BABU SO HAUSA NOVEL

DAN SARKI SAUBAN COMPLETE NOVEL

Gaban sauban ya fad’i dajin furuncin hajjah.”

Sarki yace “tabbas hakan ne umma,
Sai dai inaji a jikina kamar farin cikin da mahaifiyarsa take fad’ar masa zai samu a cikin gidan gonar sa,
Ina hasashen shine ya fara bayyana a garesa.” Domin samun macce ta gari babban farin cikin d’a namiji, yasami rabin duniyarsa domin kullum cikin farin ciki zaiyi ta zama har k’arshen rayuwarsa

Yanufi k’ofar fita yace “muntafi,
Hajjah tace “adawo lafiya.”

Snn Sarki yafita ya bawa fadawa umurnin sushiga mota,
ya fad’a masu inda za’a tafi,
Suka d’auki hanyar k’auyen Lassa.”

Suna fita daga asibityn Anawa Sarki jiniya,
Alhaji Habib Naira shima yashigo da tawagarsa sarki yabada umurni a tsaya,
hakan shima Alhaji Habib yaba da umurni a tsaya, anan suka fito daga motar suna dariya suka shiga gaisawa da juma cike da farin ciki da kewar juna,
Tare da tambayar yaushe rabo,
Domin Alhaji Habib business dinsa baya barinsa zama yau yana wannan k’asa gobe yana wancan k’asa jibi yana wancan k’asa.”

Anan Alhaji Habib yake tambayar Yaya Sauban?” Ai yanzun
Yasan yaron ya girma sosai.”
.dariya sarki yasaki yana fad’in sosai kuwa har yayi aure,
Yanzun hakan k’arb’o masa auren mata ta biyu zamu tafi muyi.”

Kuma tab’awa sukayi suna dariya Alhaji Habib yace “yaro yayi gadon ajiye mata da yawa,
kaine baya ko ni.”

Sarki yasaki dariya yana fad’in lafiyar kenan, ai duk Wanda ya ganmu yasan ba rangwanci a tare damu.”

Suna dariya tare da zolayar juna sukayi sallama ko wanne yashiga motarsa Alhaji Habib yana fad’in abokina kafin natafi zan shigo fada domin asakamun Albarka,

Sarki yana dariya yace “badamuwa sai ka shigo,
Sukaja mota suka tafi cike da farin cikin ganin juna domin abokanaine sosai kasuwanci ne yarabasu da junansu.”

Sarki yana fita daga asibityn likita yashigo ya k’ara duba jikin sauban yaga yasami lafiya,
Anan take ya sallamesu direba tare da fadawa suka d’aukesu a mota suka nufi gida su.”


Dawowar dakaru da labarin da sukaje dashi na tarwatsa k’auyen su safna ba k’aramun farin ciki yasaka Saudat da mahaifiyar taba,
Musamman dasukaji cewar Safna ta mutu domin,
Sunce dajin da tabi da gudu anan ne maciji ya kashe biyu daga cikin mutanensu, suma dakyar suka sha,
Suna da yak’inin ko gaggar jikin safna baza’a gani bare gawarta shikenan ta mutu sai dai wata ba itaba”

Wayyo dad’i a ranar Saudat kid’a tasaka a b’angarenta saboda farin ciki sai cashewa takeyi tana rawa, tana juyawa Yau duniya tamata dad’i, gaba d’aya ta manta da mijinta dake kwance akan gadon asibity.”

Har sauban yadawo gida batasaniba,
Hakan ya nufi part d’insa ya shiga toilet yayi wanka yafito, yasaka k’ananun kayansa marasa nauyi farin wando riga bak’a,
Yunwa yakeji amma babu abinci a b’angaren nasa,
Hakan ya janyo ‘ya’yan itatuwa ya soma ci,
Ciyakeyi yana lumshe ido
Babu abinda yake masa yawo a kai sai magagganun da hajjah tayi akan Safna, sune suke masa yawo sunaso su birgita masa,
kwakwalwa,
Wad’anda take cewa dole ne a binciko asalinta atabbatar da suna da kyakkyawan asali basa da wani abi fad’i, domin duk wacce taza shigo gidan sarauta dolene sai in tana da cikakken asali mai kyau

To yanzun idan sarki ya shiga bin ciken asalinta yasami cewar tsintar ta akayi a gefen hanya,
ana nufin bata da asali shegiyace Shikenan.”

Rasa zaiyi bazai taimaki rayuwarta ba?”
Runtse idonsa yayi yanajin zuciyarsa tana k’una,
Jiyakeyi duk abinda zai faru sai dai yafaru amma bazai tab’a barin rayuwar safna ta sallawanta ba, akan wani dalili can nasu na masarauta.”

sautin kid’a yakeji yana tashi a part d’inta Wanda duk ya damesa ya hanashi sukuni bare yayi tunanin mafitar abinda yake damunsa, kwakwalwarsa da kansa duk sun har gitse,
Cikin zafin rai yafita yanufi part dinta,
Har ya tura k’ofa yashiga batasaniba abinda baitab’ayiba shiga d’akinta.”

