DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Ran Hajjah ya b’aci matuk’a musamman da ganin Saudat tafita tana kuka,
Tace “wnn ai sakarci ne, ta yaya zai kara jikinsa a dinga zuga masa bulala har hakan a kan macce wace irin macce ce wnn wace tafi sauran matan duniya,
Na rantse da Allah da Nasan wnn sakarcin zaitafi yayi da bazan barshi ya tafi gidan gonar ba.”
Murmushi maimartaba yayi yace kiyi hakuri Hajjah jarumin namiji shike nuna bajintarsa akan abinda yakeso,
sauban yayi matukar k’ok’ari wurin karawa da fulanin daji a wurin shad’i, wnn ya nunamun cewa Sauban jarumine ko a fagen yak’i zai iya fafatawa da mak’iya .”
Hajjah ta wurgawa sarki harara cike da jin haushi tace “ai dama duk abinda sauban yakeyi kai kake d’aure masa,
Har yaje ya kashe kansa da kansa a kan macce.”
Cikin fushi hajjah tabar d’akin saboda takaici tanufi wurin Saudat domin ta lallasheta,
Wayam tagani ba Saudat ba fadawanta ba alamarta,
Alamar tayi zuciya kenan tabar asibityn.”
Sai wurin k’arfe goma na dare dakaru suka Dura k’auyen su safna,
Rarraba k’afa sukayi gaba d’aya suka zagaye k’auyen,
Fetur suka fito dashi da ashana karon farko suka shiga kunnawa runbun hatsin da duk sukaci karo dashi,
Anan take garin ya d’auki hasken wuta, tanaci bal bal,
Tin shigowarsu hankalin mutanen k’auyen ya tashi domin yanda sukaji shigowar motocin suka tabbatarwa da kansu ba lafiya,
duk Wanda yake bacci aka tayar dashi yara k’anana iyayensu suka goyasu a bayansu sukayi tsaitsaye suna jiran mutuwa ko rayuwa.”
Hakan gidansu safna Wanda yake zagaye da dakaru,
Idon safna biyu domin batayi bacci ba gabanta kawai takeji yana fad’uwa yarima take gani yana mata gizo a idonta, anan take ta tabbatarwa da kanta yana cikin mawuyacin hali.”
Sautin maganar mutane taji a bayan d’akinta suna fad’in mu cinawa gidan wuta kawai kowa ya k’one,
Wani Mai kakkausar murya yace “gimbiya Saudat tace “na haye yarinyar na moreta son raina, snn daga k’arshe mukasheta.”
Idonta ya cika da hawayen tausayin kanta domin, ta tab’ajin sunan matar yarima Saudat a bakin Safwan,
Wani lokacin suna tare da yarima safwan yakira wayar sa,
Yake shaida masa da cewa ya ina ne,
GIMBIYA SAUDAT takira wayarsa tace tajita a kashe,
tace ya kirata tanason zatayi magana dashi,
A lokacin dogon tsaki taga sauban yaja bai bawa Safwan amsaba illah ya kashe wayar gaba d’aya ya ajiye,
anan ta fahimci matarsa ake nufi
Cikin ranta tashiga fad’in Ashe sunanta Saudat, tin daga lokacin sunan Saudat ya tsaya mata a rai,
Duk lokacin da taji an anbaci sunanta takanji gabanta ya fad’i ta rasa dalili hakan da takeji,
hannu tasaka tashare wayen fuskarta ta mik’e tsaye, tanufi k’ofar fita,
Tana fad’in wato itace ta turo a kasheni kenan burinta ayi mun illah a rayuwa mai natare mata?” Hasalima bata sanniba ban santaba.”
Tanajin muryar su a waje suna shawar yanda zasu shigo cikin gidan,
Cikin sand’a tabud’e k’ofar d’akin tafita tanufi d’akin baba Wanda suke tare da inna idonsu biyu sunajin duk abinda ake fad’a a waje ko wanne sai zarar ido yakeyi cike da tsoro,
Ganinta da sukayi Baba ya taso ya rungumeta yasaki kuka itama safna kuka takeyi domin sun rigada sun sadakar lokacin mutuwarsu ne yazo,
Inna sai fad’I takeyi muna zaman zamanmu lafiya muka d’aukarwa kanmu bala’i da masifa Safna ke annoba ce a rayuwarmu.”
Jin anfara durowa cikin gidan, yasaka inna yin shuru, bakinta kawai ke rawa.”
Hannu Baba safna ta Rik’e cike da zafin rai tace “baba mugudu bana son rabuwa da Kai.”
Girgiza kai Baba yayi yace “Safna ta ina zamu gudu bayan gasu nan suna shigowa cikin gidan da Zarar munfita kashemu zasuyi.”
