BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

“Wow Sauban yace domin tayi matukar burgeshi shagwab’ar tayi mata kyau,
Ajiyar zuciya ya sauke snn yace “Alhmdulillah naji sauki Safna rigima sai a tashi azo a zauna.”

Tana murmushi tazo ta zauna a gefensa,
Yana kallonta yace “Safna burina a koda yaushe naga wnn murmushin ya danwama a kan fuskarki banason ganin kukanki,
dan hakan na yanke shawarar Zan amshi Aurenki domin d’orewar farin cikinki kinsan dama nayi maki Alk’awarin Zan taimakeki Zan samar maki farin ciki Mai d’orewa,
Safna ki yarda dani?
Zaki Aure ni?”

Hawayen farin ciki suka shiga d’iga a idonta, domin tarasa bakinda zatayi masa magana,

A gabansa takai durk’ushe hawaye suna zuba a idonta,
Tace ni wacce ce da Zan furta bana sonka,
Kai ka taimakeni kayimun dukan komai a rayuwata, yarima nasan kafi k’arfina ni ba ajin aurenka bace, amma saboda ganin nasamu farin ciki wanda iyayena basa tunanin nasameshi tinda suka iya jefar dani akan titi, batare da sunyi tinanin halin da zan shigaba, Kaine mutum na farko da ka sanyani farin ciki, kaina wanda kake tausayina kake sharemun hawayena
Ni wacce da zan furta bana son ka?”
Kaine wanda ya taimakeni daga fad’awa daga cikin wata rayuwa wacce har gara wacce nake cikinta a yanzun da wacce Zan fad’a a hannun jarmai,
Babban burin yarima shine ya taimakeni ya bani gata ya ‘yanta daga cikin k’angin bauta,
bakinta yana rawa akan kukan da yakeson yaci k’arfin ta kuma matsowa daf dashi saiti k’afafunsa ta sunkuyar da kai tace Yarima inasonka zan Aureka Zanyi biyayya a gareka tamkar baiwa,
Zan bi dukkan umurninka fatana kada kajuyamun baya idan katina da ni shegiya ce banada iyaye, ta fashe da kuka mai sauti tamik’e tafita da gudu tabar d’akin tanufi hanyar gida tana kuka.”

Runtse idonsa yayi zuciyarsa cike da tausayinta yakai kwance anan take zazzab’i Mai zafi ya rufeshi.”

Safwan ne yashigo ya tarar dashi cikin yanayin zazzab’i,
Anan take yakira direba suka shiga shirin tafiya domin yaga likita.”

Sauban yana jin jiki, amma
Hankalinsa yana kan zuwa wurin maigari domin ya gana dashi yayi maganar safna akan gobe zai turo iyayensa.”

Zazzab’in da yake damunsa yaci k’arfinsa sosai ko magana baya iyayi idonsa a rufe,
cikin gaggawa Safwan ya Rik’ashi yasakashi a mota suka bar k’auyen suka nufi gida.”


Mota goma sarauniya Bilkisu tacika da dakaru masu shirin yak’i domin sutafi k’auyen su safna sutayar da garin”

Kafin sutafin sai da takira Saudat tak’ara yi masu kwatancen k’auyen,
kamar yanda fadawa suka fad’a mata.”

gudun kada asami matsala wurin aiwatar da aikin tacewa fadawan da tatura,
Tabasu umurnin akan su dakata kada sudawo sujira zata turo dakaru domin su nuna masu gidansu safna,
Tana buk’atar a tashi k’auyen gaba d’aya.”

Anan suke fad’a mata yarima Sauban yabaro k’auyen yana kan hanyar komawa gida.”
[9/9, 6:09 AM] Hayat: REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 27

* ” murna Saudat takeyi jin sauban yabaro k’auyen,
yanda dakaru zasu sami damar cika aikinsu batare da wata matsala ba.”

Kiran sarauniya Bilkisu Saudat tayi, tace “mommy bani d’aya daga cikin shugaban dakarun zanyi magana dashi.”

Mommy tabata shugaban rundunar gaba d’aya Wanda yafi sauran rashin imani da kafirci.”

Saudat takira sunansa “tace “Barde kanajina, umurni nabaka kafin Ku cinnawa gidansu yarinyar wuta, Ka tabbatar da kayi mata kaca kaca kayi mata fyad’e Wanda har abada bazata k’ara moruwa ba, snn ku cin nawa gidan wuta duk su k’une da duk zuri’ar su.”

Dariya Bard’e yasaki yana fad’in “angama ranki ya dad’e duk abinda kikace hakan zamu aiwatar Allah ya k’ara girma da d’aukaka,
Snn ta kashe wayar a jiye gefe d’aya tana sakin dariyar farin ciki da jin dad’i, burinta ya cika domin da zarar anruga kauyen anyi Mata fyale koda ta rayu a duniya bazata tab’a moruwaba, yarima zaiji ya tsaneta tinda ta riga da ta nakkasa.”

