN COMMENT DINKU, SNN NADINGA GANIN ANABI PRV ANA BANI HKRI WASUMA BANYI TINANIN SUNA KARANTAWA BA, TO KUBARI KUJI KO YANZUN IDAN BANGA RUWAN COMMENT BA AJIYE RUBATA SHI ZANYI SABODA INA DA ABINYI BAZAI YIWO NA B’ATA LOKACINA NAYI MAKU TYPING SABODA JIN DADINKU COMMENT YAYI MAKU WAHALAR YI, ALLAH BANDA NARIGA NAYI ALK’AWARIN BAZAN SAYAR DA WNN LABARIN BA DA TINI NA MAYAR DASHI NA KUDI KO A JIKINA????????‍♀

[9/3, 6:26 AM] Hayat: REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 24

SHAD’I
Kamar yanda kowa yasan yanda Al’adar fulani take musamman fulanin daji masu rok’o da Al’ada, wad’anda suka d’auki Al’ada da mahimmaci tamkar Addini.”

FAGEN SHAD’I

Jarmai ne tsaye a tsakiyar fili rik’e da zungureriyar bulalarsa sai zarar ido yakeyi yana d’aga kwanda????????,
yaransa sai zuba masa kirari sukeyi suna k’Ara masa kwarin gwaiwa suna fad’in “sai kai oga mijin Safna kaine mai nasara domin nasara takace,

Gaban JARMAI a Audu ne a tsaye shima rik’e da bulalarsa fuskarsa alamun wasa a tare da shi, sai hura hanci yakeyi????????
Dukansu ba riga a jikinsu jiran umurni kawai sukeyi sufara dukan junansu.”

Gaba d’aya jama’ar gari maza da Mata sun hallara a wurin,
sun zagaye fagen wasar suna kallo suna jira a fara,
A can gefe d’aya akan kujera maigari ne zaune tare da hadimansa suna kallon yanda shad’in zai kasance.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button