Safna tace “baba idan bamu fita a gidan nan ba cinnawa gidan wuta zasuyi duk muk’une a cikinsa,
Baba zaiyi magana wani k’arfi yazowa Safna ta fisgo hannun Baba suka bud’e k’ofa suka fito inna tana biye dasu a baya,
K’atti majiya k’arfi hud’u suka gani a cikin gidan sun juya baya sunajiran shigowar Sauran,
Cikin sand’a safna take Rik’e da hannun Baba sukabi ta bayansu suka nufi k’ofar baya sukafita, Wani irin ihu inna tasaki a lokacin da ta taka k’usa a k’afa, Wanda ya hankaltar da dakarun inda suke.”
Suka nufo wurin inna tana kwance rik’e da k’afa,
Safna tana rik’e da hannun Baba sai gudu suke shek’awa.”
Ai kuwa dakarun sukace gata can ta gudu,
Suka dafawa safna,
Gudu kawai sukeyi dakaru suna biye dasu a baya da makamai a hannu,
Baba ya fisge hannunsa daga na Safna sakamakon gajiyar da yayi da gudu ji yakeyi kamar numfashinsa zai d’auke,
Ya kalli safna hawaye suna zuba a idonsa yace “safna kiyi tafiyarki Allah zai taimakeki zai tsiratar dake a duk inda kika tsinci rayuwarki, kibarni su kasheni domin baxan iya kub’utar DA kaina daga garesuba, bazan iya aikata komai ba, Allah yayi maki Albarka,
Ki mik’e kada ki karya kwana a kan hanya kike, zatayi magana kenan ta hango dakaru sun kusan zuwa wurinsu, a lokacin Baba ya zube ya d’auke numfashi,
tanaji tana gani tabar Baba a wurin ta keci daji da gudu,
Gudu takeyi suna biye da ita a baya jefa k’afa kawai takeyi a cikin daji batasan inda takeba ga duhun daji.”
Wayyo safna????????
Mrs Ana’s Bawa✍
[9/9, 7:43 AM] Hayat: REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S✍
???? D’AN SARKI SAUBAN????
Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)
Page 28
” Gudu take shek’awa Idon rufe jefa k’afa kawai takeyi a duk inda tasamu hanya, Wanda takejin zugin zafi k’afarta kasancewar ba talkami a tare da ita,
Wani irin k’aton macije tagani ya tashi tsaye a gabanta Wanda girmansa baya misaltuwa,
Wani irin ihu tasaki ta zube wurin a some.”
Sautin ihunta yayi dai dai da farkawar Sauban a kan gadon Asibity, babu abinda yakeji a kunnensa sai sautin kukan safna tare da ihunta da ya farkar dashi.”
Waige waige yakeyi akan gadon asibityn domin yakasa barin jin sautin a kunnensa,
Hajjah ta taso tanufoshi tana fad’in “Sauban ka farka me kakeso?”
Girgiza Kai yayi alamar baya son komai, ya lumshe idonsa hawaye suna zuba a gefen idonsa.”
Kallonsa takeyi cike da mamakin ganin hawaye suna zuba a idonsa, yaushe rabon da taga hawayen sauban tin yana k’arami, KO a lokacin ba komai yake sakashi zubar da hawayeba,
Sai gashi yanzun da girmansa yana zubar da hawaye.”
Matsawa ta kumayi a gefen gadonsa tana share masa hawaye tana fad’in “magaji meyake damunka?”
Me kakeso?”
Kukan me kakeyi?”
Girgiza mata kai yayi alamar ba komai hawaye sukaci gaba da zuba a idonsa.”
Babu Neman da dakaru basuwa safna ba a cikin dajin amma basu ganta ba wata alamarta.”
ai kuwa Sai k’ara kutsa Kai sukeyi cikin dajin, da manyan fito masu hasken gaske a hannunsu,
D’aya daga cikinsu yaji wani abin ya sareshi a k’afa, wani irin Ashar yasaki ya juya domin ganin Ko meye wani irin k’aton maciji yagani ya nad’e wuri d’aya,
ya kuma kai masa Sara a cinya,
Ihu yasaki ya d’aga murya yana fad’in ku gudu kada ku karaso maciji,
ai kuwa anan take kumfa yashiga zuba a bakinsa ya fad’i wurin a macce,
Sauran dakarun sunajin hakan suka juya a guje, macijin yabi bayansu shima suna gudu yana gudu yana biye dasu a baya yana masu rakiya sai da yayi nasarar kashe mutum biyu a cikinsu snn saura suka tsira.”
Koda suka shiga cikin k’auyen suka shiga cinawa gidaje wuta k’urumus suka k’one gidansu safna tare da makotansu snn suka shiga mota sukabar k’auyen cike da bakin cikin mutuwar yan uwansu.”