Manyan mata yagani su hud’u kwance a kan gadonta KO wacce ba kayan kirki a jikinta,
Tana tsaye a tsakiyar d’aki sai rawa takeyi tana juyawa, irin rawar da turawa sukeyi idan suna cikin farin ciki.”

Wani bak’in ciki ya kamasa ya kashe soket d’in,
Jin shurun da tayi ba sauti t
Yasa ta juya a fusace domin ganin Wanda ya kashe mata sauti.”

Ido biyu tayi dashi tsaye a bayanta,
Anan take gabanta ya fad’i,
Ta juya da sauri ta kalli matan da ta ajiye a kan gadonta.”
ajiyar zuciya ta sauke ganin ba abinda suke aikatawa a kwance kawai suke,

Kallonta yakeyi cike da tsana da takaici da ace shi ma’abucin dukan macce ne da yau babu abinda zai gana ya daki saudat yayi mata duka irin na mutuwa.”

REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

???? D’AN SARKI SAUBAN????

Writing by
UMMU SAFWAN
( Fareeda Basheer)

Page 29

* A lokacin da aka nufi asibity da Safna ba rai bare numfashi a tare da ita,
Kai tsaye Emergency aka nufa da ita cikin gaggawa likitoci suka k’arb’eta suka duk’ufa a kanta domin ceto rayuwarta da tsayar da jinin dake fita a hanci da bakinta.”

Sosai hajiya LAILA ta girgiza da ganin yanayin da yarinyar tashiga, danko fuskarta bata tsaya ganiba hankalinta a tashe yake matuk’a.”

Hajiya laila mace ce mai mai tausayi mai son ‘ya’ya,
haihuwarta d’aya a duniya ‘yarta d’aya macce mai suna SUHAILAT wacce ta b’ata tin lokacin da ta haifeta bikin sunanta kawai akayi washe gari aka wayi gari babu ta ba alamarta tab’ata.”

B’acewar da har yanzun ba labarinta bare a san dalilin b’atan nata,
wacce a kullum hajiya laila take kukan rashin ‘yarta kwaya d’aya tilo wacce take tunanin itace kwanta a duniya, tun daga gareta KO b’atan wata bata kumayi ba, amma sai dai tanaji a jikinta Suhailat d’inta bata mutuba, tana raye domin tana yawan mafarkin ‘yarta ta girma tana cikin mawuyacin hali.”
A kullum Addu’a takeyi Allah ya bayyanar mata da tilon yarta cikin k’oshin lafiya”
Cire glass din idonta tayi ta share hawayen dake zuba a idonta,
snn ta mayar da glass din a fuskarta,
takoma cikin mota ta zauna tare da jinginawa akan kujera,
Wayarta ta d’auka kira mijinta Alhaji HABIB SANI NAIRA,

RINGING d’aya zuwa biyu Alhaji Habib ya d’auka, a lokacin yana office suna mitting tare da yaransa akan cigaban da aka samu a kanfaninsa,
Yana ganin kiran nata Saida yasaki murmushi ya kalli wayar,
Snn ya tsayar da maganar da yakeyi,
Snn Ya d’auki wayar , Cikin so da k’aunar matarsa, kuma Amaryarsa yake fad’in “Amarya bakya laifi koda kin kashe d’an masu gida, da fatan kin isa lafiya.”

Murmushi tasaki tana fad’in “Alhajina akwaika da tsokana shekara goma shatakwas kake kirana da Amarya,
Da ace Suhailat tana raye aida munfara shiga sahun iyaye dan kuwa kasan kamar yanzun mun sami suriki.”
Murmushi yasaki domin shi kansa ta tayar masa da dafin b’atan ‘yarsa wacce tafi soyuwa a ransa,
Itama yanzon yasan tashiga cikin damuwar domin yasan da zarar akayi zancen suhailat sai ta zubar da hawayenta,
Gyaran murya yayi yace “Amarya kamar yanda yake kiranta meyafaru dake ne?” domin najiya a jikina kina tare da matsala.”

Share hawayen dake zuba a idonta tayi, cikin da sanshinyar murya tace “Alhajina muna kan hanyar tafiya,
munzo gaf da fita cikin gari muka samu matsala,
Yahuza direba ya bige wata yarinya ‘yar fulani tana sanye da kayan fulanin a jikinta , a lokacin tana k’ok’arin k’e tara titin, yanzun hakan muna Asibity.”

“Subahanallahi Alhaji Habib Naira yace,
Tare da mik’ewa tsaye a firgice,
yayiwa yaransa Alama da hannu akan sutafi sai ya k’ara nemansu,
Cikin Sauri yanufi hanyar fita , Da waya a kunnensa yana fad’in wacce asibityn kuke a halin yanzun?”
Hajiya laila ta fad’a masa sunan asibityn.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button