BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

domin muna amfani dashi a duk lokacin da hakan ta faru, musamman ga Wanda akayi shad’i dashi Saboda yana karye dafin bulala yanda bazata kwanta ajikinkaba bare tayi maka tabbo.”

Murmushi sauban yasaki yace “nagode Baba,

Baba yace “bakomai zaka iya gyarawa na Shafa maka A duk inda bulalar ta kwanta maka.”

Gyara kwanciya sauban yayi ya ajiye rigar da ya rufe jikinsa gefe d’aya,
Baba ya matso ya shiga shafa masa maganin a duk inda bulala ta kwanta masa.”

Sosai jikinsa ya d’auki zafi alamar akwai zazzab’i a tare dashi, idonsa a kan Safna wacce take tsaye a Bayan Baba tana kallon yanda kwancin bulala duk ya b’ata masa kyakkyawar fatar jikinsa, hawaye tausayinsa kawai ke zuba a idonta,

Wanda duk wani d’igo na hawayenta jinsa yakeyi har cikin zuciyarsa tamkar ana yayyafa masa ruwan zafi yakeji,
saurin runtse idonsa yayi cike da k’unar zuci domin baya son ganin zubar hawayenta ko kad’an a rayuwarsa.”

A hakan Baba ya kammala Shafa masa maganin ya gyara masa kwanciya ya nemi wuri a kusa dashi ya zauna, Baba yayi gyaran murya yace Allah yabaka lafiya insha Allah wnn maganin zai taimake ka sosai zakaji k’arfin jikinka da walwalarka duka zata dawo,
Ranka ya dad’e idan ba damuwa inaso zanyi magana da Kai.”

Bud’e idonshi sauban yayi ya tashi zaune yana kallon Baba da Safna wacce ganin Baba ya zauna itama taje kusa dashi ta zauna a gefensa,
har yanzun hawaye ke zuba a idonta tana gogewa da bayan hannunta,
Kallonta sauban yakeyi yana jijjina wnn soyayyar dake tsakanin Baba da Safna domin ya lura yana tsananin sonta itama hakan.”

Baba ya fara da cewa “hakika kayi namijin k’okari wurin karawa da Jarmai a wurin shad’i, kuma daga k’arshe Allah yabaka nasara akansa Wanda duka Mutanen gari suke cike da mamakin hakan har yanzun,
Kamar yanda kasani jarmai yakanyi shad’i akan yasami macce idan yasa meta yayi nasarar Aurenta daren farko yake keta mata mutumcinta yayi mata illah sosai Zara kasa moruwa, da yawa daga cikin wad’anda ya aikatawa hakan wasu sun mutu wasu sun nakkasa yanda bazasu tab’a moruwaba har Abada.”
Ranka ya dad’e nasan kasami wnn labarin ne shiyasa ka shiga shad’i domin ka taimaki rayuwar Safna ba wai dan kana sonta ba har cikin zuciyarka,
Alfarmar da nake nema a wurinka itace, ka taimaka mun ka Auri Safna koda baka sonta saboda tafita daga cikin wnn k’auyen Wanda zamanta a cikinsa a halin yanzun yanada hatsari sosai a rayuwarta da tawa baki d’aya,
musamman idan jarmai ya gyallara ido ya dinga ganinta, tana yawo a cikin garin nan.”
Ranka ya dade koda baka ra’ayin Aureta bata cikin tsarinka,
Ina neman Alfarma a Karo na biyu shine a cikin bayinka KO kuyanginka ka nemo Wanda ka yarda dashi ka yarda da hankalinsa ka aura masa Safna,
Babba burina a rayuwa shine Safna tabar garin nan,
Tasami inda zata zauna cikin kwanciya hankali da natsuwa.”
Ka dubi maraicinta Safna bata da iyaye Allah shine gatanta.”

Sharad’in shad’i a garin nan shine, idan kayi shad’i kamar a yau,
A gobe duk Wanda yacinye zai tura mahaifansa a wurin maigari domin asaka ranar Aurensa da yarinyar,

Ranka ya dad’e miye mafita kai nake saurare.”

Murmushi sauban yasaki domin duk magagganun da Baba yakeyi yanajinsu suna durar masa har cikin zuciyarsa tsantsar tausayin Safna mai zafi yakeji yana dakar masa zuciya,
Idan yabari yabawa wani aurenta bai san yanda zai amsheta ba, bai san yanda zai tausaya mata ba,
shi ya kamata ya amshi Aurenta domin yafi kowa sanin ko wacece safna domin ya rik’eta tsakani da Allah yaji tausayin maraicinta ya share Mata hawayenta,
Da duk wahalar da Tasha a baya tazama tarihi a rayuwarta.”

cikin muryarsa ta marasa lafiya yace “Baba ni Zan auri Safna,
Ni Zan zauna da Safna domin tasami farin ciki mai d’orewa, yanda zata manta da batada iyaye ta manta da ko ita wacece a duniya.”

