BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Can d’aya gefen kuma Safna ce tsaye kusa da Baba sai kuka takeyi idanunta sunyi jajir sun kumbura Baba sai lallashinta yakeyi yana fad’in ta daina kuka Addu’a ya kamata tayiwa Audu Allah yabashi sanara ya cinye.”

D’aga kai tayi alamar “to ta daina kukan,
illah taci gaba da sharar hawayen domin duk yanda takeso taga kukan ya tsaya ta kasa saboda kuka shi keyin kan sa ba ita keyin saba,
waige Waige kawai takeyi ta inda Sauban zaifito mata domin taji a jikinta zaizo gareta.”

A can ta hangoshi tafe ya tunkaro wurin cike da k’asaita da isa mai cike da tsantsar mulki, fuskan nan tashi sai Annuri take fitarwa,
safwan yana gefensa, fadawa guda biyu suna bayansa sun take masa baya,
wani irin murmushi tasaki Wanda batasan tanayin irinsa ba,
yunkurin zuwa wurinsa tayi cike da farin ciki Baba yayi saurin tareta yana mata gargad’in kada ta karya Al’ada.”

Ido yadawo kansa kowa cike da mamakin zuwan nasa yakeyi,
Murmushi maigari yasaki yana kallonsa domin ganinsa a dai dai wnn lokacin ba k’aramun mamaki yabashi ba.”

Maigari yabada umurnin akawowa yarima abin zama,
Cikin minti uku aka d’ora kujeru sauban da safwan suka zauna fadawa suka zagayesu a baya.”

Gaisuwa maigari ya kai wurin yarima,
yarima yana fara’a suka gaisa.”
Tare da tambayarsa yaya maimartaba?”

Lafiya k’alau sauban yace,
maigari yana murmushi yacewa sauban “yau Allah ya kawoka a dai dai lokacin da muke gudanar da Al’adarmu ta shad’i Allah yasa zata k’ayatar dakai, duk da dai kaima bafulatanine amma na birni.”
Murmushi sauban yasaki tare da jinjina Kai.”
snn suka maida hankalinsu wurin shad’in a dai dai lokacin da ake neman maigari yayi magana a fagen wasa domin yayi gargad’i tare sanarwa tare da yin tini akan abinda ya gabata akan shad’i kodan ganin yarima ya halarci wurin .”

A can ya hangota tsaye kusa da baba tana kallonsa tana murmushin farin ciki hawaye suna zuba a idonta.”

Shima murmushi ya Sakar mata,
Yayi mata alamar ta share wayenta ta daina kuka.”
Ai kuwa cikin sauri ta share hawayenta tana sakar masa murmushi.”

Ido Safwan yake binsu yana kallo cike da mamaki k’iri k’iri ga gaskiya ta bayya sauban son Safna yakeyi Safna son sauban takeyi amma saboda taurin kai irin na Sauban baitab’a yarda da Sonta yakeba har b’acin rai yake nunawa idan akace sonta yake, sai yace shi tausayinta yakeyi a daina cewa yana sonta saboda shi baya da lokacin wata soyayya can ta shirme bai masan abinda an soba kuma baya fatan yasani saboda baya da lokacin shi son.”
Safwan ya Rik’e baki yana mamaki to yanzun kuma meya kawosu nan?”

Maigari yasoma bayani kamar hakan “kamar yanda kuka sani a duk bayan shekara d’aya mukan gudanar da Al’adarmu ta fulani wato shad’in fidda gwani,
Wanda Al’adace wacce muka taso muka tarar iyayemun da kakanninmu sunayi kuma suka d’oramu akai,
Indai Kai bafulata nine Wanda kake rayuwa a cikin wnn k’auyen dama wajen nan in har zaka mallaki macce, komai kudinka KO Mai mulkinka saikayi shad’i tare da abokan kashewar ka,
Anan zaka nuna bajintarka da k’arfinka snn k’arfinka ya baka macce.”

Dokokin shad’i sune bamason hayaniya tayi yawa,
Snn duk Wanda aka daka har zafin duka yasakashi ya fad’i k’asa, kamar yanda kuka sani yafad’i a fagen shad’i,
Wanda kuma bai fad’i ba shine mijin Safna banason fad’a ko wani tashin hankali a nan.”

Snn yaba da umurnin a Fara wasa.”

Anan take jarmai da Audu suka shiga dukan junansu da bulala ba girma ba arziki,
Ko wanne k’ok’ari yakeyi yakai d’an uwansa k’asa.”