A guje dakaru suke shek’a gudu bana wasaba, duk wasu kayan aiki sun tanadesu cikin motocinsu Kai tsaye suka nufi k’auyen Lassa.”


A gaggauce Safwan suka iso,
kai tsaye asibity aka nufa da sauban domin jikin nasa yayi nauyi sosai numfashi kawai yake saukewa baya iya bud’e idonsa,
Taimakon gaggawa likitoci suka shiga bashi,
Snn safwan yakira maimartaba yake shaida masa a inda suke a yyanzun,
suna asibity da sauban ankwantar dashi baya da lafiya.”

Hankali maimartaba ya tashe idonsa rufe yakira Hajjah ya fad’a mata halin da sauban yake ciki

Anan take, Hajjah da Anna suka shiga shiri tare da fadawa suka nufi Asibityn.”

ai kuwa cikin minti goma gidan sarautar ya d’auki Labarin yarima Sauban baya da lafiya yana kwance a asibity.”

Inda Sarauniya jamila tayi murna tayi farin ciki tare da Addu’ar Allah yasa daga can sai k’abari

A bakin wata baiwa Saudat taji labarin cewar mijinta baya da lafiya,
Ai kuwa hankalinta ya tashi cikin zafin nama da k’unar zuci, tashirya ta nufi asibityn kasan cewar family hospital ce kowa yasanta.”

bak’aramun tashin hankali hajjah tashi cikin saba a lokacin da taga yanda sauban ya rame lokaci d’aya,
Uwa uba taga duk jikinsa kwancin bulala ne, tayi masa jajir akan farar fatar jikinsa,
Wurinsa tanufa cike da tashin hankali,
yana kwance a kan gado ana masa k’arin ruwa idonsa a rufe yana bacci tare da sauke numfashi sannu a hankali, kansa tashiga shafawa tana fad’in Sauban meya sameka?” Meya faru da kai?, nashiga uku wnn yaro marayan Allah kana ganin rayuwa iri iri.”

Saudat ta bud’e k’ofa ta shigo ido rufe tanufi wurin sauban ta fad’a kan jikinsa ta saki kuka mai sauti.”

Kallonta hajjah takeyi cike da tausayi ta janyota zuwa jikinta ta rungumeta tana lallashinta,
Ganin yanda jikin Sauban ya kwanta da bulala ya kuma sanya Saudat ta fashe da kukan bak’in ciki da tsananin kishi, domin tasan dukan da akayi masa ne akan tsinanniya yarinyar da yakeso ‘yar k’auye, yanzun gashi nan yana neman ya hallaka kansa da rayuwarsa.”

Likita ya turo k’ofa yashigo tare da Safwan yana biye dashi a baya, kai tsaye wurin sauban likita yanufa, ya k’ara dubashi tare da yi masa Allura,
Safwan yana bayan likita a tsaye yana kallon sauban cike da tausayi”

Kallon Safwan Hajjah tayi tace “Safwan meyasami abokinka ne a lokacin da kuka tafi gidan gonar?”

Turo k’ofar da akayi ita ta hana Safwan ya bawa hajjah amsar tambayar DA tamasa.”

Maimartaba sarki ne da kansa ba aike ba,
Yashigo fadawa suna biye dashi a baya,
Ganin yanda Sauban ya koma lokaci d’aya ba k’aramun firgita sarki yayi ba, musamman yanda yaga jikin nasa duk ya kwanta da shatin bulala.”

Safwan sarki ya kalla cike da ayar tambaya yace “Safwan meyasami magajin Sarki hakan?”
Ya akayi naga jikinsa da kwancin bulala?” Meya faru a cikin gidan gonar?”

Sunkuyar da kai Safwan yayi cike da ladabi yashiga bawa sarki labarin shad’in da akayi da yanda sauban ya kamu da son yarinyar bai san yanayi ba.”

Sautin kukan Saudat sukaji wacce tafita a d’akin da gudu saboda bakin cikin abinda Safwan yake fad’a.”

Sosai maimartaba ya tausayawa sauban domin yasan zafin dafin so tin a kan mahaifiyarsa Bintu,
Yasan yanda so yake illahta zuciya da gaggar jiki gaba d’aya,
so yakansa mutum ya makance ya daina ganin kowa sai abinda yakeso
So ya kansa mutum ya haukace ya zama tamkar marar, hankali ya dinga sabbatu a duk inda ya tsinci kansa,
masoyi zai iya sadaukar da rayuwarsa da,farin cikinsa da lafiyarsa a kan masoyinsa,
Wanda shine sauban yayi ya sadaukar da gaggar jikinsa,da lafiyarsa domin ganin ya ceto masoyiyarsa daga halaka.”
girgiza kai maimartaba yayi yana murmushi domin shi sam baiga laifin sauban ba, idan akace bintu zata dawo duniya zaiyi abinda yafi hakan akanta.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button