Yau komai dare Zan koma gida gobe zan turo maimartaba da fadawa domin a nemamun Auren Safna.”

Wani irin murmushin farin ciki Safna tasaki Wanda yasa Sauban shima murmusawa,
Yaci gaba da fad’in Ka kwantar da hankalika Baba babu abinda jarmai zaiyiwa Safna tin daga yanzun har zuwa lokacin da zatabar garin nan, kafin na wuce zanga maigari zan zauna dashi zamuyi magana.”

Godiya sosai Baba yake masa har sai da sauban ya dakatar dashi,
Snn Baba yayi masa sallama tare da fatan samun lafiya yanufi hanyar waje Safna tana biye da Baba a baya.”

Kallo sauban yabita dashi yana murmushi Wanda baisan yana yinsaba,
har zasu fita daga d’akin sauban yakira Baba yace “Baba Ina neman Alfarma zanyi magana da safna.”

Cak Safna taja ta tsaya a inda take,
Baba yana murmushi yace badamuwa ya kalli Safna dake tsaye ta sunkuyar da kai yace “kije wurin yarima ki kula da kanki,
Snn Baba ya wuce yanufi gida.”

Tsaye tayi wuri d’aya a inda take takasa motsawa,
kanta a sunkuye cike dajin kunya.”

Kallonta yakeyi cike da Burgewa domin yana son macce mai kunya,
Juyawa yayi ya kalli safwan Wanda yake zaune a kan kujera latsar waya kawai yakeyi azahirance kamar baisan abinda akeyi ba,
Amma Duk abinda da akeyi yanaji a kunnensa kuma yana gani da idanunsa,
mamakin sauban yakeyi a yanda soyayya tayi masa mugun kamu wacce baisan yanayin taba,
Bai san tayi masa mummunan kamu ba.”

Sauban yana kallon Safwan ya had’e fuska yace ” malam saika fita magana zanyi da ita.”

Banza Safwan yayi dashi kamar badashi yakeyiba.”

A hasale Sauban yace Safwan kanajinafa nace kad’an bamu wuri magana zanyi da Safna.”

Sai a lokacin Safwan ya kallesa yasaki murmushi cike da tsokana yace “cewa zakayi nad’aga nabaka wuri soyayya zakayi da safna.”

Harara sauban ya kai masa yace “ka d’auka kowa irinka ne, mutu macce.”

Dariya mai sauti Safwan yasaki yanufi hanyar waje yana fad’i waye ni ai duk abinda nakeyi shafin maine dan ka zartani a fagen soyayya yarda ne kawai bakayiba.”

Mere baki sauban yayi yabishi da harara, sai da yaga fitarsa snn ya koma kan safna wacce take a tsaye a bakin k’ofa sunkuye da kai cike da jin kunya.”

Muryarsa taji yana kiran sunanta cikin wata irin murya Mai taushin gaske,
“Safna kizo mana.”

Sannu a hankali take takawa kanta a sunkuye a k’asa ta nufi wurinsa.”

Murmushi yake saki a fuskarsa ganin batason had’a ido dashi,
A gabansa tazo tayi tsaye kanta a sunkuye gefen gado yanuna mata a kusa dashi yace ” zauna a nan.”

Da sauri ta d’aga kai ta kallesa ta kuma sunkuyar da kai tace “A nan Zan zauna tana nuna k’asa.”

Kallon d’an k’aramun bakinta yayi tare da kyakkyawar fuskarta yaji ta burgeshi,
Yace “safna musu zakiyi dani tin yanzun?”

Da sauri ta girgiza kai alamar “A’a.”

Yace “zo nan ki zauna, ya kuma nuna mata gefensa.”

A hankali ta tako tanufi inda yace ta zauna, tare da sunkuyar da Kai ta zauna”

Idonsa akanta yana murmushi,
Yace “safna wnn kunyar tayi yawa a d’an ragemun ita.”

Rufe fuskarta tayi da tafin hannunta tana murmushin jin kunya.”

Murmushin shima yakeyi yace “ko sannu ya jiki baki cemun ba, bayan akanki aka dokeni.”

Janye hannunta tayi a fuskarta ta kallesa cike da tausayi ta zame daga kan gadon zuwa k’asa tana kallonsa tace “kayi hakuri ya jiki?” Insha Allah zakasamu sauk’i.”

Kallonta yakeyi cike da burgewa ji yakeyi kamar ya janyota ya d’orata akan k’irjinsa,
Cikin kasalalliyar murya yace “tashi kidawo inda kike ki zauna,

Cikin shagwab’a wacce d’abi’ar tace,
Take fad’in ni sai ka amsamun gaisuwata ko Zan tashi.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button