Sosai Audu ya daku ya jigata jikinsa da fuskarsa suka fara fitar da jini, amma yaki ya fad’i sai buga in buga sukeyi da jarmai Wanda jikinsa kawai ne yayi kwancen bulala, jini bai fitaba,
Kuka safna ta fashe dashi a lokacin da taga jarmai yana neman cin galaba akan Audu domin jini har ya fara wankewa Audu fuska amma har yanzun bai fad’i k’asaba, Wanda da zarar ya fad’i shikenan jarmai ya ci galaba a kansa.”
hakan Audu yake dukan jarmai
jarmai yake dukan Audu, a can jarmai yasami sa’ar Audu ya doka masa bulala a tsakiyar kai, anan take Audu yasaki wata irin k’ara ya fad’i k’asa a some.”

Da gudu Safna tanufi wurinsa tana kuka tana jijjagashi tana fad’in katashi Audu katashi meyasa kabari Azzalumi yaci galaba akanka?” kana gani za’a auramun azzalumi,
ta d’aga murya cikin sauti sai da gaba d’aya wurin ya amsa tace Audu katashi .”

Dariya Jarmai yasaki cike da jin dad’in samun nasara,
Hakan masu goyon bayansa suna murna tare da ihu suka d’aukeshi suka d’agashi sama suna juyashi,
Yashiga yiwa kansa kirari kamar hakan “saini jarmai angon Safna mainasara, sai ni Jarmai d’an maigari ba Wanda ya isa ya tab’ani ya zauna lafiya.”

Snn ya sauka daga d’aukar da aka suka masa,
Yanufi wurin safna dake durk’ushe a gefen Audu tana jijjigashi tana kuka tana fad’in tashi Audu karka mutu,
hannu jarmai yasaka ya ruk’o hannunta ya mik’ar da ita tsaye ya Janyeta a wurin,
tana tirjewa tana dukan hannunsa a kan yasaketa yak’i yasaketa sai da yafito da ita tsakiyar fili ya d’aga hannunta sama yana fad’in saini jarmai na Safna,
Safna ta wace idan akwai wani Wanda yakeji da kansa yafito mukara idan uwarsa bata haifi wani ba.”

Safna tana kuka idonta akan sauban, Wanda ya runtse ido jikinsa sai rawa yakeyi alamar ransa a b’ace yake.”

Cikin zafin nama sauban yamik’e tsaye tare da cire rigar jikinsa sai ciccira yana neman yashiga filin shad’in,
Safwan ya rik’eshi hakan fadawa sukayo kansa suka rik’eshi suna fad’in ranka ya dad’e meye had’inka da shiga filin shad’i?”
bazaka iyaba, ka rufamana asiri bamaso mujewa maimartaba da mummunan labari.”

Hannu biyu yasaka ya turesu gefe d’aya dukansu sai da suka fad’i k’asa har safwan,

jikinsa sai rawa yakeyi yanufi wurin jarmai ya fisge hannun safna daga hannunshi ya turata gefe d’aya snn ya duk’a ya d’auki bulalar da Audu ya jifar k’asa
Yanuna Jarmai yana fad’in,
Kana fad’in sunanka Mai nasara amma yau kasanyawa ranka daga yanzun sunanka marar nasara,
domin bakomai akeyin nasara akansaba,
har yanzun Safna bataka bace Safna ta mai raboce tsakanin ni da kai.”

Da gudu safna ta nufo wurin yarima tana kuka takai durkushe a gabansa tana fad’in banaso na rasaka, domin bazaka iya da wnn Azzaluminba kayi tafiyarka kawai.”

janyeta yayi a gabansa domin ya tsani ganin kukan nan nata a idanunta, ransa ya kuma b’aci jijiyoyin kansa duk suka firfito jikinsa sai rawa yakeyi yana kallon jarmai.”

Dariya Jarmai yasaki yana kallon yarima yace “d’an birni zaka iya karawa dani?”

Bai iyar da rufe bakinsaba cikin zafin rai Sauban ya sakar masa bulala a tsakiyar gadon bayansa, wacce anan take wurin ya tulb’e da jini,
Ai kuwa shima jarmai yashiga kaiwa yarima duka kota Ina,
Idon yarima a rufe suke saboda b’acin rai da zuciya bayajin dukan da jarmai yake masa shima cikin zaffin nama yake kaiwa jarmai duka anan take bakin jarmai ya fashe da jini abinda bai tab’a faruwa dashiba,
Dukansa sosai sauban yakeyi dukanda bayaji baya gani domin idonsa a rufe suke,
Dukan da ya kaimasa a tsakiyar kai yasaka jarmai zubewa k’asa a some.”

Ihu mutan gari suka d’auka suka tunkaro sauban suka d’ashi sama suka shiga juyashi kamar yanda Al’ada take.”

umurni ya bada akan a saukeshi sakamakon kansa da yakeji yana Sara masa,
Ana saukeshi Safwan yanufo wurinsa ya mik’a masa riga yasaka, da gudu safna ta nufoshi ta fad’a kan jikinsa tasaki kukan farin ciki,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button